🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 6**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim~Saida tayi me isarta kafin bacci ya saceta, cikin baccinta tarinka mugayen mafarki, a firgice ta tashi ta tofa "Auzubillahi minashaid'anirrajeem" sau uku a gefenta na hagu, daganan ta canja yanayin kwanciya kafin bacci ya d'auketa, yanzu Kam tayi bacci me kyau Wanda har tana kyawawan mafarki
_wannan kenan_
"Abbanku yakira yace yau ze shigo"
Noor ce tayi tsalle tace "ye Abba ze dawo"
Hararanta Ammi tayi tace "dama tanan kikafi kauri ai, indai Abba ne kina gaba Amma banda Ammi"
Hannu tasa a kunne tace "a gafarceni Ammi"
Tab'e Baki Ammi tayi sannan tawuce zuwa sama.Kwance yake akan lallausan katifar datake shinfid'e akan makeken gadonshi na Alfarma, Jikinshi lullub'e da farin blanket ya rufe har kanshi Yana bacci cikin kwanciyar hankali da hutawa, mirginawa yayi sannan ya janyo filo ya rungume, yamutse fuska yayi Kamar baccin yanaso ya isheshi, be bud'e ido ba Amma yacire kanshi a blanket d'in,
Noor ce tashigo d'akin da gudu tafad'a kan gadon, rungumeshi tayi tana dariya, d'an tureta yayi yace "matsa da Allah meyafaru?"
Kin matsawa tayi takara rikeshi tace "Abba ze dawo yau"
Kyaleta yayi bece komai ba, dukda yaji dad'i da akace Abba ze dawo saide yasan zed'an shiga takura kad'an, mikewa yayi yace "To sakeni naji Allah yakawoshi lafiya"
Sakeshi tayi sannan ta dira akan gadon tafice da gudu, girgiza Kai yayi yace "Noor bakya girma"
Sauka yayi dagashi se wani gajeren wando na bacci, toilet ya shiga sannan ya tari ruwan zafi, sirkawa yayi kafin yayi wanka da sabulanshi masu kanshi, Saida yagama wanka kafin yashafa wani turare Wanda Mamanshi na Maiduguri ta tura mishi, turarene me kamshin gaske, da karama towel a kanshi yafito Yana tsane gashin kanshi, wurin had'addiyar wardrobe d'inshi yanufa, bud'ewa yayi yaduba wurin manyan kayanshi sannan ya d'auko wani Shadda Brown, lafiyayye Wanda yasha zubin hannu irin na 'yan Maiduguri, Saida yaje wurin dressing mirror d'inshi kafin yashafa lotion me had'e da kulaccam, mataji ya d'auka ya taje gashin kanshi, man gashi ya d'auka ya shafa a hannunshi shafewa yayi a kanshi nan gashin yafara shek'i, sajen dake kwance a fuskarshi ya aje Nan kyaunshi na Asalin bafulani yafito, wurin kayan yaje ya d'auka tareda sawa a jikinshi, ya karb'i jikinshi ba wasa saide yayi tsaki a ranshi yace "yanzu zan takura"
Hula Dinkin Bama yasa a kanshi sannan ya d'auko wayarshi da makullin Mota a hannunshi Yana kad'awa, fita yayi yanufi d'akin Ammi, Ammi na zaune akan Sofa tana kwance kitson kanta, ganinshi yasa ta tsaya da tsifan tace "Nabil Ina zuwa?"
Saida yazo ya zauna a kasa ya d'aura kanshi a cinyanta sannan yace "Ammi na zanje nad'auki Dady a airport ya kirani yanzu"
Ammi tace "To Masha Allah sunyi shigowar safe kenan?"
Yace "um"
Hulan kanshi ya cire baida alamar tashi, ganin haka yasa tace "to me kake jira jeka d'aukoshi mana"
Shiru yayi sannan yace "Ammi kinsan Abba da takura yanzu ze fara yimin fad'a ba gaira ba dalili Kuma Ni banason hayaniya wallahi"
Shafa kanshi tayi tace "Mahaifinka baze tab'a yimaka fad'a batareda dalili ba, Kuma idan kayi hakuri ai baze dadeba ze Kara tafiya ko?"
