🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 9**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim~A kwana atashi ba wuya Amal sunyi kusan sati tareda Hafeez, yanzu rayuwarta tad'an fara dad'i data had'u da Hafeez sanyin idanunta, yauma Kamar Kullum zaune suke a karkashin bishiyar kofar gidansu, Hafeez yasa jampa da earpiece a kunnenshi, yayi kyau sosai, kallon Amal yayi datake gefe yau ba laifi tasa wani hijabi me kyau Purple color, waya yaciro daga aljihunshi katuwa yamika Mata, kallonshi tayi batayi magana ba Kuma Bata karb'a ba, yace "Karb'a mana"
Tace "na waye?"
Yace "nakine aciki zamu rinka waya Kuma zamuyi chatting"
Girgiza Kai tayi tace "A,a Baba zemin fad'a Kuma Mama zata kwace ta fasa"
Wani irin tausayin yarinyar ne ya d'arsu a zuciyarshi, Haka kawai take bashi tausayi kana ganinta So Emotional, yace "Na fad'awa Baba"
Dariyan daya bayyana kyaunta tayi jin yace yafad'awa Baba, a hankali ta d'ago dogayen yatsunta ta Karb'a cikin jin dad'i da murna tace "nagode ya Hafeez"
Bece komai ba sai d'an murmushi dayayi, yace "d'ago ki kalleni"
D'ago Kai tayi ta kafa mishi ido dama itakam tanason kallon mutum, ido cikin ido suke kallon juna, Saida ya shagala kafin tace "Ya Hafeez"
Dawowa Sense d'inshi yayi yace "Na'am Baby"
Tace "to ban iya anfani da waya me latse latse ba"
Murmushi yayi sannan yace "matso"
Matsowa tayi gefenshi, kunna wayar yayi yafara nuna Mata, dama da watsapp aciki Nan yafara koya Mata yacce ake chatting, bud'e data d'inshi yayi sannan yafara tura Mata sako, ganin sakonshi yana shigowa yasa tafara dariya Wanda yasa gefen kumatunta lotsewa dakuma fararen hakoranta bayyana, Idan tana dariya bayason d'auke idonshi daga kanta hakanne yasa baya wasa da zuwa wurinta yarinyar tafiya take da imaninshi wani irin so yakeyi Mata Wanda shi kanshi baya yiwa kanshi son, cikin murna tariko hannunshi tace "nagode Ya Hafeez"
Janye hannunshi yayi, da sauri ta lurada tab'argazar datayi, sunkuyar dakai tayi zuwa kasa saide har yanzu fuskarta be daina dariya ba sabida farin cikin wayar, "Su Amal anyi waya"
Koya mata yanda zata amsa Kira yayi da yanda zata kunna data Kuma takashe, yace "karki Bari yafad'i sabida screen nashi ba'a fiye samu ba, na saita Miki G_Mail kisa komanki akai, sabida Koda wayar yafad'i zaki samu abinda kikeso a Gmail d'inki"
Tace "nagode, Amma miye sunan wayar?"
Yace "I Phone 13pro"
Batasan meyake nufi ba tace "to nagode"
Ya lura batasan kan waya ba, earpiece da charger yabata sannan yace "nikam zan koma Abbu ya aikeni"
Tashi tayi suka jera rakashi tayi wurin motarshi sannan sukayi sallama, kallonta yayi yace "My Amal Baki fad'amin kalma me dad'i ba"
Gefen Hijabinta taruko sannan ta rufe fuskarta cikin yarinta tace "I Love you"
Murmushi yayi ganin yarinyar akwai yarinta yace "Love you too my Amal, ki kulamin da kanki"
Tace "To kaima haka"
Shiga motarshi yayi tafara d'aga mishi hannu Alamar bye bye, Saida yabar layin kafin tajuya takoma gida, Zama tayi acikin gida tana latsa wayar bakinta yaki rufuwa, Mama datake zaune a kitchen tacika tayi fam sabida Baba ya taka Mata birki tsakaninta da Amal da Hafeez, gashi bataso tafita a gidan sabida batasan Wanda ze hakura ya zauna da ita a Rashin haihuwa Nan ba, Bakin ciki duk ya cikata ganin Amal da katuwar wayar daya girmi hannunta,
Amal kuwa Saida tagama danne danne kafin ta tashi tayi wanke wanke, tayi shara sannan ta goge d'akuna, shiryawa tayi tad'au Awara akanta wayarta tab'oye acikin kayanta sannan tafita talla, sauri tayi yau ta siyar domin tadawo gida ta Danna waya, bata kula su Fati domin ta canja wurin Zama yanzu tasamu wata kawa me hankali wacce halinsu yazo d'aya Sunanta Fauziya, ita Kuma shinkafa da wake take siyarwa, Allah yahad'a jininsu sosai, Amal dawuri ta koma gida, mikawa mama kud'in tayi kafin tafara aikace aikacen cikin gida, Saida tagama tayi Alwala, d'akinta taje tayi salla, sannan tafito tafara girki, Saida tagama girkin kafin tayi sallan isha'i, Baba yadawo taje tayi mishi sannu dazuwa sannan ta gaidashi, d'aki Takoma taciro wayarta, kaiwa Baba tayi tace "Ga wayar da Ya Hafeez yabani"
Karb'an wayar yayi sannan yace "tayi kyau Amma ai wannan wayar yafi karfinki Amal Ina laifin Nokia?"
