Pg 4.......

103 5 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

بسم الله الرحمن الرحيم

*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_

*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_

_*pg 4.......

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_


           Kallon Sulaimy Dr.Maryam tayi cike da firgici hadi da mamaki tace"sun rabu,ya sake ta",cikin kuka nace"ummi daddy ya saki mummy ya zamuyi ta tagi ta barmu,ba kowa,mu kadai muke kwana",ji Dr.Maryam tayi kamar ta daura hannu a kai ta fara kuka,wannan wani irin masifa da balai ne,ace yara an barsu haka babu mai kwaba musu babu me nuna musu abinda ya dace suyi da wanda bai dace ba,kallon yaran kawai Dr.Maryam keyi tama rasa mai zata ce,kallona tayi tace"ANAYAH ina daddyn ku yake",kafin tace wani abu Sulaimy tayi caraf tace"ya tafi kai karuwar sa gida,tare suka zauna a gidan nan har ma iskanci suke yi",da sauri Dr.Maryam tasa hannu ta rufe ma Sulaimy baki tana cewa "kar in kara jin haka daga bakin ki",mikewa tayi ta fita harabar gidan,wani kuka ne ya taho mata wanda ita kanta bata san ta ina ya taho mata ba,matsananciyar tausayin su ANAYAH ne a cikin zuciyar ta,yanzun ita tambayar da take ma kanta shin menene taka mai mai abinda ke damun baban ANAYAH yake aikata wannan mummunar aikin,abin ya wuce waje har ya dawo cikin gida,har takai ga cewa yar sa ta kamasa red handed yana aikatawa,wannan wacce irin masifa ce,wacece wannan Sabreen din,me take dashi wanda Mum ANAYAH bata dashi,me tafita dashi?",kuka kawai ta kara fashewa dashi,tasan cewa ita kanta mum ANAYAH yaudarar kanta tayi da tace ANAYAH ta kula da yaran nan,ta ina zata fara,yarinya ce itama wacce take bukatan kulawa a wannan shekarun a gun mahaifiyar ta,abinda zuciyar ta ta raya mata shi ne ta kwashi yaran nan ta hadasu da nata ta cigaba da tarbiyan su,Allah na ganin niyyar ta kuma in Allah ya yarda zai mata kyakykyawan sakamako,da wannan tunanin ta koma parlour din,kallona tayi tace "ANAYAH kun ci abinci",jinjina kai tayi tace "eh ummi mun dafa nida Sulaimy mun ci",kallon su take yi cike da tausayawa,sai gurin karfe tara na dare kafin daddy ya dawo daga inda yaje,yayi matukar mamakin ganin Dr.Maryam a gidan,kallon ta yayi kafin yace "kinji abinda kawar ki ta aikata ko Dr,ta tafi ta barni da yaran nan,taya take tunanin zan iya kulawa dasu da rayuwar su",kallon shi Dr tayi sannan ta zayyane ma daddy kudirin ta,kallon ta yayi yana murmushin nan nasa sannan yace"Dr Maryam kiyi hakuri gaskiya bazan iya baki yara na ba,nima ina da bukatar su a kusa dani",cike da mamaki dr Maryam take kallon sa,tama rasa me zata ce masa wannan mutumin na bata mamaki wallahi,kallon sa tayi sannan tace"shikenan Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairy,ya maganar makarantar su,dan gaskiya bai kamata a datse musu karatu ba",ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "ina sane dashi,sai dai su Sulaimy su koma,ita kuma ANAYAH ta cigaba da zama a gida tana kula da gidan",cike da mamaki Dr.Maryam ke kallon sa kasa yin shiru tayi sai da tace "dad ANAYAH ban san dalilin dayasa kafi jin zafin ANAYAH ba duk cikin yaran ka,ajiyar zuciya yayi sannan ya juyo ya kalli Dr.Maryam yace "saboda tafi kama da uwarta,ga mugun hali da dabi'a duk na uwarta ta dakko",jinjina kai Dr.Maryam tayi ta tana cewa"Allah ya kyauta toh".Daga wannan lokacin shikenan karatuna ya katse,da yake lokacin ina JS 2 ne,hakanan nayi hakuri da makaranta tun da daddy ya riga ya fadi haka toh babu Chanji,kullum cikin neman layin mummy muke amma bamu samu ba,kullum sai nayi kuka ina Allah wadai da dabi'un mahaifina wanda har yanzun basu chanza ba,ni kaina nasan ba karamin kokari nake yi ba gun kula da yan uwana,na rame,nayi naki,kashin wuya na duk sun bulluko saboda tsabar wahalar danake sha a hannun daddy,na rasa dalilin dayasa daddy ya tsaneni,baya kaunata,baya son ganina cikin farin ciki da dariya,yana ganin murmushina a ranar duk yanda zaiyi yaga ya koma kuka sai yayi,a haka nake hakuri,kullum Sulaimy ce take tausa na,nuna mun take wannan itace jarabawa ta da kuma kaddarar rayuwata,inyi hakuri wata rana sai labari,in cigaba da addua da karatun Quran zasu taimaka mun,ba karamin aiki kuwa shawarar Sulaimy tayi ba,dan ya mata anfani matukar gaske.

ANAYAHWhere stories live. Discover now