Pg 18......

58 2 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_









*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*







بسم الله الرحمن الرحيم






*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_




*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_




_*pg 19




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_



Hankalina ya matukar tashi yanzun ne nake ganin wautata na biyo Suhaib muka fito ba tare da sanin kowa ba,kuka nake yi kamar raina zai fita,bansan mafita ba yanzun,kallon shi nayi cikin kuka nace "Suhaib dan Allah kayi hakuri,kar ka keta mun mutunci na,ka tausaya mun ka tausayawa rayuwa ta,in ka rabani da mutunci na mutuwa zanyi,bazan iya rayuwa ba ",dariya ya kwashe dashi tare da cewa"lallai yarinya in kin mutu asara ta ko ta iyayen ki ",mikewa nayi ina kara neman hanyan guduwa,wani gigitaccen mari ya sakar mun wanda gani na da jina suka dauke na wasu mintoci,dambe muka fara duk kuwa da cewa nasan karfin mu ba daya bane ko kusa,duk adduar dake raina kawai shi nake yi,wani abu naji hannu yakai kai akan centre table duk da cewa ban san meye ba haka na dauka na buga mai,wani gigitaccen ihu ya saka ya sake ni,ganin jini na zuba yasa na fito daga dakin da gudu,ta hanyar da muka shigo ta nan na fita,gudu kawai nake yi dan duk na rude gashi ban fito da ko biyar ba,sai yanzun nake ganin wautata akan abinda na aikata,haka ina tafiya ina hutawa har na dawo gida,jin Mumm na fado wacce take zaune a parlour tana kallo,cike da tashin hankali da firgici take kallo na sannan tace "ANAYAH lafiya daga ina kike,yaushe kika fita ",hankalin ta duk ya tashi,kallon ta nayi kafin cikin kuka na labarta mata abinda ya faru,saukan wani gigitattun maruka guda biyu naji wanda gani na da jina sai da suka dauke na yan dakiku saboda azaba,ran Mummy ya baci fiye da tunanin mai karatu,cikin matsananciyar bacin rai tace"ANAYAH ban san baki da hankali ba baki da tunani ba sai yau,ki fita kibi saurayi ba tare da kowa ya sani ba,tarbiyyar da nayi miki kenan ANAYAH ",girgiza mata kai nake yi kawai dan na kasa furta ko da kalma daya ce,kuka kawai nake yi,kara kallo ma tayi tace "dama abinda kike yi kenan a makaranta kibi saurayi ki rinqa fita saboda bama kallon ki",nuna ni da dam yatsa tayi tare da cewa"bari in fada miki daya yau bazaki kara taka koda tsakar gida ba,i will make sure i deal with you,kuma kisa a ranki kar ma kiyi tunanin zaki koma makaranta dan Allah kadai yasan nan gaba mai zai faru ",tashin hankalin da ba'a sa mai rana kenan,ban masan ta ina zan fara tumani ba wai bani ba makaranta,kadan fa ya rage in gama 