Shiru tayi yace "To saiki kula domin waya Yana daga cikin abinda yake lalata tarbiyyar Yara a wannan zamanin ki kula sosai kisan yanda zakibi da wayar Nan, idan naga kanki yafara rawa da wannan wayar wallahi kwacewa zanyi inkai mishi abinshi da hannuna"
Tace "to baba nagode"
Karb'a tayi Takoma d'aki"
Ganin Ana Kira yasa ta amsa da sauri, karawa tayi a kunne jin muryanshi me sanyi yasa taji zuciyarta ta buga, a hankali yace "My Amal"
Ciro wayar tayi daga kunnenta takara kallo, yakara cewa "My Amal kina jina?"
Tace "Um"
Yace "Meyasa nayi kusan 5miss calls Baki d'auka ba Ina kika ajiye wayar?"
Tace "na b'oye acikin kayana"
"Ina kikaje?"
Tace "Naje talle"
Ranshi ad'an b'ace yace "banace kidaina wannan tallen ba? Please banaso ki karayi kinji?"
Tace "mama bazata Bari ba""To idan nasaki a makaranta ai zata Bari ko?"
Wani dad'i ne ya ziyarceta jin yace ze sata a makaranta, yace "ko bakya so kiyi ilimi?"
Da sauri tace "inaso"
Dariya yayi ganin yanda ta amsa, yace "to ba komai a cikin week d'innan zaki fara zuwa school"
Cikin jin dad'i tace "nagode ya Hafeez"
Yace "ba godiya nakeso ba"
Tace "me kakeso?"
Yace "Kiss nakeso"
Da sauri tacire wayar a kunneta jin abinda yafad'a, Kara tad'awa tayi tana zazzare ido, abin ba karamin dariya yabashi ba, yasan za'ayi haka dama, yace "bazaki iya ba?"
Cikin sauri tace "bazan iyaba gaskiya"
Yace "To kicemin I love you"
Saukar da murya tayi tace "I love you so much ya Hafeez"
Har cikin ranshi yaji dad'in maganar Shima yace "I love you so much Baby Amal"
Hira suka fara dukda ita dashi d'in duk ba gwanaye bane a surutu Amma sabon da sukayi yasa suke yawan Hira, acikin hiran yace tabashi labarin rayuwarta, shiru Amal tayi Dan jin tambayar tayi bambarakwai, yace "kina tare Dani?"
Jin sheshekar kuka yasa yace "Baby Amal? Kuka Kuma? Menayi Miki?"
Hankalinshi yatashi bayaso yaji Ana kuka musamman mata, gashi Kuma Amal d'inshi ce takeyi hakan ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba,
Amal kuka ne yaci karfinta Dan babu abinda yake cikin labarin rayuwarta banda Bakin ciki da tashin hankali, ta tabbata idan ta gaya mashi labarinta dolene Shima ya gujeta, Kuma bazata iya jure hakan ba, soyayyar datake mishi yayi karfi sosai, batajin zata iya rabuwa dashi, jikinshi ya matukar mutuwa jin yanda take kuka, a hankali cikin sanyin murya yace "My Amal? Ki daina kuka banaso d'agamin hankali kike idan kina kuka, ko so kike nima nayi kukan?"
Girgiza Kai tayi kamar Yana gabanta, yace "to banason nakara jin kina kuka kinji?"
Daurewa tayi tace "Eh"
Yace "yawwa Good Girl matar Hafeez"
Murmushi tayi Wanda har Saida yajiyo sautinshi yace "Bazan Kara yimiki irin tambayar ba kinji?"
Tace "Eh"
Saida ya tabbatar ya lallab'ata tayi shiru harta fara yimishi magana kafin yace ki kwanta to kiyi bacci ko zamuyi chatting?"
Tace "A,a" Domin a lokacin hutu kawai take bukata, yace "to good night kiyi mafarkina Kuma me dad'i kinji?"
Tace "To"
Yace "I love you"
A hankali tace "love you too"
Katse wayar yayi sannan yabi wayarshi da kallo, dama akan gadon Bedroom d'inshi yake kwance, gyara kwanciyar yayi sannan ya janyo wani lallausan filo ya rungume sosai, tunani yafara akan abinda yafaru yanzu tsakaninshi da Amal, tausayi tabashi sosai sabida duk Wanda ya rasa mahaifiya tabbas yayi babban Rashi musamman 'ya mace, to Amma ya ta iya da kaddara?
A zuciyarshi yace "insha Allahu bazaki Kara kuka da rayuwarki ba, zan zamo Miki gata, har sai kin manta mahaifiyarki, Amal Ina sonki sosai banaso naga kina kuka Koda na minti d'ayane, banason naga kina kuka Koda kukan farin ciki ne, nayi alkawarin zamowa farin cikinki da yaddan Allah"Amal kuwa yana kashe wayar tafad'a kan katifar data gyara a tsakar d'akinta tarinka rabzar kuka, tunaninta idan ya aureta ya zata fara kallonshi har tayi mishi bayani?
Cikin kuka tace "Allah ya isa tsakanina da Kai bazan tab'a yafe maka ba Duniya da Lahira, wasu saisu aikata Abu su Basu Damuba kuma baze damesu ba, Amma shi Wanda sukayiwa abun ze iya zama sanadiyyar rasa rayuwarshi ma, Allah kabimin hakkina"
Jitayi Kamar tayiwa Hafeez bayanin abinda yafaru saide tana tsoron rasashi, Dan ko ba komai akwai kishi dakuma zargi, jitake kamar tayi ihu ko zata samu saukin wannan damuwar.*Wattpad*
Jiddah S Mapi
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.