🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸_Book one free_
Na
Jiddah S Mapi*Chapter 21*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Paid Book*~Inna miye zanyi da wannan ganyen?
Innakam kuka take, da zaran Amal tayi magana saita fara kuka, ganin abun yayi yawa tace "Inna kukan me kike haka?"
"Rayuwarki abin tausayine miji ya mutu ya Barka da ciki? Yaya zakiyi da ɗan cikin naki Amalu?"
Amal ta lura matarnan akwai drama, itakam ganyen takeso tasan na menene, saida ta lallaɓa ta da kyar tayi shiru sannan ta ɗago ganyen tana kallo "wannan na menene Amalu?"
Amal tace "Sadauki ne ya bani"
Jeki tambayeshi yaya za'ayi dashi, badan taso ba ta mike, itafa tsoronshi take har zuciya amma yazama dole domin shine yake bata magani, a karkashin bishiyan Gwaiva ta ganshi ya tsinki wata farar Gwaiva yanaci a hankali, a hankali yake bin duk wani me wucewa da ido, karan tsuntsaye yana tashi da alama akan bishiyoyin dasuke zagaye da kauyen ne, a gefenshi ta zauna itama ta zubawa inda yake kallo ido, gwaivan dayake hannunshi taga ya gutsura a hankali yana taunawa, kallon yadda yake motsa baki take, acikin kwanciyar hankali da nutsuwa yakeyin duk wani abunda ya shafeshi da alama baya shiga lamarin kowa, abinda yake gabanshi shi yakeyi, ɗan juyowa yayi ya kalleta ganin yanda ta zuba mishi idanu yasa ya mike yana shirin barin wurin, cikin zazzaƙar muryarta tace "Hamma Sadauki? Wannan ganyen ya zanyi dashi?"
Dakawa zakiyi ki shafa a cikinki, yafaɗa a tsanake sannan yaci gaba da tafiyarshi.To shi wannan wani irin mutum ne? Da farko tayi tunanin kurmane sai kuma yayi magana, gashi ko kallon mutum bayayi idan yana magana, tana zaune a wajen taga yafito cikin shirin kayan Maharba, riga da wandone na gargajiya wanda maharba suke sawa idan zasuje daji, rigan ya amshi jikinshi sosai, gefen hannunshi ya rataye bindiga irin na maharba, kafarshi kuma sanye da takalmin Boot, tafiya yake irin ba mazajen da suka amsa sunansu maza,
Inna ce tafito daga ɗaki tana raka Malam, ganin Sadauki yasa tace "Umaru? Haka zaka tafi baza kayi mana sallama ba? yaushe zaka canja haline Umaru? Hakan dakake bai dace ba gaskiya"
Tsayawa yayi cak Saida tagama kafin yawuce yana cewa "natafi"
Malam yaushe ɗannan zai daina miskilanci ne?Halittane, haka Allah yayishi bazai taɓa canja hali ba, saide Addu'a kawai, cewar Malam,
To Allah ya kiyaye hanya,
Ameen ina Amal ɗin take?"Gani Baba"
Ta amsa lokacin datake karasowa, durkusawa tayi har kasa cikin girmamawa "gani" shine abinda tace,
"Ki kwantar da hankalinki kizauna kiɗauka nan gidanku ne kinji? Idan kin samu sauki saiki koma garin dangin mijinki kinji?
Gaban Amal ne yayi wani irin faduwa jin yace idan ta warke zata koma "to ina zataje? Shine Tambayar datakeyi a zuciyarta, ganin tayi shiru tana tunani yasa Yace "ki zauna anan har lokacin da kikaga dama saiki tafi kinji?"
Giɗa kai tayi cikin jin daɗin maganar tashi, "tashi Kishiga"
Miƙewa tayi tashige ɗaki, gefen gadon Inna ta zauna tareda jingina kanta jikin gadon, hawayene yafara sauka daga idanunta yana bin kumatunta, kirjinta yanayi mata zafi sosai, bayan hannunta tasa sannan ta share hawayen cikin bawa kanta kwarin gwiwa tasa hannunta a kasan maranta tana shafawa tafara magana "Bawai nabarka dan inason mahaifinka ko kai bane, nabarka ne saboda kazamomin shaida, nasan babu ɗan dazaiki mahaifiyarshi, zaka bani goyon baya har musamo ubanka"
Kara share hawaye tayi "wallahi Tallahi na rantse da Allan daya halicci sammai da kassai, sannan yayi rantsuwa da abinda ya halitta saina nemo wanda yamin fyaɗe kuma saina sashi a tashin hankalin dayafi wanda yasani, saika ɗaga hannayenka sama kana roƙan Mutuwa tazo ta ɗaukeka, sai nasa rayuwarka cikin masifa fiyeda wanda kasani, saika durƙusa ƙasa ka rike kafafuwata kana rokan na yafe maka, kamar yadda kasani nayi ranar ɗaurin Aurena.
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.