_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
بسم الله الرحمن الرحيم
*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_
*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*__*Pg 12........*_
WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYAN LITTAFIN ANAYAH,KUYI YADDA KUKE SO DASHI,INA KAUNAR KU A DUK INDA KUKE,SON SO FISABILILLAH ❤️
ZAHRATY LOVES YOU TOO ❤️
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_Da kyar muka lallashi Salmah muka shiga da ita daki,tun da nake ban taba jin bacin rai kamar wannan ba,haba dan Allah wai meye sa maza basu da imani ne wannan wani irin rashin tausayi ne,yarinya ta baka amanar kan ta,ta dauki duk wani yadda daso ta baka amma abinda zaka saka mata dashi shi ne kaci amanar ta,Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi ne kawai abinda nake ta maimaitawa,ji nake in banyi kuka ba hankali na bazai taba kwanciya ba,ban samu kwanciyar hankali ba har sai da nayi kuka ba kadan ba,haka sai muka dinga lallashin Salmah har tayi hakuri ta dau dangana tunda dai dama bata isa ta chanza komai ba,mai faruwa ta riga ta faru.Haka muka cigaba da rayuwar makarnta mai cike da kalubale wanda ko wanni dalibi dai yasan wannan.Yanzun na riga da na saba da rayuwa ta babu HAYDAR duk kuwa da cewa kullun yana raina amma haka na daure dan nasan banda yadda zanyi,rabon da muyi waya dashi yakai kusan 4months a haka har mukayi hutun makaranta na koma Abuja,ba karamin farin ciki na tsinci kaina ba lokacin da naga yadda yan gidan mu suke ta nuna mun so da kulawa ga kuma kewata wanda kallo daya zakayi musu a wannan lokacin ka gane sunyi kewata,har tambayar kaina nake yi "wai dama haka suke sona,dama suna kauna ta har haka",wani farin ciki na riski kaina a ciki wacce bakuyi tsammani ba,har da daddy a masu farin cikin dawowa ta,hanawa yayi a girka komai,order din abinci yayi mana a wani babban eatery mamaki kawai nake tayi dama daddy na so na,to meye dalilin dayasa duk cikin mu yafi tsanantawa a kaina,ranar mun sha kuka da muka tuni da Sulaimy da irin yadda muka shaku da ita,nasan sa tana da rai yanzun babu wanda zai kaita farin cikin dawowa ta a wannan ranar,haka muka yini cike da farin ciki da kaunar juna tare da tarin addu'a wanda muna fatan zai kai kabarurrukan wadanda mukayi domin su.
—————
HAYDAR
—————Kamar ko da yaushe yau ma yana kwance rigingine a kan gadon aa,babu abinda yake tunani sai ANAYAH wasu kwalla ne yaji sun cika masa cikin idanuwan sa,tunani yake yi shi kansa yaushe rabon da yayi kwalla har ya manta,wai yau gashi akan mace yana kuka,Ummi wacce tun dazu take sallama ba'a ansa mata ba ta shigo,cike da mamaki take kallon shi ganin hawaye a fuskar sa,cikin firgici tace "baba na lafiya mai ya faru kake kuka,yaushe rabon da inga hawaye akan wannan kyakykyawar fuskar taka,dan Allah ka fada mun mai yake damun ka kar nima in shiga wani hali ",a hankali ya kalli Ummi,Allah ya sani shi dai bazai iya kallon ta yace mata akan mace yake kwalla ba,tunani ya fara yi mai zai ce wanda zai kare kanshi daga gun ta,ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Ummi tunanin rayuwa kawai nake yi,tunani kawai nake yi wai zamu mutu,zamu kwanta a cikin kabarin mu,bamusan ranar da Allah zai dauki ran mu ba,bamu san mai muke aikatawa ba Allah zai karbi ran mu,zamu tsaya a gaban shi a ranar karshe zai mana hisabi,akwai aljanna akwai wuta,haka za'a cigaba da rayuwa wacce bata da karshe",ajiyar zuciya Ummi tayi itama tana share hawayen da suka cika mata cikin idanuwan ta,kallon sa tayi tace "hakane baba na ko da wannan kadai ya ishi mutun yaji tsoron Allah sannan yayi masa biyayya ",kallon sa ta kuma yi tace "kazo muje kaci abinci naga kwanakin nan kwata kwata baka son cin abinci ",dan murmushi yayi tare da cewa"okay ummi bari inyi wanka inzo"jinjina mai kai tayi tare da cewa "okay amma kayi sauri dan kasan bana son zama da yunwa ",mikewa tayi ta nufi hanayar fita shikuma ya shiga bayi,ko da ya shiga kasa tabuka komai yayi,dafe bangon kawai yayi yana tunanin ta,Allah ya sani yana matukar kaunar yarinyar nan,tun randa ya ganta yaji gaba daya ta chanza mai tunani,shi kansa ya kasa gane kansa,ya rasa mai ke damun sa da yasa yake aikata abubuwa kamar wanda bashi da hankali,yana so yaje gidan su ya nemi auren ta amma ya rasa abinda yake sashi ja da baya akan hakan,wannan wani irin kaddararran soyayyace,yanzun a wani hali take shi ne tambayar da yayi ma kansa,shiru kawai yayi dan baisan taya zai ansa ma kansa wannan tamabayar ba,wayyo Allah ya zayyi yanzun,ji kawai yayi yau in beyi waya da ita ba zai iya mutuwa,wata soyayyar ta ce ta dawo mai sabo a cikin zuciyar sa,haka dai ya gama wanka,yazo ya shirya kafin ya nufi sasan Ummi,yana zuwa ya tadda ta a dining table tana zaune,yasan shi take jira dan haka kai tsaye can ya nufa,da kanta ta zuba mai a plate kafin ta fara bashi a baki,turawa kawai yake yi badan abincin na masa dadi ba dan kawai kar Ummi ranta ya baci ne. Haka ta gama bashi abincin,yana gamawa yace ma Ummi zai je ya kwanta dan wani bacci ne yaji kamar wanda yasha kwaya ko akama alluaran bacci,yana zuwa dakin sa ko addu'a bai iya yi ba wani nannauyan bacci ya kwashe shi,shi kansa lokacin da baccin yazo mai yayi mamaki dan bai dade da tashi daga bacci ba,amma ya kasa rike baccin har toilet sai da yaje ya wanko fuskar sa amma baccin yaki sakin sa,bai da wani mafita face kawai ya kwanta yayi baccin,bai masan baccin ya kwashe shi ba shiyasa ma ko addu'a bai samu yayi ba haka baccin nan mai nauyin gaske ya kwashe shi wanda da girmansa dai yasan bai taba yin irin shi ba,kuma yasan shi ba mai bacci mai nauyi bane amma sai yau abun yazo mai unexpected,haka dai ya cigaba da baccin sa.
