🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸_Book one free_
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 19**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________**Paid Book*
~Zama tayi akasa wurin Bama tason tashiga gida, Bama haka ba tasan koda ta mike da wuya kafafuwanta su iya takawa ji take sunyi mata mugun nauyi, yara tagani sunzo wurin suna wawa akan Goro da cingum ɗin da aka tanada domin ɗaurin Aure,
Wani katutun bakin cikine ya sauko mata daga ƙwaƙwalwarta har zuwa cikin zuciyarta,
Maryama itace Kawarta na unguwa zuwa tayi wurin tariko hannunta "Ki tashi ki shiga Gida Amal zamanki a titi bazai kareki da komai ba sai zagin dazaki kara jawa kanki"
Share hawayenta tayi ta ɗago tana kallon Maryaman, rigan daya rufe ciwon dataji a kafarta taɗan ja kaɗan, ciwone babba a kafarta kuma alama yanzu taji dan jini sai ɓulɓula yake, "Maryama kiga naji ciwo kafata sai jini take"
Tausayinta ne ya ɗarsu a zuciyar Maryama da muryan lallashi tafara baiwa Amal hakuri "kiyi hakuri ciwon zai warke"Hannu Amal tasa a kunnenta ta toshe, bama tason jin magana daga bakin kowa, zuciyarta tafarfasa kawai take,
"Yakamata kije asibitin da aka kai Babanki"
Da sauri ta mike dan tsabar tashin hankali har ta manta da cewar an tafi da Baba Asibiti, jiri taji yana shirin kadata kasa, dafe bangon dayake gefenta tayi, domin tanada buƙatar dauriya a wannan lokacin."Awani Asibiti aka kaishi?"
Tafaɗa muryanta na rawa,
"naji Unty Laila tana cewa specialist aka kaishi"
Bata jira komai ba tafara tafiya zuwa bakin hanya domin samun abin hawa"Kibi a hankali kada ki faɗi"
"Gara nafaɗi dana rasa mahaifina"
Tafaɗa tana tangal-tangal kamar wacce tasha abu
lallen kafarta da hannunta duk sun ɓaci da kasa, hannu tafara ɗagawa daidai lokacin data iso bakin hanya,
"Hajiya ina zuwa?"
Wani madaidaicin me Daidaita sahu ne yake tambayarta."Specialist Hospital"
"Shiga muje"
Dogayen kafarta masu ɗauke da zanen fulawa ta zira cikin Napep ɗin, zama tayi tana kallon titi, bata damu data share hawayen dayake sauka a idonta ba mutane sai kallonta suke dukda acikin Napep take amma hakan bai hana a gane tana kuka ba,
Suna isa bakin Specialist tafita, "Hajiya kuɗina fa?"
Daradaran idanuwanta wanda suka cika da hawaye ta ɗago tana kallonshi, "Hajiya kuɗina nace"
"Dan Allah kayi Hakuri banida kuɗi, idan nasamu zan baka ko kuma kaje Gidanmu ka karɓa yanzu matsala ce ta fito dani ba shiri"
Tafaɗa tana kokarin tafiya domin gaba ɗaya hankalinta yanakan Mahaifinta so take taga wani hali yake ciki yanzu,
"Ban gane Bakida kuɗi ba, dama kinsan bakida kuɗi kika shigamin Napep? Wallahi saikin biyani kuɗina"Tafiya tayi tabarshi tsaye wurin yana kiranta ko juyawa batayi ba,
Cikin asibitin nada girma, hannu tasa tariko gefen hijabinta tana kallon mutane gabanta na faɗuwa kirjinta na bugawa ga kuma kanta dayake sarawa kamar ba'a jikinta yakeba,
"Dan Allah ƴar uwa ko kinga wani mutum wanda aka kawo yanzu?"
"Eh kamar na gansu a Icu intensive care unit"
Cewar madaidaiciyar matar da Amal ɗin ta tambaya...Kafin ma takara Amal tabar wurin har tana haɗawa da ɗan gudu-gudu, Saida ta isa kafin taɗan nutsu kaɗan sanin cewar likitoci basason kaje gun mara lafiya a firgice, a hankali tafara tafiya tana shiga ta buɗe kofar bakinta ɗauke da sallama, ido huɗu sukayi da Baba wanda ya jingina bayanshi jikin gadon da aka kwantar dashi
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.