Pg 16.....

71 2 0
                                    


_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_









*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*







بسم الله الرحمن الرحيم






*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_




*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_




_*pg 16




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_




Wannan wani irin masifa da bala'i ne,ace mutun ya mutu a cikin wannan halin,mai ze je ya fada ma ubangijin sa,yana aikata aikin sabo ya rasu,hawaye ne naji sun kara wanke mun fuska,bazan iya tsayawa kallon wannan tashin hankalin ba,wani jiri nake ji amma haka na nufi dakin mu,ikon Allah ne kawai yakai ni daki dan ban san a wani yanayi nake ciki ba,har wani zazzabi zazzabi nake ji,kan katifa na fada ina sakin wani kuka mai ban tausayi ga mai sauraro,Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi ne kawai abinda nake iya maimaitawa,wani tsoron Allah me da qarin imani naji a cikin zuciya ta,addu'a nake yi kawai"Allah yasa mu cika da kyau da imani,Allah yayi mana kyakykyawan karshe",wannan mutuwar da Safeenah tayi ba qaramin tada ma abokan harkar ta hankali yayi ba,ni kaina da ba'a cikin su nake ba na kara gyara rayuwa ta,na kara tsoron kusanta kaina da aikin sabo,kamar Asiya kenan roommate dina,tunda Safeenah ta rasu itama wani tsoron Allah ya shige ta,shigar banzan da take yi da duk ta bari,kullum cikin sallah da karatun Quran dan neman yafiya gun ubangiji,yanzun hatta azumin Monday da Thursday basa wuce Asiya sai dai idan bata da tsarki duk ta watsar da mugayen dabi'un nan ta rungumi ibada da bautar Allah,rayuwar kenan fah,shikenan duk wani abinda aka tara an tafi an barshi.Haka muka cigaba da rayuwar mu cike da kalubale masu yawan gaske wanda bansan taya zan musalta muku ba,in wannan matsalar ta afko mun tana tafiya sai kiga wannan matsalar tazo,yanzun haka matsalar da nake fuskanta shi ne kusan wata daya kenan HAYDAR ya bar mun magana,tun bana damuwa bana nuna wani bacin rai tunda dole in mai uziri yana da hidimomin sa da ya kamata ace ya kashe bani kadai bace a gaban sa,ranar farko na kira wayar sa,yana picking yace "sorry HEENAH ina highway ne inna kai gida zan kira ki",yana fadin haka ya kashe wayar sa,cike da mamaki nabi wayar da kallo,meyesa yace haka,ajiyar zuciya na sauke ina cewa kaina "haba ANAYAH ki mai uziri mana tunda yace zai kira toh tabbas zai kira ",Na'am nayi da wannan maganar da zuciya ta ta rada mun,har magrib HAYDAR bai kara kirana ba,ganin haka yasa na kara trying number din sa,in takaice muku na kira shi yakai sau kusan ashiri amma bai dauka ba,na shiga damuwa,zuciya ta ta kasa samun sukuni,wofantarwa daga wanda kake kauna ba karamin mai juriya bane zai iya jurewa,tun ina hawaye ina iya kuka har na koma kukan zuci,ban taba tsammanin haka daga gareshi ba,na bashi dukkan yarda,soyayya da kuma amanar kaina amma ga dukkan alamu kamar hakan bamai yuwuwa bane,tun damuwar da nake ciki bata fitowa fili har ta fara fitowa,lokaci daya na zabge na rame nayi baki duk dan saboda HAYDAR,ni kaina nasan bayana mahaifi na babu da namijin da nake kauna kamar HAYDAR,i love him to the core,bansan ta yaya zan fara fuskantar rabuwa dashi ba,ban shirya ma wannan tashin hankalin ba hakika in har HAYDAR yaudara ta yayi toh tabbas ya cuce ni,yaci amanar kauna,ya karya alkawarin dake tsakani na dashi kuma