Pg 8......

79 5 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


بسم الله الرحمن الرحيم



*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_


*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_



_*Pg 8........*_



Kuyi hakuri da wannan ba yawa


_EDITED_

Kallon ta Maryam tayi tace "Aunty kiyi hakuri,ki kyale daddy yayi auren sa kar azo daga baya muna dana sani ",kallon Maryam nayi ina murmushi sannan nace "Maryam ke dama kina tunanin na isa in hana daddy aure ne,ai kema kin san hakan bazai taba yuwuwa ba,kawai dai auren ya bani mamaki ne dan ban taba tunanin zai kara nan kusa ba ",jinjina kai Maryam tayi tace "hakane,Allah dai ya sanya Alkhairy yasa ta arziki zai auro"da Ameen na ansa mata sannan muka cigaba da tattaunawa akan auren,abinda ya bani mamaki game da auren da daddy zai kara shi ne sai da daddy yayi mana akwati daddai na kaya,ni da maryam kowa kala goma goma Abdallah haka,ga takalma,jaka,veils da kuma hijab kai hadda sarkoki masu tsada wanda kallo daya zakayi musu kasan an kashe makudan kudade gun sayan su,ni kaina abin na daddy mamaki yake bani sosai,dan yadda daddy ke dokin bikin ya wuce yadda ake tunani,haka dai aka cigaba da shirye shiryen bikin wanda daddy yake kashe makudan kudade kamar bai san zafin su ba,ranar laraba aka zo yi ma amaryar jere,gaba daya kayan gidan mu aka kwashe aka chanza wasu wanda ko tantama bana yi daddy ne yayi wannan aikin,haka dai aka cigaba da shirye shiryen,ranar juma'a bayan an sakko daga sallah aka daura auren Daddy da amaryar sa,ansha shagalin biki kamar na wani saurayi,da yamma aka kawo amarya,ba laifi munga sakin fuskan ta a karo na farko a rayuwar mu da matar daddy ta taba nuna damuwar ta akan mu,sai nan nan take yi damu sai kace ita ta haife mu,wannan kyautatawan da Aunty Madeenah ke mana ne yasa naji ta kwanta mun raina ko ba komai nasan ba irin Sabreen bace wacce ta azabtar da rayuwar mu,mun cigaba da zama da Aunty Madeenah cikin kwanciyar hankali,so da kuma kaunar juna.
       Bayan wata daya da bikin daddy da Aunty Madeenah ina zaune a parlour ina kallon wani Korean film a laptop dina mai suna MOON LOVERS wanda ya hadu,na dade zaune a gun saboda dadi kallon da nake ji,bude kofar da naji ne yasa na daga kaina na kalli kofar,wata yarinya ce wacce bata wuce sa'a ta ba ta shigo cikin dakin,bin ta da kallo nayi ina kallon ikon Allah,mutun ya shigo har gidan uban ka amma ya rinka maka kalan wannan kallon wanda yake nuna tsantsar tsana da wulakanci,kallon ta kawai nake yi ba tare da nace mata komai ba,a kaina ta tsaya tana mun wani irin kallo,sai da ta gama yatsine yatsinen ta sannan tace "mummy na nan ",ba tare da na dago kaina daga laptop din ba nace mata "baki iya sallama bane ",cikin fusata tace mun"malama kar ki fada mun magana gun mahaifiya ta nazo,bada din ita da take wannan gidan ba da bazaki ganni acikin sa ba ballantana ki fada mun maganar da tazo kanki ",dagowa nayi cike da mamaki dan bansan Aunty Madeenah nada ya ba,nuna mata bedroom din nayi nace mata "ga dakin ta nan ki shiga ",tsaki kawai taja ba tare da ta tanka ni ba tayi wucewar ta,mamakin ta na dinga yi dan a gaskiya dabi'un ta basu mun ba kwata kwata,yanda naga Aunty Madeenah nada kirki da son mutane da kuma sanin darajar jama'a sai abun ya kara bani mamaki,watsar da lamarin ta nayi kawai na cigaba da kallo na tunda ba ita ta aje ni ba cikin gidan ubana ta shigo dan haka bata isa ta takani ina tsaye ina kallon ta ba,sai da aka kira sallah