Pg 13.....

98 3 2
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


بسم الله الرحمن الرحيم



*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_


*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_



_*Pg 13........*_

Kuka sosai take yi dan hankalin ta ba qaramin tashi yayi ba,Abba ne da a lokacin ya shigo dakin da sauri,dago shi tayi tace "Abban su dan Allah ka taimaka mun kar ya mutu,ina son sa ban son rabuwa dashi",a hankali ya zuba mai ruwa,a take ya farfado da wani azababben ciwon ciki da ya qara firgita ahalin gidan,yayar Abba wacce suke kira da Yaya ta shigo dakin,kallon shi take yi yadda yake juye juye hakan ya kara tabbatar mata da cewa yana cikin matsananciyar azaba,salati kawai yake yi,kallon Abba tayi tace "haba Mahmoud ka tsaya kana kallo yaro yana cikin azaba amma kayi tsaye akan shi kana kallon sa ",ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyar sa tana karyewa yace"Yaya ban san ya zanyi ba,na rasa ta ina zan fara tunani wallahi ",kallon sa tayi tace"ka tashi muje asibiti mana ",mai gadi ya kira suka dauke shi zuwa asibiti,suna zuwa aka bashi gado,duk iya bakin kokarin likitocin na son gane mai yake damun HAYDAR sun kasa yi,babu kalan binciken sa ba'ayi ba amma sun kasa ganin abinda ke damun shi,haka dai aka dinga ajiye shi a asibiti,in ciwon ya tashi sai dai a mai allurar bacci,in kaga Ummi a lokacin sai ka matukar tausaya mata,tayi baki ta rame sai kace wacce ta shekara tana ciwo,kullum cikin addu'a kawai take Allah ya bashi lafiya dan yanzun ciwon nashi tsoro yake bata,HAYDAR din shima yayi wani irin haske saboda jinya amma ya rame sosai dan shi kadai yasan irin azabar da yake ciki,ji yake yi dama ya rasu kawai ya huta da wannan matsananciyar azabar da yake ciki,wani lokacin in ciwon ya taso mai har so yake yi hawaye su zubo daga cikin idanuwan sa dan kawai su rage mai radadin da yake ciki amma sai suki zubowa kullum da tunanin ANAYAH yake kwana yake tashi,in ya tuna yadda ta wofantar da shi,ko kira balle text message ba qaramin tashin hankali yake shiga ba,bai shirya rabuwa da ita ba dan yana son ta,yana kaunar ta,muradin shi shine ta zama matar shi ta sunnah,haka kullum yake cikin tumanin ta,kamar kullum yau ma Farouq yana tare dashi,kallon Farouq yayi yace"Farouq kaga yadda HEENAH take min ko,ta bar kulani,bata san halin da nake ciki ba,ban san mai na mata ba",ajiyar zuciya Farouq ya sauke yana cewa "haba HAYDAR wai meyesa baza ka bar yarinyar nan bane,ta riga ta nuna bata son ka,jifa har ciwo ka kwanta amma ta kasa ko da kiran ka ballantana kasa ran zata maka text message ",murmushi HAYDAR ya saki sannan yace "Farouq kenan nasan wacece HEENAH da tasan ban da lafiya ba wacce zata kaita damuwa dani bayan Ummi",tabe baki Farouq yayi yace "ai shikenan sai kayi ta wahalar da kanka a banza saboda ita",jinjina kai kawai HAYDAR yayi ya rasa mai yasa Farouq yake so su rabu da HEENAH amma yana barin abun a ran shi ne dan shi ba mutum bane da ya cika son surutu da yawa.Abun na HAYDAR yanzu ya wuce tunanin mai tunani,dan ya mugun fita hayyacin sa,yanzun haka komai sai dai a masa babu abinda yake iya yi da kansa,kamar kullum yau ma daga shi sai Abba sai yaya a cikin dakin,hawaye ne suka wanke fuskar Abba dan hankalin sa ba qaramin tashi yayi ba,baya son ya rasa dan shi,yana matukar son HAYDAR,hankali tashe Yaya tace "haba Mahmoud kuka kuma da girmama ka,insha Allah zai samu lafiya",kuka Abba ya fashe dashi yana cewa "Yaya wallahi na rasa irin wannan ciwon da HAYDAR yake yi,kalli fa yadda ya koma duk ya fita a hayyacin sa",kamo hannun Abba yayi yace"Abba kayi hakuri in har Allah ya riga da ya rubuta zan bar duniya shikenan zan tafi amma in har ina da rabon zan kara lokaci a duniya tabbas duk wahalar da zan sha sai na rayu ",wannan maganar mutuwar da HAYDAR yayi shi ne ya qara tada ma Abba da hankali,shi kansa HAYDAR tun da aka haife shi bai taba ganin Abba na kuka ba sai yau,yana kukan tausaya mishi,kallon su Yaya tayi tace "ni dai a gani na Mahmoud ciwon yaron nan bana asibiti bane,mu maida shi gida kawai ayi mai magani ",aikuwa shawarar Yaya Abba ya dauka dan gida aka maida HAYDAR aka fara mai magani,hankalin Ummi ya kara tashi da aka ce asiri aka mai,haka aka cigaba da magani,ranar da asirin ya sake shi hankalin su ba qaramin tashi yayi ba dan kashin gashi da laya yayi muraran,hankalin Abba yayi mugun tashi ranar,wai wannan abun ne a cikin dan sa,bayan komai ya lafa malamin ya kalli HAYDAR yace"abinda nake so da kai shi ne kayi imani da Allah cewa wannan abin da ya sameka yana daya daga cikin kaddarar ka,kar kayi zargin wani me ya aikata maka haka,sannan ka riqe ibadun ka,addu'a kariya ce sakaci kadan zakayi da addu'a a samu dama akan ka,ka rinqa kwanciya da alwala da kuma y sarki,ka yawaita sauraron karatun Quran kaji",ajiyar zuciya HAYDAR ya sauke yana jinjina kai sannan yace "na gode",magunguna ya hada mai sannan ya tafi,gaba dayan su jikin su yayi sanyi,dukkan su tunanin su waye yake son ganin bayan HAYDAR din waye baya kaunar shi har haka da zai aikata mai wannan mummunan aikin,ita kanta Yaya kasa shiru tayi duk da cewa basa ga maciji da HAYDAR dan yadda take kyarar Ummi yasa shima baya kaunar ta,kwata kwata baya shiga harkar ta,kallon su tayi tace "kai duniya ina zaki damu,yanzun wani mara imanin ne yake son ganin bayan yaron nan",shiru HAYDAR kawai yayi ba tare da yace komai ba dan gaba daya abin ya gama dagula mai Lissafi,daga baya kawai yabi shawarar malan kan cewa kar ya zargi kowa akan abinda aka aikata mai.Kulawa sosai yanzun HAYDAR yake samu daga dukkan ahalin sa.

ANAYAHWhere stories live. Discover now