Chapter 24

299 15 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸

      Na
Jiddah S Mapi

*Chapter 24*

_Wannan littafin na kuɗine ku biya 300 ta nan 6037523268 Hauwa shuaibumapi Keystone Bank, ku turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, masu kati ma zasu iya turo 300 tanan 08144818849_

     *____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

      

               ~Saida taji muryan Inna tana tashinta kafin ta farka tana murza ido, ɗan turo baki tayi tace "sai yanzu Inna?"
Eh sai yanzu kinsan ƴar gidan Talatu babu lafiya to munje muka gaisheta, kuma kika kwanta anan cikin hijabinnan ƙatuwar? Kalli tsabar zafi har kin jiƙa da gumi,
Cire hijabin tayi tana kallon jikinta, matashin cikintane ya bayyana ta cikin zanin data ɗaura a kirjinta, Inna Wanka zanyi,
To bari nakai miki ruwa sai kiyi ko?
Giɗa kai tayi, Inna tafita tahaɗa Mata ruwa masu ɗumi, leƙowa tayi tace "fito to kiyi wankan"
Fita tayi bayan ta zira hijabin ta ɗau soso da Omo, tana fita sukayi ido huɗu, yana tsaye yazuba hannunshi a Aljihu yana kallonta, da sauri ta koma bayan Inna ta ɓuya, "ke lafiyanki?"
"Inna ki ɓoyeni" tafaɗa tana shiga Hijabin Inna, tureta tayi banason iyayi kiwuce kije kiyi wanka, da gudu tashige Toilet ta rufe, shi dariyama taso bashi, fita kawai yayi yabar gidan, bayan tagama wanka ta leƙo ganin baya nan yasa tafito tana tura cikinta daya fara fitowa, ɗaki tashige tashafa mai, wani dogon riga buɗaɗɗe tasa domin samun iska yashiga jikinta da kyau, hulan Fulani tasa wani fari sal tafito ta zira silifas a kafarta tawuce karkashin bishiya, zama tayi, tayi tagumi tana tunanin Hafeez, taso ta cireshi a ranta amma hakan ya faskara, kullum kara tunoshi take, batayi kuka ba domin tayiwa kanta alkawarin baza takara yin kuka akan rayuwarta data wuce ba.

             "Ammi meyasa kike yawan tunani idan akwai wani abu dan Allah ki faɗamin banason ganinki cikin wannan yanayin "kiramin Akeela" Ammi tafaɗa tana cikin damuwa sosai, waya ya ɗaga yakira Unty Akeela, kizo inji Momy shine abinda ya faɗa, kallon Ammi yayi yasan akwai damuwa dan tun safe take Safa da marwa a ɗakinta, gashi ta kori Noor daga gefenta tabbas akwai matsala, Unty Akeela cikin tsoro tashigo Gidan dan tunda ya kirata taji gabanta ya faɗi, tana shiga Falon Nabeel yaje ya rungumeta "Good Evening Bro" bai amsata ba yace "Momee tun da safe take cikin damuwa Unty Akeela na tambayeta taki faɗamin kawai tace na kiraki"
"To jeka zanji da ita" tafaɗa yayinda ta sakeshi, fita yayi daga falon Ammi riko hannun Akeela tayi tace "muje Sama" janta take har suka isa ɗakinta dayake up, buɗewa tayi suna shiga ta rufe harda makulli, zaunar da Akeela tayi akan Bed sannan itama ta zauna, tace "Akeela akwai Matsala"
"Meya faru Ammi?"
Cikin kasa da murya Ammi tace "jiya nayi mummunan mafarki akan wannan abun dana aikata anya Akeela kina ganin zan wanye lafiya?"
Ammi dan Allah ki daina wannan zancen wallahi kina ɗagamin hankali kuma kiga Beel gaba ɗaya hankalinshi ya tashi sabida ganinki cikin wannan yanayin, gashi kinada ciki so kike damuwa yasa ki rasa cikin kiyi biyu babu?

Ammi data rabka tagumi tace "A,a"

"To ki rufa mana Asiri ki manta da abinnan wallahi ko bacci bana iyayi me kyau Ammi dan Allah ki daina ɗaga hankalinki wallahi har mijina yaso yagane cewar ina cikin damuwa" Akeela tayi maganar cikin nuna gajiyawa, Ammi cire tagumin tayi tace "to shikenan na daina Allah dai ya saukeni Lafiya"
Ameen, matsawa yayi daga bakin kofar jin maganar da Unty Akeela da Ammi sukeyi, to wani matsala ne? Me Amminshi Tayi har take wannan damuwar, da sauri yaja da baya ya sauka kasa, part nashi yawuce zama yayi kan Sofa yana tunani, ji yake kamar yaje ya tambayi Ammi meya faru saikuma wata zuciyar tabashi shawarar kada yayi haka domin Ammi zatace yayi mata laɓe, a rayuwa babu abinda ya tsana kamar yaga Family ɗinshi cikin matsala, abin yana damunshi bada wasa ba, wayarshi ce tafara Ruri, kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga "Zuby" shine abinda yafaɗa, ka koma Abuja shine baka kirani ba? Tafaɗa, "eh nakoma"
"Amma Beel You never love me baka sona baka damu dani ba"
"Nataɓa cewa ina sonki dama?"
Shiru tayi dan tasan halinshi idan ta dameshi da magana zai iya kashewa, to yaushe zanzo Abuja? Tafaɗa cikin yauki da kashe murya,
"Anytime you want"
Tace "ko Gobe?"
"Yeah" shine abinda yafaɗa, domin shima yanada sha'awar zuwan nata.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 20, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MUTUNCINA!!!Where stories live. Discover now