kafin na tashi naje nayi na dawo,Aunty Madeenah ce ta fito daga dakin ta tare da wannan budurwar,kallo na tayi kafin ta juya ta kalli budurwar tace" Saddeeqa ga ANAYAH nan kun gaisa kuwa ",dariya tayi sannan tace "eh mummy mun gaisa ai ANAYAH nada kirki sosai ",juyowa tayi ta kalleni tace "ANAYAH wallahi kina da kirki sosai dan Allah zaki zama kawata ",kallon mamaki kawai nake mata,yarinyar da ta gama mun rainin wayo amma ji yanda take mun magana yanzun saboda duniyanci da kuma iya fusk biyu,kallon ta nima nayi da kayataccen murmushin dake kan fuska na wanda mutane da yawa sukance yana karamun kyau idan nayi shi,ce mata nayi "sannun ki ya gida ",murmushi tayi tace "gida Alhamdulillah ",ita kuwa Aunty Madeenah sai dadi take ji yanda muka mutunta junan mu kallon mu tayi tace "kuzo kuci abinci bari in duba abu a kitchen ",ansa mata nayi da toh "tana wucewa tayi ta shiga kitchen Saddeeqa ta kalle ni tace "ke kar ki ga na sakar miki fuska kice zan zama kawar ki,sa'an mummy kawai kika ci",kallon ta nayi na watsar dan ni bamma ga anfanin yi mata magana ba,da nasan in har nayi mata magana tabbas sai mun zo muna cacan naki ni kuwa na wuce da ajin wannan yanzun dan nasan abinda ke kaina,ai ni ba yarinya bace,kallon mu Aunty Madeenah tayi wacce yanzun ta fito daga kitchen tace"kuzo kuci abincin mana",mikewa mukayi dukkan mu muka zauna akan dinning din,abincin mu muka fara ci ba tare da daya ya kula daya ba,muna gamawa muka mike,ni na harhada plates din nje kitchen na wanke,ina fitowa Saddeeqa na tashi zata tafi,kallo na tayi ta kalli Aunty Madeenah tana cewa"kawata muje ki rakani mana in samu abin hawa ",kallon ta nayi sannan na tashi,daki naje na dakko hijab dina na rakata,muna fitowa daga gidan ta kalle ni tace "ke ANAYAH kike ko wa kike da suna kar fa ki cika zakewa da yawa dan ba ita ta haife ki ba ",murmushi nayi mata sannan nace"ai dama ba ita ta haife ni ba,ki sani ita din matar baba na ne ",wani irin kallo mai cike da tsana tayi mun sannan tace "shikenan bari kiji kar kiyi marmarin in dawo gidan nan da zama dan sai na zame miki karfen kafa dan sai kinyi dana sanin sani na a rayuwar ki",tana gama fadin haka tayi wucewar ta,daga murya nayi kadan ina cewa "ai in kin dawo gidan mu da zama toh ki dauki kanki a matsayin Agola mai cin arziki ",ina fadin haka na juya nayi shigewa ta gida,wannan kalmar ta Agola ba karamin bata ma Saddeeqa rai tayi ba,dan ansha fada mata wannan kalmar amma bata taba jin zafin ta ba kamar yadda taji sanda na jefe ta da wannan kalmar,gyada kanta kawai tayi ta tari abin hawa tayi tafiyar ta.Ina shiga gida Aunty Madeenah ta kalle ni tace "har ta tafi ne ",ansa mata nayi da cewa "eh ta tafi ta samu abin hawa ",kallo na ta kara yi tace "nayi mamakin saurin shakuwar ku da Saddeeqa dan mutun ce mai wuyar sha'ani ",dariya nayi nace "Aunty ai kinsan kowa da yanayin sa jinin mu ne yayi saurin haduwa shiyasa ",dariya kawai tayi tace "amma ga abin da mamaki ",chanza zancen nayi ta hanyar dakko wata magana ta daban na fara yi mata,haka muka zauna muka cigaba da hiran mu cike da farin ciki da kaunar juna,jiyo Maryam nayi tana kwalo mun kira,ansawa nayi da sauri ina tashi dan jin yadda take kira na,ina shiga dakin naga wayana a hannun ta,ansa nayi dan duba wake kirana haka,sunan mummy dana gani akan screen dim wayar ne yasa nayi saurin picking cike da farin ciki,sallama na fara yi mata sannan na gaishe ta,ansawa tayi sannan tace "ANAYAH tun kuna Mambila nazo gun daddyn ku akan