Wani mummunan mafarki yayi wanda ya haddasa mai da tashi yana sakin wani azababben ihu wanda sai da gidan ya ansa gabaki daya,kafin kace kobo su Ummi da Abba sun iso cikin parlour din,ganin shi sukayi har ya kusa isowa kofar dakin,cike da firgicin ganin sa a wannan yanayin Abba yace"Aliyu lafiyar ka kuwa meke faruwa ne ",bige Abba yayi zai wuce,da sauri ya riki sa,sosai fuskan Abba ya cika da mamaki jin wani irin karfi da yayi mai matukar ban mamaki wanda sai daya tsorata daddy,basu suka samu suka danne shi ba sai da kannen shi biyu Musaddiq da Imam,hankalin Abba yayi matukar tashi kasancewar HAYDAR shi ne baban dan sa wanda a kullum yake alfahari dashi Ganin yanayin da yake ciki ne yasa Abba kiran wani malami dake kusa dasu,karon farko da yazo yana duba shi yace aljanu ne,cike da mamaki Abba ya maimaita "aljanu kuma ",Ummi kuwa kuka ta fashe dashi,ita bata taba jin inda namiji aljanu suka bige shi,tana dai jin ana fadi amma bata taba gani ba,wai yau sai gashi dan ta data fi kauna shi ne aka ce aljanu sun bige. Kuka sosai Ummi ta dinga yi,da kyar Abba ya lallashi Ummi har tayi shiru amma ta kasa tafiya tayi ta barshi dan gani take in ta tafi da kyar ta dawo ta tadda shi,gaba daya dai hankalin ta ya kasa kwanciya,Abba shi kansa ya tausaya mata dan yasan duk cikin yaran ta ba wanda take kauna kamar sa duk kuwa da cewa bashi bane dan fari,amma kyautatawan da yake mata da kuma nuna mata so da kulawa ya wuce tunanin mai tunani,wadannan dabi'un yana daya daga cikin abinda yasa itama take son sa sosai. Haka HAYDAR ya cigaba da jinya,ya rame sosai yayi baki wanda hakan ya kara tsorata iyayen sa sosai dan gani suke kamar wani abun ne ke damun sa ba aljanu ba,ga kuma damuwar ANAYAH wanda a kullum kara azazzalar sa yake yi,ya kasa kwantar da hankalin sa gu daya,kullun tambayar kansa yake yi anya bai cutar da yarinyar dani ba,anya ba hakki na bane yake bibiyar sa,ya koya mun soyayyar sa sai sanda nake matukar bukatar sa a kusa dani ya tafi ya barni,idanun sa ne suka kada sukayi jaaaaa,ji yake yi kamar yayi tsuntsu ya ganshi a Abuja a kofar gidan su,gaba daya ji yake yi bazai iya cigaba da zama ba ba tare da sun dawo kamar da ba,wadannan tunanin na daya daga cikin abubuwan da yasa ya kare ramewa ya kuma yin baki,kamar ko yaushe yau ma yana kwance akan gadon shi,Ummi ce zaune a gefen shi tana cewa yaci abinci amma yana ce mata cikin sa na masa ciwo ne,tun Ummi na daukar abin da wasa har hankalin ya ya fara tashi ganin yana juye juye,mikewa yayi da sauri jin wani amai na taho mai,wani bakin amai ya fara yi wanda ya tada hankalin Ummi,kafin ta iso kusa dashi tuni numfashin sa ya dauke,girgiza shi ta farayi tana cewa"HAYDAR!HAYDAR!!HAYDAR!!!,dan Allah ka tashi kar ka tafi ka barni..........
DAN ALLAH KUYI MUN UZURI ABUBUWA NE SUKA HADE MUN BANI DA LOKACI SOSAI,ALLAH YA SANI YAU NASO MUKU TYPING DA YAWA,UNEXPECTED KUMA NA SAMU ORDER SHIYASA KUMA INA GAMAWA NA TAFI ASIBITI,DAN ALLAH KUYI HAKURI KUMIN AFUWA NASAN BAKWA JIN DADIN YADDA BANA POSTING AKAI AKAI AMMA DAN ALLAH KUYI HAKURI 🤦🏻♀️🥹
Zahraty ❤️
08063304625