bazan yafe mai ba,kamar kullum yau ma ina zaune a daki da yake yanzun mun ragu dan Asiya ta koma day dan haka ta siyar da best space din ta,yanzun haka Maamah ce a dakin mu,shigowan ta kenan ta ganni zaune na zuba uban tagumi sai tunani nake yi,dafani tayi tana fadin,"haba ANAYAH wannan wacce irin rayuwa ce zaki saka ma kanki damuwa akan da namiji,in har kikace haka zaki cigaba da tafiyar da rayuwar ki hakika zaki sha wahala,ki kyale wani tunanin namiji ki fara wata rayuwar ki manta dashi da problems din sa ",hawayen da suka dade ina son inga sun zubo daga cikin idanuwa na sune suka samu damar zubowa hannu na sa na share hawaye na,kallon ta nayi nace "maamah ina son HAYDAR ina kaunar sa ban shirya rabuwa dashi ba wallahi",dafa kafada na tayi tana sakin dariya sannan tace "haba ANAYAH meyesa kike damun kanki ne,kisa ma zuciyar ki salaama mana HAYDAR din nan fah bashi bane autan maza ",hadiye kukan dake zuwa mun nayi nace "na sani maamah amma bazan iya bane ",dariya ta saki tana cewa"kar ki damu duk rashin sanin duniya ne sa rashin budewar idanu suke damun ki ",jakar ta ta bude ta dakko wata kwaya a envelope tace "kinga wannan ki sha shi wallahi daga yau bazaki kara tuna wani HAYDAR ba,you will forget HAYDAR and his problems i promise u,cike da mamaki na dago ina kallon ta,da kyar na iya bude baki na nace mata "wannan maganin na meye ",dariya ta saki tana cewa "that's my problem with you ANAYAH ke bazaa taba miki abim arziki ba sai kin kushe mutun,toh kwaya ce wannana duk wani damu da problems din ki it will solve it,do you know yadda kwayar nan tayi mun solving matsaloli na,I'm just trying to help you",kallon ta nayi nace "maamah nice zan sha kwaya,how on earth kwaya zatayi solving matsala ta ai saidai ta kuma assasata ",dariya kawai tayi tace "ni dai i don't know yaushe zaki waye,kina wasu abubuwa sai kace wata yar kauye koh yat kauye ce ke ai kya dauki wannan shawarar balle ke haihuwar birni tashin birni rayuwar birni haba dan Allah ",gaba daya na rasa taya zan fara fassara wannan tashin hankalin maamah bata wuce 19yrs ba amma in kaga rayuwar data jefa kanta a ciki sai ka tausaya mata ita da iyayen ta,wasu magungunan ma har mamakin inda take samowa nake yi,akwai lokacin da tazo da 100k a gabana ta buga ma mai kawo musu drugs din tace na Abban su ne ta taso daga lokacin ne na gane cewa babu abinda shaye shaye baya kawo wa,saboda duk ranar daka rass kudin siyan kayan shaye shayen mutun zai fara sata,wasu daga cikin kwayoyin ma zasu iya sa ka aikata wani mummunan abu in baka cikin hayyacin ka saika dawo normal kazo kana dana sani,kallon ta nayi nace "haba Maamah kina mace kar ki manta fa nan gaba uwar wani zaki zama,kina tunanin da wannan dabiar wani mahaukacin namiji ne zai yadda ya baki dansa ki aura ",dariya tayi tana kallona tace "ANAYAH kenan kece soyayya ta dama,ni nan da kike gani na cire soyayya a tsarin rayuwa ta,na bar yin ta har abada,kinga wannan kwayoyin da syrups din nan sun isheni rayuwa ta,zanyu rayuwa ta hankali kwance dasu ",hawaye ne suka zubo mata tace "kinsan wani abu sanadin soyayya ne na fara shan wadannan abubuwan,ina shansu ne dan in manta da existence din Taheer,shiyasa na tsani a mun magana akan shaye shaye dan shi kesa in tuno dashi,na rasa mai zanyi in manta da Taheer da matsalolin shi da kuma wani soyayya da muka yi ,kallon ta nayi nace mata"hmmm Maamah baki da wani kwakwkwaran