ya bani ku mu dawo amma yaki,wallahi hankali na ya kasa kwanciya akan zaman ku a gidan nan ku kadai ",ajiyar zuciya na sauke tare da nima cikin kewan ta dan mahaifiya ta wuce tunanin mai tunani cewa nayi "mummy baki san cewa daddy ya kara aure ba kusan wata biyu kenan yanzun ",cike da tarin mamaki tace "aure kuma shikenan ",cigaba da fadi tayi "ki rokesa ya kawo ku guna ko wata daya ne kuyi tunda anyi hutun makaranta ",cike da farin ciki nace "Okay mummy,insha Allah i will try my possible best inga nayi convincing din shi ya bar mu muzo gidan ki hutu ",ajiyar zuciya mummy ta sauke tana cewa "yawwa baby na gode sosai"cikin farin ciki nace "haba mummy stop thanking me mana ai kin wuce haka a waje na wallahi",haka muka gama tattaunawa da mummy sannan na bama Maryam suka gaisa kafin muka katse wayan,tunani na farayi ta ina zan fara ma daddy maganar cewa zamuje gun Mummy nasan yadda yake da saurin fusata din nan yanzun nan zai mun kaca kaca,idea din tunkarar Aunty Madeenah da maganar ne yazo mun,nasan in ita tayi masa maganar may be ya yadda muje har mu karasa spending holiday din mu acan,mikewa nayi na fito daga dakin zuwa parlour,tadda Aunty Madeenah nayi a zaune a parlour tana kallon wani season film wanda akeyi a zeeworld,Sannu da zama nayi mata,ansa mun tayi cikin kulawa,can na kalle ta nace "Aunty dama hanzun mummy ta kira ni a waya wai tana so mu zo mata hutu,wai mu karasa ragowar hutun mu da ita,shi ne nace bari in miki magana ki dan taimaka ki roka mana daddy kin san shi in ni naje zai iya cewa ba zamu ba,amma in kece zaki iya mai magana kuma ya amince ",murmushi ta saki tana cewa "ANAYAH sarkin tsoro kar ki damu zan mai magana insha Allah zai amince,ai dama ba'a taba raba da da mahaifiyar sa ",cikin farin ciki na rungume ta ina jin dadin yadda tace zata yiwa daddy magana,shiyasa har yau duk cikin matan da daddy ya aura ba wacce nake kauna kamar Aunty Madeenah dan ta rike amanar mu kuma tayi mana halacci a rayuwa amma daga baya in na tuna irin rabuwar da mukayi sai inji kamar me,dan rabuwa ce mara dadi,haka dai na cigaba da sauraro ko daddy zai amince da zuwan mu gidan mummy shiru,har dai akayi sati daya,ganin hakan da nayi yasa na cire rai da zuwa gidan mummy gaba daya,dama nasan dawuya daddy ya amince da zuwan mu gidan mummy ta dadin rai,ina zaune a bedroom din mu ina gyara kayana naji daddy na kira na daga downstairs,da sauri na sauka,zaunawa nayi a kasa na gaishe shi ansa mun yayi tare da cewa "ku hada kayan ku keda su Abdallah zan kaiku gidan mummyn ku",cikin farin cikin da daddy bai taba sanya ni a cikin sa ba naji ya dabaibaye ni,ban san sanda na rungume shi ba ina cewa "thank you daddy we really appreciate ",kallon Aunty Madeenah nayi nace "Aunty mun gode Allah ya saka miki da mafificin alkhairy ",ansawa tayi da ameen ya hayyu ya qayyum itama cikin farin ciki ganin yadda nake cikin farin ciki nima,tashi nayi na shiga dakin mu ina wa Maryam dake game a wayar ta albishirin cewa yau zamuje gidan mummy,ihu ta saka tana rungume ni tace "wallahi ji nake kamar nayi tsuntsuwa na ganni a gidan mummy yanzun",kallon ta nayi nace "kije ki hada ma Abdallah kayan sa ni bari in hada namu ",mikewa tayi sa sauri ta fita daga dakin zuwa na Abdallah ni kuma na fara hada mana namu,cikin lokaci kankani mun gama hada kayan cikin travelling bags din mu,wanka muka shiga,bayan na fito na shirya cikin lace golden colour,kwalliyar da na dade banyi irin shi ba shi na zauna na tsantsara,ina cikin