Chapter 2

303 22 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA !!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

          *Chapter 2*

              ~Gwada tashi tayi taga bazata iya ba, da rarrafe tafara tafiya tana Nishi da kyar, jini ne yake zuba daga kasanta Yana sauka Yana b'ata jikinta, ruwan samane yake wankewa, duk wurin yab'aci da jini, da rarrafe da ja da ciki tabar lungun, bread d'in ma batasan inda ta yasar ba, jikinta rawa yake sosai, ganin bazata iya kikewa ba yasa ta zauna ruwan yayita dukanta, Saida ruwa yad'an tsaya kafin tamike tafara tafiya tana ware kafarta kad'an kad'an, kuka takeso tayi Amma takasa, a zuciya take ta kuka Wanda har yafi na ido zafi, da kyar Allah yasa takarasa gida, shiga tayi tana rarraba ido gaba d'aya a firgice take, Baba ne yafito daga d'aki yace "kamar motsin mutum nake ji" jin anyi shiru yasa yaciro toci daga Aljihunshi yahaske, ganinta tsaye yasa yace "AMAL" kallonshi kawai take kara haskata yayi yace "Ina bredin?"
Shiru tayi tana kallonshi idonta ne ya bushe, yace "lafiyanki?"
Batayi magana ba, ta wuce wani d'aki dayake gefe, shiga tayi tafada kan wani tabarma dayake shinfed'e a tsakar d'akin, a hankali tace "Ya Allah kasa nay kuka, Allah inason nayi kuka, ka taimaka kasa nayi"
A hankali taji idonta yafara cika da hawaye, da sannu hawayen yafara sauka Yana wanke Mata fuska, jitayi tafara samun numfashi me kyau daganan tafara jin sauki, zafin datake ji a jikinta ne yake Kara dad'uwa,
Baba turo kofar yayi yashigo d'akin, da tocin hannunshi ya haskata yace "Mamana" kina lafiya?
A lokacin tasamu bakinta ya bud'u saide muryarta Yana rawa tace "Eh"
Cikin sanyin jiki yace "Lafiyanki kalau?"
A hankali takuma cewa "Eh"
Yace "Ina bredin da Mamanki ta aikeki?"
Cikin rawar murya tace "na fad'i shine bredin ya fashe ya b'aci da cab'i"
"Subhanallah sannu bakiji ciwo bakam?"
Tace "a gwiwana naji ciwo Amma ba sosai ba"
Yace "sannu Mamana tashi ki girka ruwan zafi kiyi wanka zakid'an samu saukin sanyin, kinji?"
Gid'a mishi Kai tayi, Amma taki mikewa, Saida yafita kafin tamike da kyar tashiga kitchen, wuta ta hura sannan ta girka ruwa, Zama tayi a gefen wutan tana kallon yanda wutan yake ci, yatsanta d'aya tasa acikin wutan, a hankali ta rufe ido tanajin zafi, da sauri tacire bayan yatsan yad'an kone, rad'ad'i hannun yake Mata cikin kuka tace "Wannan zafin wutan haka nakeji acikin zuciyata, waye ze taimakamin ni Amal? Tun Ina yarinya nake fuskantar kalubalen rayuwa" kwanciya tayi cikin kasan tafara kuka, tace "Yaya Mukhtar Ina kake? Kazo ka ceci kanwarka daga wannan masifar data fad'a, meyasa zaka tafi ka barni acikin wannan bala'in? Kasan ni yarinya ce bazan iya d'aukan wani wahalan ba"
Kuka cin karfinta yake sosai, takata taji anyi da karfi ta tsala ihu, ganin matar Babanta a tsaye kanta yasa ta tashi ta zauna, a hankali tace "Mama?"
Cikin masifa tace "wacece mamar taki? Allah ya tsareni da haifar yarinya irinki, to ai gara da Allah be bani haihuwan bama akan irin wannan haihuwar da uwarki tayi kuma ta mutu tabarwa mutane Ala kakai, yanzu bredin Dana aikeki siyowa kika samu wuri kika zauna sannan kika cinye shine kika kwaso jiki se gida ko?"
A hankali tace "A,a Mama fad'uwa nayi..."
Kafin takarasa ta buge Mata Baki tace "rufemin Baki banza me kama da mayu, fuska jaa kamar mecin naman mutum, yo to ma waya sani ko kece kika cinye uwarki"

Kuka take sosai Bata kula ta ba, Saida tagama masifarta kafin tajuya tafice daga kitchen d'in, da ihu tace "Yaya Mukhtar Dan Allah kazo ka taimaka min"