hujjan da zai gamshe ni akan wannan halin da kika jefa kanki a ciki,shin shaye shayen yasa kin manta da Taheer ne,kina tsammanin ko Taheer din ya dawo ya tadda ki a wannan halin zan iya auren ki ne",kallon ta na kuma yi nace "bari kiji na fiki shiga cikin masifa da tashin hankali na soyayya amma duk da haka nayi hakuri nasa ma zuciyata dangana ",dariya Maamah tayi tana cewa "naki kawai kika sani shiyasa kike fadin haka amma da kinji nawa da baki fadi haka ba ",dariya nayi nace "bani labarin soyayyar ki ni kuma zan baki nawa daga nan zaki banbance waye yafi shiga cikin tashin hankali da masifa a cikin soyayya",murmushi ta saki na takaici hawaye suka fara zuba daga idanun ta sannan ta fara cewa "ANAYAH naso Taheer yadda bakya tsammani na bashi dukkan wata amanata da amanar raina,munyi alkawarin aure tsakanina dashi amma yazo ya yaudare ni,ANAYAH yaudara daga wanda kake matukar so da mutuntawa yafi komai ciwo,nayi kuka,na shiga damuwa duk dan rashin Taheer amma duk da haka ban samu natsuwa ba,shaye shaye shine kawai abinda ya iya zamowa maslaha ta,farkon haduwa ta da Dr.Taheer ta farko ta kasance a asibiti ne,abin kamar a labari haka haduwar mu ta kasance,muna tafiya da Maimunatu daya daga cikin classmate dina da yake sister din ta ta haihu anan muka tadda shi,da farko yar tsama ce ta fara shiga tsakanin mu amma daga baya sai muka fara shiri muka zama friends,mun dade muna tare bai taba ce mun yana so na ba sai daga baya,daga nan muka fara soyayya ",kallona tayi cikin kuka mai tsanani wanda nima shi nake yi dan tun fara maganar Maamah na gano dacin da maganar yake mata,cigaba dacewa tayi "ANAYAH yaudara bata da dadi ban san mai nayi ma Taheer ba da na cancanci wannan hukuncin daga gare shi",cigaba da cewa tayi "haka muka cigaba da soyayya dashi,duk wata kulawa da soyayya da kika san saurayi na bama budurwar shi Taheer yana bani shi,ni kaina har mamaki nake yi wani lokacin nakan ce dama har yanzun akwai samari kamar Taheer a duniyar nan masu kulawa da mace",kuka ta kuma fashewa dashi tace "bazan manta da wannan ranar ba,wani friday evening na hau WhatsApp ina chat,kamar wacce aka tsikara na fara duba status dina,unfortunately kuma ba wani network sosai dan haka status din duk sun ki budewa,duk cikin wannan story babu wanda yafi jan hankali na kamar na best friend dina wato Jiddah dan kamar pre wedding pictures tayi posting,Allah yayini dason kallon pictures ballantana ma na biki,da kyar na samu suka bude,hotunan da nayi tozali dashi ne suka hargitsa mun tunani,suka sani cikin mamaki,al'ajabi da kuma tsoro mai tsanani,duk tunani na a lokacin mafarki nake yi ba gaskiya bane dan nasan yadda Taheer ke sona bazai mun haka ba,ganin dai ba mafarki nake ba yasa na aro jarumta na yafa ma kaina na tambayi Jiddah wacece wannan,amsar da ta bani shine ya kara gigitani,ya kuma gigita tunani na,cemun tayi"baki gane ta ba,Aunty Ameerah ce cousin dina zata auri Dr.Taheer wannan babban likitan kwakwalwan,ANAYAH Taheer ya cuceni,ya dasa mun tabon da bazan taba iya mantawa dashi ba,Allah kadai yasan irin son da nake ma bawan Allahn nan amma yaci amanata,ban boye ma Jiddah komai ba na sanar da ita,tayi mamakin jin cewa shine wanda muke soyayya dashi dan sau da dama takan tambaye ni ko a hoto tagansa sai ince mata it will be a surprise haduwar sa,tabbas kuma gashi ya zama abin mamaki,shawarar da Jiddah ta ban shi ne in kyake shi kar