Gid'a Kai yayi Alamar "Eh"
Tace "to tashi kaje ka d'aukoshi"
Tashi yayi sannan yasa hulanshi yace "saina dawo"
Tace "adawo lafiya"
Fita yayi yanufi wurin parking wata farar mota ya d'auko kirar Benz glass d'inshi Tinted ne, horn yayi megadi ya bud'e mishi get, fita yayi yau Yana tuki a hankali, kira'ar alkur'ani daga Bakin Sudays yasa, abin mamaki bin suratul Yusuf yake babu b'ata, har wani lumshe ido yake Dan yanda karatun yake shiga jikinshi,
Cikin nutsuwa ya iso airport d'in da Abba yake, parking yayi sannan yafito daga motar, wayarshi ya d'auka yakira number d'in Abba, a hankali yace "na iso Abba"
Abba yace "Kaine kashigo yanzu"
Yace "eh Abba nine"
Cikin jin dadi Abba yace "To juya bayanka ka ganni"
Juyawa yayi ganin Abba tsaye Yana mishi murmushi yasa yaji wani irin dad'i acikin zuciyarshi, da sauri ya karasa wurinshi ya rungumeshi cikin jin dadi, Abba Yana dariya yace "my son Kaine ka Kara girma haka?"
Yace "Abba yadda nakefa haka nake har yanzu Kaine kaga na canja"
Cikin tsokana Abba yace "A,a yanzu Kam ka girma saura Aure"
Rufe fuskarshi yayi Alamar kunya, murmushi kawai Abba yayi yace "Ya gida yasu Ammin ka?"
Yace "suna lafiya"
Bud'ewa Abba mota yayi Saida yashiga ya zauna kafin yaje ya janyo Akwatin da Abba yataho dashi" boot ya bud'e yasa Akwatin aciki sannan ya zagayo yashigo motar, Zama yayi yace "Abbana kasha hanya, ya London?"
Abba yace "Toh London dai babu dad'i sabida babu Amminku awurin"
Dariya yayi yace "Abba kenan Ammi kad'ai kayi missing?"
"A,a har daku Amma nafi yin na Fatimana"
Murmushi Nabil yayi Dan yasan halin Abba idan soyayyar ta tashi musu dagashi har Ammi ba nauyinsu sukeji ba, unguwarsu suka shiga, shiru unguwar babu ruwan kowa da kowa, Zakayi wata ma bakaga makocinka ba, abinka da unguwar masu kud'i komai nadu dabanne, manyan gine gine suka wuce sannan suka iso Babban gininsu suma, Abba ganin gidanshi yasa yace "Home is Home"
Nabil yace "This is true Abba nima idan nayi tafiya missing d'in gida nake sosai"
Megadi ne ya bud'e get, tsayawa yayi Abba ya sauke glass yace "barka dai Baba"
Baba megadi cikin murna yace "Barka dai Alhajin Allah, yaushe a gari?"
Yace "yanzu saukana"
Cikin girmamawa suka gaisa, shikuma Nabil hankalinshi ya mayar akan wayar dayake hannunshi, Saida suka gama kafin ya karasa dasu wurin parking, fitowa yayi ya bud'ewa Abba motar, fita Abba yayi sannan ya bud'e boot yaciro Akwatin, shiga gida sukayi, suna shiga wani kamshi ya bugo hancinsu, Abba yace mutanen Borno kenan akwai son kamshi, kaga bambanci tsakanin Yan Borno da Kuma wasu?"
Suna shiga cikin babban falon dayake kasa, Ammi ta karaso wurin Abba, Tasha wani leshi pink color Wanda yasha d'inki me kyau, kwalliya tayi me kyau gata fara, d'ankwali tayi mishi d'aurin gwaggwaro, wani sarka ne a wuyarta siriri na gwal Yana shining da abin hannunshi dakuma zobe da d'an kunne, kamshi take kamar Amarya, da sauri tazo ta rungume Abba, cikin jin dadi da kewa Shima ya rungumeta Kam Kam, Nabil tsayawa yayi abakin falon Yana kallonsu, idan yaga iyayenshi cikin wannan yanayin Sai yaji wani dadi Yana riskanshi,
Noor ce tafito da gudu hannunta rikeda siket d'inta gajeran wandone ajikinta jin muryan Abba yasa takasa tsayawa tasa siket d'in, rungumesu tayi duka tana murnan ganin Abban, Abba ganin Nabil tsaye yasa yayi mishi alama da Shima ya karaso, karasowa yayi Shima ya rungumesu, Abba cikin jin dad'i yace "Allah kada yakawo abinda ze tarwatsa wannan jin dad'i dakuma farin cikin wannan Family d'in"
Tare sukace "Ameen"*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_
VOUS LISEZ
MUTUNCINA!!!
Roman d'amourA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.