yi kawai Sulaimy ta fado mun a rai,wai da ace tana raye nasan ba karamin farin ciki zatayi ba jin cewa zamuje gidan mummy,hawayen da suka zubomun na share sannan nace "Allah ka jikan wannan baiwa taka kasa tana kyakykyawan matsayi",Maryam ce dake shiryawa tace "Ameen y hayyu y qayyum Aunty "bayan mun gama shiryawa muka sakko da kayan mu kasa,daddy da kanshi ya kaimu gidan,yana sauke mana kayan mu ya juya mu kuma muka shiga gidan,a compound din gidan muka tadda mummy cike da mamaki,al'ajabi da kuma farin ciki wanda ya fito sosai a fuskar ta tace "ANAYAH ,Maryam da Abdallah kune ",cike da farin ciki muka nufe ta muka rungume ta,shiga cikin dakin ta mukayi a parlour muka zauna muna ta hira,gaba daya mummy ta rasa inda zata saka mu,komai ta dakko ta kawo mana,tun daga kan biscuits,cookies,chocolate,cakes da su samosa abubuwa dai kala kala,har wani kwallan farin ciki sai sa naji sun cika mun idanuna saboda tsabar kewar mummy da nayi,daya daga cikin daku nan dake parlourn ta kai mana kayan mu ni da Maryam,Abdallah kuma ta ajiye mai a dayan,hira sosai muka sha da mummy kafin mijin ta ya dawo ,nayi mamakin yadda yasan mu gaba daya,sannan kuma ya kara mana ta'aziyar rasuwar Sulaimy,mutumin kirki dashi,sai naji dama daddy ne yake haka,dama wannan ne daddyn mu dan yana da sakin fuska sa kuma jan mutane a jiki,cikin lokaci kankani mun saba dashi sosai dan har muna iya zama muyi hira tare dashi,mun shaqu cikin kwanakin da basu wuce kwanaki goma sha hudu ba wato sati biyu,yau ma da yake a gun mummy yake da kwana,da daddare bayan mun gama hiran mun mukaje muka kwanta,gun karfe biyu na dare kamar a mafarki naji ana shafa mun jiki,ni dai ban farka ba amma tabbas  bacci na ya fara chanzawa ji nayi abun ya cigaba da tafiya,a firgice na farka daga baccin,bude baki nayi zan saka ihu naji an rufe mun baki na ruf na kasa cewa komai,wanda ido na yayi tozali dashi ne ya tada mun da hankali,Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai nake ta ambato a fili,wannan wani irin masifa ce,dama duk wannan nan nan din da bawan Allah din nan keyi damu dan ya lalata rayuwa tace,cikin fushi da bakin ciki hade da matsananciyar tsanar sa nace"daddy ban taba ganin mutun mara kirki,mara tunani mai tunanin dabbobi ba kamar ka,wai ko ka manta cewa ni yarinayar matar kace ",dariya ya saki irin na yan duniya ya fara cewa "hmmmm ANAYAH kenan bari kiji kar ki saka ma ranki matsayi na ina sane dacewa ke yarinyar matata ce meye a ciki toh,kin san meye ",kara sassauta muryar sa yayi tate da cewar"kar ki damu in har kika amince dani babu abinda bazan miki ba,duk kasar da kike son kije a duniyar nan zan kaiki,zan karbo ki daga gun daddyn ki ki dawo nan da zama",cikin matsanancin kuka nace "wallahi bazan taba amincewa dakai ba",kallo na yayi yace"in kuma naji labarin nan a gun wani sai na kashe mummyn ku inzo in kashe ki sannan in kashe daddyn ku kinga shikenan daga Maryam har Abdallah sun zamo marayu sannan Maryam ta zama karuwa ta",ban san sanda na fashe da wani kuka ba wanda yake hade da ihu,a hargitse mummy ta shigo cikin dakin tana cewa "lafiya "hankalin ta duk ya tashi,ta rasa inda zata sakani sai tambaya ta yakeyi mai ya faru amma na kasa ansa mata ballantana in mata wani magana,addu'o'i kawai ta fara mun har na samu na koma bacci,sanda na tashi da asuba da kuka sosai na tashi,ina sallah ina kuka,ina idarwa nayi azkar din bayan sallahr asuba sannan na kara karanta wannan addu'ar wanda a kullum ina ganin alfanun shi

