Pg 11......

126 5 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


بسم الله الرحمن الرحيم



*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_


*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_



_*Pg 11........*_


WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYAN LITTAFIN ANAYAH,KUYI YADDA KUKE SO DASHI,INA KAUNAR KU A DUK INDA KUKE,SON SO FISABILILLAH ❤️

ZAHRATY LOVES YOU TOO ❤️


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

Sai yau na kara raina wayon da nake dashi dan kuwa wayo HYDAR yayi mun a lokacin ya amshi phone number na ba tare da na sani ba,har unguwar mu suka kaini kafin mukayi sallama nayi musu godiya na shige gida,tadda daddy nayi da securities din shi a compound din gidan mu hankali a tashe suna kai Komi,shigowa na gidan yasa daddy tahowa guna da wani irin sauri wanda har sai da ya bani mamaki,jawo ni jikin sa yayi yana cewa"ANAYAH ina kikaje ne nake ta neman ki,me ya faru da ke ",nayi mamakin jin wadannan tambayoyin daga gare shi dan ban taba tsammanin zai raga mun ba,hawaye ne kawai ke sauka daga fuska ta ji nake kamar in zauna in ta kuka har sai naji zuciya ta tayi sanyi,kallon daddy nayi nace "daddy dan Allah mai na maka da zafi ne da yasa ka tsane ni,baka so na,ba ka kauna ta ",ajiyar zuciya ya sauke zuciyar sa tana bugawa da sauri da sauri kafin yace "ANAYAH meye sa kike fadin haka,kin taba ganin inda uba yake tsanar yaran sa ko baya son su,ina son ki ban tsane ki ba,kawai ki cigaba dayi mun addu'a insha Allahu nan bada dadewa ba komai zai zo karshe ",murmushi mai kayatarwa na saki wanda ban taba ma daddy irin shi,jan hannu na yayi muka nufi cikin gida,tadda su Maryam muka yi sunyi jugum jugum a zaune,suna gani na suka mike da gudun gaske sukayo kaina suna fadin"Aunty ina kika tafi kika barmu",kallon su nayi kwalla na zubowa daga cikin idanuwa na nace "ai gani nan na dawo kuyi hakuri ",nayi mamaki da daddy bai tambaye ni inda naje ba,haka suka zauna muna ta hiran mu tare har da daddy shi kan shi,wani mashahurin farin ciki na tsinci kaina a ciki gani na gani ga ahali na cikin farin ciki da kwanciyar hankali,kai wannan wacce irin rana ce,ranar da nayi ta jiran zuwan ta,ranar da zan ganni tare da daddy inuwa daya babu fada,zagi balle duka ko kyara,Alhamdulillah kawai nake maimaitawa a cikin zuciya ta,Allah na gode maka da wannan ni'imar da kayi mun,sai kusan karfe sha biyu na dare kafin muka tashi muka nufi dakunan mu,Abdallah ya tafi nashi muma muka tafi namu,muna shiga,wanka na shiga ina fitowa na shirya cikin kayan bacci riga da wando,kallon Maryam nayi wacce ta dade dayin bacci nayi,ko cire kayan jikin ta bata yi ba,bubbuga ta na farayi ina kiran sunan ta "Maryam!Maryam!!Maryam!!!",da yake ita irin mutanen ne masu magagin bacci yasa bata farka ba,da kyar na samu ta tashi ta chanza kaya,sai da na tabbatar ta chanza sannan nazo zan kwanta,fadawa kan gadon tayi ta kwanta a tsakiya,ce mata nayi "dalla matsamun ",banza dani tayi kamar bata ji me nace ba,tsungulin ta da nayi ne yasa ta gyara kwanciyar ta da sauri,gefen ta na kwanta,tunane tunane kawai nake yi na rayuwa da abubuwan da suka faru damu a rayuwa,Allah sarki Sulaimy,Allah yayi bazata ga dawowar mummy a karo na biyu cikin gidan nan ba,Allah ya jikan ki,Allah ya gafarta miki",shi ne abinda na ambata bayan na goge sirarun hawayen da suka zubo mun wanda duk sanda zan tuna da rayuwa ta da Sulaimy sai na yi su,tunawa da abubuwan da suka faru yau kawai na fara yi,karamar dariya ce ta subuce akan fuska ta tunawa da su HYDAR da nayi,mamakin kaina nake yi yanda nake ta tuna moments di na dasu dazu,a haka wani bacci mai dadi da yake cike da kwanciyar hankali yayi gaba da ni.Ana kiran assalatu na farka kamar yadda na saba tashin Maryan nayi,sallah mukayi kafin na zauna na fara azkar di na har sanda gari ya waye,farin ciki nake ciki wanda ban san ya zan musalta muku shi ba dan kuwa yau ne za'a mai da auren daddy da mummy,muna zaune daddy a parlour gun karfe sha daya daddy ya fito daga dakin sa sanye da wata dakakkiyar farar shadda wacce akayi mata dinki mai kyau,golden hula ne akan shi kamar yadda aikin dake jikin shaddar take golden,sai zuba kamshin turare yake,anko sukayi da Abdallah dan tare zasu tafi daurin auren,inda mu kuma gidan mummy zamu tafi inda take taron bikin,duk kuwa da cewa ba wani taro bane kawayen ta ne kawai dan yan uwa wadanda suka zo daga Adamawa,daddy da kanshi yaje har kofar gidan ya ajiye mu kafin suka wuce da Abdallah,shiga gidan mukayi cike da farin ciki,mummy na ganin mu ta hada mu ta rungume mu cike da farin cikin ganin mu,ban taba tsammanin nayi missing mummy har haka ba sai lokacin da na ga mummy a gaba na kuma na tabbatar da cewa yau zata kara dawo da rayuwa a karo na biyu a tare damu,ban san sanda wasu hawaye masu zafi suka sakko daga idanu na,lallashin mu Dr.Maryam ta farayi daga mu har mummy tun da itama tazo bikin duk da cewa yanzun an ma mijin ta transfer shima ya koma Abuja da aiki,karfe sha biyu na rana aka maida auren mummy da daddy wanda auren ya samu halarta mutane da yawan gaske,anyi shagali ba kadan ba a bikin,in ka gani sai kayi tsammanin wata budurwa ce ke aure ba bazawara ba,haka muka sha bikin mu har dare,inda mummy ta tare a dakin ta a karo na biyu,mun yi farin ciki sosai da dawowar mummy a cikin rayuwar mu.Mun yi kuka sosai a daren saboda tunawa da Sulaimy da muka yi,tunawa da yadda take matukar son mummy ta dawo cikin rayuwar mu da dai abubuwa da dama wanda zafin dake cikin zuciya ta ba zasu sa in iya fadan su ba,Addu'a muka mata kafi kowa ya nufi makwancin sa dan yin bacci.

ANAYAHWhere stories live. Discover now