200L dina,Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un na shiga uku,yanzu ya zanyi,Suhaib ya cuceni Allah sai ya bi mun hakki na,raina ne ya raya mun kedai kika cuci kanki tunda bada karfi da yaji yasa ki bishi ba kuka kawai nake yi na kasa tashi daga gun,tsawa mummy ta daka mun tana cewa "bazaki tashi ki ban gu bane kin wani tsaya mun a kai kina kuka,yanzun ba kuka kike ba zakiyi mai dalili ne",dakin mu na wuce,tadda Maryan nayi a zaune ta zuba uban tagumi sai kace wacce akayi ma mutuwa,ina shigowa ta mike tace "Aunty ANAYAH gaskiya abinda kika aikata yau bai kamata ba,haba dan Allah yanzu fa daya ci galaba akanki ya kike so muyi muda Mummy ki kin manta abinda ya faru da Sulaimy ne,gaskiya kar ki kara aikata irin haka in ba haka ba kin san in ran mummy ya baci bazaki ji da kyau ba",rungume ta nayi ina sakin wani sabon kukan ina fadin "Maryam Allah nayi nadama ban san tsautsayin da ya kaini bin shi ba,dan Allah ki taimaka ki tayani bama Mummy hakuri ta barni in koma makaranta",ajiyar zuciya Maryam ta saki sannan ta kalle ni tace"Allah abinda mummy tayi shi ne dai dai ko nice hukuncin da zan dauka kenan akan yata tunda har ta aikata irin haka ta kira shi da tsautsayi saboda soyayya gaba ma zata aikata abinda ya fishi ta kira shi tsautsayi kuma duk akan soyayyar ,kallon ta nayi cike da mamaki nace "yanzum Maryam kema baki yadda dani ba",girgiza kai tayi tace"aa Aunty na yadda dake fiye da yadda kike tunani amma ina son ki gane cewa wannan shi me maslaha kuma bazan iya zuwa in tunkari mummy ba akan wannan maganar dan kin san halin ta yanzun nan nima zan gane kura na ",haka na zauna nasha kuka na,sallah ne kawai ke tayar dani gaba dayan su sun fita harkata kowa fushi yake yi dani,na kasa samun natsuwa gaba daya,gashi na kasa zuwa in tunkari dan tsoron ta ma nake ji,ko da daddy ta dawo mummy bata boye mai ba ta sanar ma,hankali na yayi masifaffen tashi dan nasan dadi,kuma daga kiran da yake mun nasan ranshi a bace yake,ranar na gane kurana dan dukan gaske daddy ya mun har mamaki na dinga yi yaushe rabon da daddy ya daki wani a cikin mu amma yau gashi ya dakeni,kowa a gidan in ka ganshi yana cikin bacin rai,kaina na fara tuhuma,wai yau ni ANAYAH nice silar bacin ran iyaye na,abinda ya kara daga mun hankali yadda daddy ya maimaita mun bani ba komawa Kano,hankali na ya tashi nasan shikenan maganar nan ta zauna,nayi kuka na zubda hawaye kamar raina zai fita,Suhaib yasha tsinuwa yafi cikin kwando ji nayi na tsani maza gaba dayan su,ban taba samun mutun kamili ba duk cikin wadanda nayi soyayya dasu sai HAYDAR shi kuma ban san inda yasa gaba ba.