‎لا إله إلا ﷲ العظيم الحليم,لا إله إلا ﷲ  رب العرش العظيم,لا إله إلا ﷲ  رب السموات ورب الارض ورب العرش الكريم

_La'ilaha illallahul azimul haleem,la'ilaha illallahu rabbul arshil azim,la'ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kareem._

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,mai girma(wanda babu abin da yake girmama a gareshi),mai hakuri (mai jinkirin azaba tare da cikakken ikon aiwatar da ita).Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Ubangijin Al'arshi,mai girma.Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Ubangijin sammai,Ubangijin kasa,Ubangijin Al'arshi mai yawan baiwa.

‎اللهم رحمتك أرخو فلا تكلني إلى نفسي طرفة عين وأصلح لي شأني كله,لا إله إلا أنت.

_Allahumma rahmataka arjuw fala takilniy ila nafsiy darfata ain wa aslihliy sha'ni kullahu,la'ilaha illa anta._

Ya Allah!Rahamar ka nake kauna,don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne,kuma ka kyautata mini sha'anina dukkansa,babu abin bautawa da gaskiya sai kai.

‎لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين

_La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzwalimin_

Babu abin bautawa da gaskiya sai kai.Tsarki ya tabbata gare ka,lallai ni na kasance daga cikin azzalumai

‎ﷲ  ﷲ  ربي لا أشرك به شيأ

_Allahu,Allahu rabbi la ushriku bihi shai'an_

Allah!Allah ne ubangiji na,bana yin tarayya da shi da wani abu acikin bauta

‎اللهم لا سهل الا ما جعلته سهلا و انت تجعل الحزن اذا ش ات سهلا

_Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna shi'ta sahlan _

_Ya Allah!Babu wani abu mai sauki sai abinda ka sanya shi yayi sauki,kuma kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sauki._

Bayan na gama na kasa komawa bacci kuka kawai nake yi,narasa mai yasa hakan take faruwa a cikin rayuwa ta,daga wannan sai wannan,da wannan bala'in ya wuce sai kuma wata ta kunno kai,kai wai yanzun ace mijin mahaifiya ta ce yake nema na,wayyo Allah na wayyo rayuwa ta,ina zan saka raina inji dadi,mai zanyi inji dadin rayuwa ta,wa zan fada ma damuwa ta ya share mun hawaye na ,ya Ubangiji gani ni baiwar ka a gabanka ina rokon ka ka share mun hawaye na,ka kawo mun mafita a cikin wannan halin danake ciki,wani kuka ne naji ya kara zuwa mun,Maryam dake gefena tun dazu tana zaune,ta juyo tana kallo na,rokona take yi akan in fada mata meye damuwa na,da kyar na iya fada mata,abin ya firgita ta da bata mamaki da kuma tsoro,ba tayi kasa a gwiwa ba ta isa dakin mummy dan sanar da ita abinda ke faruwa...........


Yawan comment, yawan typing

SHARE FISABILILLAH

Zahraty ❤️
08063304625

ANAYAHWhere stories live. Discover now