ince komai har ayi bikin,inzo musu biki in anzo daukar hoto ma hadu a nan in nuna masa cewa nasan zayyi aure,aikuwa take nayi na'am da wannan shawarar da jidda ta bani haka muka cigaba da soyayya da Taheer duk da cewa in har na gansa ko naji muryar sa sai naji wata karin tsanar sa a cikin zuciya ta,ANAYAH bazan iya musalta miki tsanar da nayiwa Taheer ba,haka har aka shiga satin bikin shi bai taba nuna mun wani abu ba ko kuma ya chanza mun,amma kullun ka kalleshi sai ka tabbatar da cewa akwai damuwa a tattare dashi dan har damuwar ta kasa boyuwa ta fito fili,duk sanda muka hadu na tambaye sa damuwar sa sai yace shi baida wani damuwa,haka har ranar bikin,tun da safen ranar faduwar gaba kawai nake ji babu abinda nake ambato irin Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a haka har karfe sha biyu da rabi na shirya zuwa hall din da ake taron bikin,ido hudu muka hada dashi ana daukar hoto,i was speechless ANAYAH a lokacin,shi kansa na hango tsantsar tashin hankali da tsoro a fuskar sa amma haka ya maze dan kar mutane su fahimta,gaba daya yama kasa kwakwkwaran murmushi a hotunan sai dai yake ,har yau da nake fada miki ANAYAH Taheer ya kasa tunkara ta ya fada mun dalilin sa na aikata haka,ANAYAH zuciya ta kasa daukar wannan yaudarar,zuciya ta bazata iya dauka ba,ina da rauni,damuwa yayi mun yawa dole in fara shan abinda zai rage mun su,yanzu haka da kike gani na riga na zama addicted to wadannan syrups din da kwayoyin nan in bansha ba bana samun kwanciyar hankali ",kuka nake sosai,tabbas Maamah ta bani tausayi,amma ya zatayi haka kaddarar ta take,dole tayi imani da Allah cewa wannan ne jarabawar ta,kallon ta nayi na share hawaye na nace "duk wannan abinda Taheer ya aikata nasan bayyi miki adalci ba,amma kiyi hakuri kisa ma zuciyar ki salaama,dama yawan ibada kika rike da Allah ya yaye miki damuwar ki,ba wai ki saka shaye shaye ba wanda ya gurbata rayuwar ki,zai lalata miki karatunki,zai lalata zamantakewar ki da mutane dan da wuya kiga mutun na shaye shaye yana zama da mutane lafiya,meye anfanin ilimin da kike dashi shiyasa akace Al ilmu noorun"ilimi haske ne "dan shi zai nuna miki hanyar billewa da kinyi anfani da ilimin ki da bazaki kai ga haka ba,dan dole brain din ki ya fada miki wannan abinda zan aikata mai kyau ne ko mara kyau ",dariya Maamah tayi tace "hmmm ANAYAH kenan dan Allah ki bar bata wa kanki lokaci dan bama zan saurari maganar ki ba dan bazata anfane ni da komai ba",tana gama fadin haka tayi ficewar ta daga dakin ta barni a nan zaune,bin ta da kallo nayi nasan a halin da take ciki bazata iya juran kalamai na ba,ta riga da tayi nisa sai dai wani ikon Allah,abin ya riga ya zama jikin ta dan gani take shi ne maganin matsalar ta,tunani kawai nake yi wai meyesa shaye shaye yayi yawa a cikin al'umar mu wanda ya kasance mata da yawa suna engaging kansu a ciki,bayan yana haifar da matsaloli masu matukar yawa a cikin al'umma bayan kuma yana da illoli masu yawan gaske wanda suka hada da ciwon huhu,hanta,hauka,yawan tunani mai tsanani da muni wanda zai iya kawo hawan jini ko kuma ya saka mutun ya aikata wani abu mai muni wasu har kisa sukan yi sannan kuma yana kawo lalaci ta yadda mai shaye shaye bazai iya yin komai ba sai ya sha wadannan miyagun kwayoyin yana kawo matsaloli da yawa a rayuwar dan Adam fiye da yadda mutum baya tsammani amma duk da haka maimakon rate din mutanen da suke sha ya ragu a'a sai ma qaruwa yake a kullum duniya,baga matasa maza da mata ba bakuma ga matan aure ba da magidan ta,da wannan tunanin ne har su Salmah suka shigo daki suka tadda ni,kallo na tayi tace "babe ya dai ya na ganki duk a sanyaye ne ",murmushi nayi nace "abin ne dai har yanzun maganar Maamah ce "tabe baki Salmah tayi tace"lallai kina kuwa da aiki babba in har kika ce zaki cigaba da ma wannan nasiha dan ba dauka zatayi ba,ta shiga ta dama ne ta fita ta hagu ne,gara ma ki hutashshe da kanki ",cike da mamaki take nake kallon Salmah,a raina rayawa nake yi wai meyesa wasu mutanen basu damu da damuwar wasu ba sai kansu kawai suka sani,kallon ta nayi nace "Salmah wai meyesa ke bakya damuwa da damuwar mutane ne,ya zama dole in ma Maamah magana akan wannan abun kuma in rinqa nusashshe ta illolin su dan wata ran zata iya zuwa ta sha ta fita hayyacin ta ta aikata mana mummunan abu tunda daki daya muke kwana da ita ",cikin sauri Salmah tace "bakin ki ya sari danyen kashi,wannan ai mugun fata me yanda suke fita a hayyacin su in sun shaa kawai tazo ta babbaka mu muna bacci ",duk da bana cikin yanayin walwala amma sai da maganar Salmah ta bani dariya,murmusawa nayi kadan nace "lallai Salmah toh ai rashin sata a hanya da bama yi ne da nuna mata illolin ta'ammali da miyagun kwayoyi ne zai kawo haka tabe baki Salmah ta kumayi tana cewa "ke dai kin cika iyayi wallahi,ni nataba ganin mutun kalan ki kuwa komai sai kin tsoma kanki a ciki ke ga mai tsoron Allah mai imani koh,wataran garin shishshigi irin naki sai kinja ma kanki masifa wallahi ",raina ne naji ya baci ban taba tunanin na iya masifa ba sai yau,cikin bacin rai nace "kinga Salmah ki kiyaye ni,dan kinga kina miki shiru shiru da kawaici kar ki dauka ban san yancin kaina bane,hakkin makota ka ce tsakani na da Maamah kuma tabbas innaga tana aikata abu mara kyau sai na mata nasiha nace ta bar aikata shi,kee bari ma in takaice miki koh kece dole in sauke hakkin maqotakar dake tsakani na dake,bansan dalilin da yasa son kanki yayi miki yawa ba,da wani naki ne yake cikin wannan halin zaki ji dadi ace babu wanda zai nuna masa cewa wannan ba hali bane mai kyau zai iya lalata mai rayuwar sa gaba daya ",Husnah ce tace "haba da girman ku zaku dinga behaving kamar wasu kananan yara aiki kananan yara bazasu aikata wannan cacan bakin ba ",kallon ta nayi nace "haba Husnah wannan wani irin abu ne ke kanki kin sani in har muka taimaki rayuwar Maamah Allah zai bamu lada zai kuma taimaki namu yayan dan zai duba da zuciyoyin da muka taimake ta ta",jinjina kai Husnah tayi tana kallon Salmah sannan tace "tabbas hakane ANAYAH kin fi mu gaskiya,yakamata ace mu hada karfi da qarfe gun taimaka ma rayuwar Maamah she is in danger,kai mazaaaa,mazaaaa mazaaaaa basuyi ba wallahi ",ajiyar zuciya na sauke nace "hmmmm ke dai bari Husnah wallahi maza basuyi ba kwata kwata,yaudara da cin amana tsakanin masoya yanzun yayi yawa,kuma shi ke kara jefa rayuwar mata a cikin tsaka mai wuya a wannan zamanin",jinjina kai Husnah tayi tace "tabbas wadannan na daya daga cikin damuwar mata sai sun gama bama namiji amanar soyayya at long last sai yazo ya yaudare su,mata da yawa bama iya jure ma cin amana,in kuma aka samu akasi kika hadu da kawar banza ta saka ki a layin shaye shaye shikenan fah haka muka cigaba da tattaunawa wannan matsalar wanda a hasashen mu ya nuna cewa kamar anfi fama da wannan matsalar a cikin al'umma.