             "Mukhtar yakasance Yayan Amal ne Wanda suka fito ciki d'aya, yabar gidan Mahaifinshi ne sanadiyyar sharrin da Matar Babanshi tayi mishi, shida kanwarsa Amal, Abin yafarune kamar haka, wata Rana Da dare Amal cikinta  Yana ciwo sanadiyyar Period dayazo Mata, tana kuka babu Wanda yazo ya dubata, Mukhtar dayake kwance a d'akinshi yafito yaji kukan nata, d'akinta yashiga yaga yadda take birgima har tafara ihu, riketa yayi cikin tausayi yace "Kanwata meya sameki?"
Cikin kuka tace cikina"
Bankad'o kofar akayi Nan sukaji Ana salati, Mama ce da Baba tsaye kansu, ran baba yayi matukaf b'aci da ganinshi zaka fahimci hakan, cikin masifa yace "shine tarbiyyar Dana koya muku Mukhtari?"
Cikin fashin gahimta Mukhtar yace "Ban ganeba Baba.."
Kafin yakarasa yaji naushi cikin bakinshi, duka baba yafara yimishi tareda tunzurashi zuwa waje, Mama ko ta tsaya tana kukan munafurci a gefe sabida itace tahad'a komai, Saida Baba yayiwa Mukhtar dukan fitar rai kafin ya turashi waje yace "duk ranar daka Kara shigomin gida saina kasheka"
Amal na kwance sai miko hannu take Dan bazata iya tashi ba, hawaye yanabin kuncinta,
Mama cikin munafurci tazo ta d'agata takaita band'aki sannan tahad'a ruwa me zafi taje ta wanketa, Amal na nokewa sabida tanada kunya sosai Amma haka mama tayi Mata wankan, Saida suka fito daga band'aki mama takallli Baba tace "Fyade yayi Mata, kaga har yanzu jini yaki tsayawa"
Amal cikin kid'ima tace "A,a wlh yaya...."
Baba ne ya d'aga Mata hannu sannan yace "daga yau idan kika Kara ambatar sunanshi a gidannan Allah ya isa"
Ranar Amal tayi kuka har tace dama Allah ya d'auki rayuwarta.
Wannan shine sanadiyyar barin yayanta Kuma Wanda yafisonta fiyeda kowa barin gidan mahaifinsu,
Daganan Mama tafara yad'ata cikin garin cewar Suna lalata da Yayanta, hakan yasa iyayen Yara dayawa suka Hana yaransu tafiya da Amal wannanne yasa take rayuwarta ita kad'ai.

*Asalinsu*

'yan garin Kano ne, mahaifinsu Bafulatani ne, sunanshi Malam Sulaiman, mahaifiyarsu Buzuwa ce, wacce mahaifin ya aura sabida kyaunta, lokacin da ya aureta batajin hausa da hankali ta koya, 'yar asalin Nijar ce, yanayi yasasu zuwa Nigeria, Sunanta Maryam, suna kiranta da Umma, Yaro d'aya Maryam ta Haifa da sulaiman, sunan mahaifinta akasa Mukhtar,  Malam sulaiman yaso Maryam sosai, saide a lokacin iyayenshi sukace dole saiya auri 'yar Asalin Nigeria Kuma 'yar Kano, badan yaso ba, suka aura mishi Aisha, wacce Mukhtar yake kira da Mama, Tun shigowar Aisha gidan Suka fara fuskantar kalubale, Aisha Biye biyen bokaye da malaman tsubbu yasa tayi tasiri a zuciyar Sulaiman, da haka tafara cusawa Umma Bakin ciki har hawan jini ya kamata, Sulaiman ya tsani Maryam, gashi babu danginta kusa, wuri daya take samun farin ciki shine Wurin danta Mukhtar, ahaka cikin mawuyacin hali tasamu cikin Amal, Nan hankalin Aisha yatashi tafara kokarin ganin ta zubda cikin, Amma ta Allah ba tata ba, Saida Allah yabaiwa Maryam Daman haifan 'yarta tasa Mata suna Fatima wato Mahaifiyarta Amma Ana cemata Amal, saide ita tana kiranta da Mamana, bayan haihuwan Amal da sati D'aya, Malam sulaiman yace ya saki Maryam, bugun zuciya yasa tafad'i daganan Bata Kara mikewa ba har Allah yakarbi rayuwarta, Mukhtar yayi kuka sosai, a lokacin ya rungumi kanwarshi Amal, yafara Bata gata, Wanda idan tana kuka Shima Sai yayi ta kuka, sannan baya bacci har sai ya tabbata itama tayi, Nan Aisha tafara Bakin cikin hakan, wahala iri iri take baiwa Mukhtar Amma hakan be hanashi kulawa da kanwarshi ba, Saida Allah yasa Amal takai shekaru goma sha bakwai kafin Aisha wato matar Babansu tarabashi da kanwarshi sanadiyyar sharrin datayi mishi.

_Wannan kenan_

   *Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

MUTUNCINA!!!Where stories live. Discover now