Chapter 10

212 18 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

   
  *Chapter 10*

   
                 ~Nabil yafara aiki acikin Company d'in mahaifinshi wato Mailafiya, Company ne Wanda suke sarrafa rake wato Company na sugar, shine manager acikin company inda yake d'auke da ma'aikata masu tarin yawa, office nashine Babba Wanda Abba ya kayata mishi da kayan more rayuwa, office ne Amma Kamar d'aki sabida yanda aka tsara, kayan cikin office d'inma Abba ne yayi mishi order daga kasar waje sabida yanaso yaga d'anshi ya maida hankali akan al'amuranshi, yanason yaga Nabil yazama abin Alfahari acikin Al'umma, hakanne yasa ya tsara mishi company Kamar a kasar Turai, idan kashiga ciki zaka rantse ba'a Nigeria bane, yau yakama Monday ranar da ko bature tsoronshi yake, Nabil ne yafito daga gida jikinshi sanye da Bakin suit bakaramin kyau yayi ba domin yafito kamar Wani bature, jakan zuwa office ya rataya a gefenshi na dama Yana tafiya cikin Isa dakuma samartaka, yanada kwarjini sosai hakanne yasa ake bashi girma dadaraja aduk inda yaje, motarshi yashiga sannan yayi Horn, baba megadi ne ya bud'e mishi get daganan yafice agidan Yana tuki a hankali, yayi tafiya me nisa kafin yatsaya a wurin Mailafiya Company wati Company d'in dayake aiki aciki, Shiga ciki yayi Parking a wurin ajiyar motoci, ganinshi yasa kowa ya nutsu ya bar abinda yakeyi, duk inda yawuce gaisuwa ake aika mishi, saide ya d'aga hannu yawuce kawai, awurin daze shiga ya tsaya Yana kallon wani me yanke flowers, da hannu yakirashi, Yana zuwa yadurkusa kasa yace "yallab'ai gani"
Kallonshi Nabil yayi wani d'an tsohone kad'an, cikin Isa da tak'ama yace "Baka ganina ne da zaka tsaya daga gefe bazaka gaisheni ba?"
Mutumin yace "kayi hakuri yallab'ai wallahi na sha'afa ne da aikin danake"
Yace "Nabaka hutun kwana biyu"
Cikin tashin hankali mutumin yace "Dan Allah kayi hakuri ka gafarceni wallahi bawai da gangan naki gaisheka ba"
Shafa kwantaccen Sajen dayake fuskarshi yayi, Wanda yake kara fito kishi da Asalin kyaunshi na jinin Fulani dakuma jinin Shuwa Arab,
Yace "nakara kwana biyu yazama hud'u kenan"
Mutumin yace "kayi hakuri yallab'ai"
Yace "nakara biyu yazama shida"
Shiru yayi Dan yasan Yana Kara bud'e Baki zece yakara daganan har ya koreshi gaba d'aya, office nashi Yana sama, stairs d'in yafara Hawa, office d'inshi yashiga Wanda yake sama kafin ya zauna akan kujeran dayake jujjuyawa dashi, waya yad'aga ya latsa wasu nombobi yace "Coffee"
Bayan minti biyar saiga wata budurwa tana sanye da farar riga dawani guntun siket hannunta rikeda Cup, da ganinta kasan ma'aikaciyace acikin company d'in, knocking tayi yace "yes coming"
Shiga tayi ta ajiye Cup d'in a gabanshi sannan tace "morning sir"
Yace "morning" juyawa tayi zata fita yace "Jennifer"
Dawowa tayi cikin girmamawa tace "Sir"
Be ko kalleta ba hankalinshi akan Computer din dayake gabanshi yace "Bance ki daina sa wannan guntun siket d'in ba?"
Cikin girmamawa tace "sir naje kasuwa siyan dogo Amma ban samu ba"
Ranshi ne ya b'aci yace "Kuma bazaki iya d'inkawa ba"
Kallon kasa tayi tace "sorry sir"