Haka na cigaba da zama a gida ba dadi dan mummy tayi fushi dani sosai,kullum cikin bata hakuri nake yi amma har yanzun bata hakura ba,har lokacin komawa ta makaranta tayi banji ance mun komai ba,hankalina ya kara tashi amma haka nan nayi hakuri na zauna dan nasan maganar makaranta ta ta kare dan yadda daddy yace bazan koma ba,haka na cigaba da zama dan ansamun takunkumi ko kofar gida bana zuwa,haka dai nake rayuwar.

————-
HAYDAR
————-

Yaya ta tasa yadda zata yi ta shiga tsakanin Abba da Ummi kullum cikin makirci take,yau tayi wancan gobe tayi wancan amma duk a banza,karshe dai tace ma Abba wai ya karo aure,kallon ta Abba yayi cike da mamaki yace "aure kuma,kamar ya?",tabe baki tayi tace "shifa auren ko baka gane bane ",mikewa yayi yace "aa wallahi wannan kuma bazai yuwu ba,haka kawai ina zaman zamana cikin rufin asiri,hankalina a kwance in debo wa kaina tashin hankalin da ban shirya ba,aa ki sake wata maganar badai wannan ba cike da mamaki Yaya take kallon Abba tun da suke bata taba bashi umurni ya tsallake ba sai yau,tabbas Fatima ba haka tabar shi ba,lallai zata koya mata hankali.
Yanzun haka HAYDAR har sunje camp sun dawo yana serving anan Katsina,shifa har yau bai san damuwar sa ba ANAYAH kullum tana ransa amma ya kasa kiranta gaba daya yana so yaji koda muryar ta ne,yana son yadda take magana,yadda take zuba shagwaba,a rayuwar sa yana son mace mai shagwaba duk yadda take dai in har tana shagwaba shikenan tafa ta mai shiyasa kullum yake kara son ta.
Si yake ya kira ta amma ya kasa hakanan ya kyale ta,da yake yana da number din Abdallah kuma suna viewing story din juna shiyasa yake ganin hotunan su lokacin suna camp,a lokacin ne ma Abdallah yayi mai reply suna dan yin hira haka kawai ya tsinci kanshi da tambayar Abdallah "ina Auntyn ki",lafiya qalau wallahi",okay,sister din ka tana da kirki gata da hankali kunyi dacen yar uwa na gari",dariya kawai Abdallah yayi yana kallon ANAYAH dake zaune tana kallo yace "Aunty kin san Allah HAYDAR din nan na mugun sonki ",wani harara ta watso masa sannan tace"Allah koh",dariya kawai Abdallah yayi yasan dama basa magana ne,shi bai ma taba ganin irin su ba,suna son junan su amma basa magana da junan su gaba daya haba,wannan wani irin abune ya gara kawai in rabuwar zasuyi su rabu ba wai su zauna suna irin wannan abin ba kamar wasu kananan yara shi abinnan na damun sa,kuma HAYDAR din yace mai kora da hali take mai,bata taba ce mai bata son shi ba amma bata nuna mai irin kulawar da masoya suke nunawa juna.

————-
ANAYAH
————-

Haka na cigaba da zama a gida ba karatu,har yanzun ban kara jin wani yayi magana akan makaran tata ba,ba randa bana zama inyi kuka inna tuna da makaranta nayi missing karatu,shikenan yanzun shekaru biyun da nayi a makaranta sun tashi a banza kenan,kuka sosai nake yi gashi daga mummy har daddy babu wanda ya sassauto,hawaye ne kawai suke zuba daga idanuwa na,kallona Maryam tayi tace "Aunty ANAYAH kiyi hakuri mana haka Allah ya kaddara miki,wannan shi ne kaddarar,sai ki roki Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar",fadawa jikin ta nayi ina sakin wani kuka mai ban tausayi dan ni kadai nasan irin zafin da zuciya ta take mun "rumgume ni tayi tana ta lallashi na ",mummy ce ta shigo cikin dakin,a hankali ta zauna kusa dani tare da dagoni daga jikin maryam,kallona tayi tace"ANAYAH mai yasa kike kuka,dan mum hanaki ki koma makaranta,ina so ki sani ba rashin yadda bace ta sani aikata hakan,wannan hukuncin da na yanke shi ne nake ganin zai zamar mana mafita dukkan mu,mu iyayen ki ne mun yarda dake da tarbiyar da muka baki amma wannan abun da ya faru ba abin dauka da wasa bane,dan haka kiyi hakuri,yanzu haka ana nema miki daya daga cikin private university din dake nan,sai ki sako hankalin ki a kwance muma hankalin mu a kwance tunda kina gida ne ",rungume Mummy nayi ina ta kuka duk jiki na yayi sanyi,ni shaida ce akan kaunar da mummy take mun tun ina karama bata son wani abu ya taba ni,kullum cikin nuna mun tattali da kauna take yi",bude baki nayi cikin murya ta data dishe saboda kuka nace"shikenan Mummy Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairy "da ameen ta ansa sannan tace muzo muyi lunch,gaba daya duk naji ni wani iri yaushe rabon da mummy ta sake mun har haka ai har na manta,Allah sarki rayuwa,Allah kadai yasan adadin kaunar da mummy take mun,sau da yawa bata nunawa ne saboda bani kadai ta haifa ba dan haka na iya kawo kishi a tsakanin mu.Bai wuci sati daya ba aka sama mun admission a African University of science and technology,hakanan nayi hakuri na cire BUK a cikin raina,a haka na fara zuwa..........

SHARE FISABILILLAH


Zahraty
08063304625

ANAYAHWhere stories live. Discover now