—————-
HAYDAR
—————

Tuni har an manta da wani Alh Saminu sai dai dan abinda ba'a rasa ba wacce zai sa a tuno sa a cikin gidan su HAYDAR,yanzun haka HAYDAR na shirin tafiya camp ne,shikan shi ya rasa gane damuwar sa yasan dai bazai iya rabuwa da ANAYAH ba,amma ya rasa dalilin da yasa yake ignoring din ta,yana sonta sosai,kullum duniya in baiji muryar ta ba baya iya baccin haka zai kunna voice note din ta kawai yana ji,abun yana matukar damun sa ya rasa wa zai kaiwa damuwar sa,yanzun haka sun shirya da Farouq amma ko karen hauka ne ya cije shi bazaije Farouq ya bashi shawara ba dan ya sire mai,ya gane shi ba abokin amana bane,kamar kullum yau ma ya shirya cikin kananan kaya kamar yadda ya saba zai tafi gun friends din sa,yayi kyau sosai cikin ash T-shirt da bakin jeans,sai da yaje yayi ma Ummi sallama kafin ya tafi,yana zuwa gidan su Saleem yayi parking motar shi a parking lot kafin ya nufi part din shi,abinda yaji me yasa shi tsayawa kamar wani statue shi dai Allah ya jarrabe shi da aboki mara amana,cike da kasa da murya Farouq yace "ai da kyar na samu muka shirya dashi dan in rinqa samun update tsakanin shi da yarinyar,ai wallahi in ban auri ANAYAH ba sai sa dagani har shi mu rasa gabaki daya ",wani bacin rai HAYDAR ya tsinci kansa a ciki wanda bai taba shiga cikin sa ba,cikin matsanancin fushi sa kishi mai tsanani ya afka dakin,a makakance Farouq ya juyo yana kallon sa dan ya firgita ainun,cikin fushi yace ya daga hannu ya sakar ma Farouq kyawawan maruka guda biyu wanda ya gigita maza dan kuwa marukan ba karamin shigan Farouq sukayi ba,sai da yayi suman wucin gadi sannan shima ya dago da zafin sa ya kawo mai duka riqe hannun sa yayi cikin fushi yana cewa "qaramin dan iska kai baka jin kunyar daga mun hannu ba ",ai kafin Farouq ya bashi ansa ya fara jibgar sa fada sosai suka fara wanda ya tada hankalin abokan su sosai balle ma Saleem tunda a gidan su ne,sai da HAYDAR yayi ma Farouq jinajina ya farfasa mai baki kafin ya kyale shi,Farouq kuwa ganin in ya kyale shi zai ji kunya yasa yayi kukan kura akan shi yayo kanshi gadan gadan.............



Yawan comment,yawan typing

SHARE FISABILILLAH


ZAHRATY
08063304625

ANAYAHWhere stories live. Discover now