Drawer dayake gabanshi ya bud'e yaciro kud'i sabbin dubu d'aya d'aya rapper biyu yace "gashi gobe kada kikara shigomin da wannan siket d'in duk yanda za'ayi yau kije ki Nemo dogo Koda a kasar waje ne"
Kasa ta durkusa tace "Thank you sir"
Ko kallonta bayayi kawai ya gid'a Kai, fita tayi daga office d'in Nan yafara aikin dayake gabanshi cikin computer, Kokarin had'a hannun jari yake da wani Company a Egypt sabida ya yaba da kasuwancin company d'in, sako yatura musu ta G-mail, cikin sa'a Kuma yaga sun mayar mishi da amsa, dad'i yaji domin yasan Addu'arshi zata karb'u, Nan sukayi exchanging din number da meshi, ba b'ata lokaci yakira sannan suka fara magana shida mutumin cikin harshen turanci,
Nan yayiwa meshi bayani cewa yanaso ne suhad'a hannu idan ba matsala, Mr Gang dama yanason cigaban Company d'inshi musamman da 'yan Nigeria, ya amincewa Nabil da sharad'in zai zo har Nigeria yaduba yanayin Company d'insu, Nabil ya amince cike da farin ciki,
Be fad'awa Abba plan d'inshi ba sabida so yake yayi surprising d'inshi,
Nan yafara gudanar da aikin dayake gabanshi, karfe 1:30 yatashi yafita zuwa d'auko Noor baya yadda da driver kwata kwata yafison yayi tuki da kanshi kuma yafison ya d'auko kanwarshi da kanshi daga school sabida bayason wani Abu Mara dadi ko Mara kyau yafaru da ita, Kamar kullum tsayawa yayi abakin get na school nasu Yana jiran tafito, ganinta yayi itada kawayenta Wanda yasaba ganinsu tare, karasowa sukayi duka, bud'e motar Noor tayi tace "kuzo ku gaida Yayana"
Nokewa suka farayi sabida sunsan halinshi be fiye dariya ba, ganin ranta Yana b'aci yasa suka bud'e motar su biyu suka shiga, cikin tsoro sukace "Good Evening"
Kallonsu yayi tacikin madubi ganin yarane sa'an Noor yasa yace "Fine how you?"
Sukace "Fine"
Fita sukayi suna kallonshi ta gefen ido Dan wallahi suna tsoronshi, chocolate yaciro yabawa Noor sannan yace "Basu"
Mika musu tayi tace "wai gashi"
Tare sukace "Thanks you"
Shiga motar Noor tayi ta zauna shiru, key yasa sannan yad'au hanya, kura'a ya kunna kad'an kad'an akeji, shiru sukayi gaba d'aya Noor sai kallon marfin mota take, juyowa yayi kad'an ya kalleta, ganin Kamar akwai abinda yake damunta yasa yariko hannunta beyi magana ba, shiru har yanzu tayi yakara kallonta, Kara kawar dakai tayi, ya murza hannunta da karfi, cikin jin zafi tace "wash Yaya hannuna"
Yace "meyafaru kike had'e fuska?"
A ranta tace "idan kayi surutu yace ka dameshi kayi shiruma yace meyake damunka shikam Yaya wani irin murd'ad'd'en mutum ne?"
Yace "umm meya sameki?"
A hankali tace "Friends d'ina idan naje gaida Brother d'insu sakemin fuska suke muyita Hira har suna tambayata yaya karatu Kai Kuma idan su Elham sunzo gaisheka saika rinke turnike fuska har basason zuwa"
"Okay shiyasa kike had'a fuska?"
Tace "Eh"
Sakin hannunta yayi yace "to kiyita had'awa"
Har suka Isa gida bece komai ba itama fushi tayi dashi sosai, Saida ya ajiyeta sannan yad'au abincinshi yakara komawa office"
Noor tasan baze tab'a canja hali ba.

   *Wattpad*
Jiddah S Mapi

MUTUNCINA!!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora