Chapter 16

173 15 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸

    
  Na
Jiddah S Mapi

   
*Chapter 16*

     *____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

               ~Jennifer batayi fishi ba zuwa tayi aka buɗa mata skirt ɗin washe gari takara dawowa, yana ganin ko sannu baice mata ba, tace "Morning Sir"
Kallonta kawai yayi be amsa ba tace "Coffee or Lipton?"
Kallonta yayi yace "ke Bakida zuciyane?"
Sunkuyar da kai tayi tace "with due respect abinda kamin banji dad'i ba but yaya zanyi Babana ya mutu yabarni da Mamana da kannena Biyar, babu me kula dasu saini hakanne yasa zan jure duk wani kalubale a rayuwa domin kula da Kannena koda ace kullum idan nazo zaka yanka naman jikina idan dai har bazasu ganiba zan iya jurewa"
Shiru yayi kamar baya jinta, hawayene yakebin idonta yace "out"
Fita tayi jikinta duk a mace tana tausayin kanta sosai, amma tafi tausayin kannenta,
Tana fita yaɗau waya yace "ina neman bayanai akan Jennifer da Gidansu yanzu"
Ba'a jima ba, yaga sako karantawa yayi yagani, jikinshine yayi sanyi, a hankali yaɗau waya yace "Come in"
Shiga tayi kanta kasa tace "gani Sir"
Kallonta yayi yace "as from today kinzama Manager na biyu a wannan Company"
Jennifer tsalle tayi cikin murna da sauri ta rungumeshi tana hawaye, ganin ya murtuƙe fuska yasa ta janye a hankali tace "duk cikin murna ne yallabai wallahi munsha Wahalar rayuwa nida kannena yanzu jinayi kamar an bani kyautar Jerusalem, kasa ta durkusa tace "thanks You sir Allah yasaka da Alkhairi"
Kasa-kasa yace "Ameen, kada kisake zuwa da wannan karin gashin, tace "To sir Nagode"
Zata fita yace "Your Account Number"
Tsayawa tayi ta rubuta mishi yace "wait"
Wayarshi yaciro yamata Transfer, jin karan message a ƴar karamar wayarta yasa ta duba, ganin Alert na 2million yasa ta zauna akasa wurin tana kuka, jitake kamar mafarki takeyi, tashi yayi yafita yabarta a office tausayi tabashi sosai, saida tagama kuka kafin tamike tafice jikinta a mugun sanyaye, acikin Company ta tsefe kanta ta zubar da Attachment ɗin, wata ma'aikaciyar ce talura da Yanayin Jennifer daga jiya zuwa yau ya sauya, tace "Jenni? Meke faruwa?"
A sanyaye tace "Babu" domin bata iya faɗawa mutum sirrinta ba,
"Amma ga alamun abu a fuskarki kuma kice Babu?"
Share hawayen farin ciki Jennifer tayi tace "Ba komai"
Taɓe baki yarinyar tayi sannan tace "In tayi tsami maji"
Shiru Jennifer tayi domin tana tsoron tayi magana Nabeel yazo yaji, gakuma mutanen duniya da faɗe faɗen magana,
A ranar tawuni cikin farin ciki.

          "Biki sai gabatowa yake, shirye-shirye sosai ake agidansu Ango saɓanin gidansu Amarya da take fuskantar tsangwama da baƙaƙen maganganu a wurin Uwar rikonta wato matar Babanta, Gaba ɗaya mama bakin ciki take da Amal ganin yanda take kiɓa tana Zama fresh,
Yauma Kamar kullum Kawarta talatu ce tazo gidan tun safe, Amal tayi musu girki suna kan ci kenan talatu ta ɗibo shinkafa da wake tacika baki dashi, kallon Mama Tayi tace "niko Aisha kina ganin yanda yarinyar nan take zama fresh tana Kara kyau tun kafin tashiga gidan?"
Mama ce ta taɓe baki tace "Hmmm Talatu kenan aini yanzu duk basirana ya toshe yarinya kamar Aljana tun Da datake shan wahala a gidannan jikinta baya nunawa, yanzu ma jikinta ba nuna wahala yake ba, ki ganta kamar jinin larabawa, nifa nafara zargin anya uwar yarinyar nan ba bin larabawa take ba har tasamu cikinta?"
Amal datake wanke-wanke a gefe tana sauraronsu tashi tayi tabar gidan domin ranta ya mugun ɓaci ta tsani a zagi mahaifiyarta,
Akan wani Babban dutse dayake kofar gidansu ta zauna tana kallon masu wucewa acikin unguwar tasu, Maryama ce tazo wucewa taga Amal zaune, zuwa tayi ta zauna a gefenta tace "Hajiya Amal"
Amal tace "Maryama kina nan?"
Maryama tace "Eh naso nazofa amma Na gagara zuwa"
Amal tace "Allah sarki"
Maryama tace "Hmm Amal kinsan meyake yawo acikin unguwar nan kuwa?"
Amal tace "saikin faɗa"
Saida taɗan rage murya alamar Gulma tace "cewa ake wai Babanki ya siyar dake, wai ya baiwa wani me kuɗi"
Amal murmushi tayi sannan tace "Nagode Allah tunda Babana ne ya siyar dani ba baban Wasu ba"
Shiru Maryama tayi dan jin amsar da Amal ta Bata, tashi tayi tace "To Allah ya kaimu ranar biki don ance wai za'ayi gagarumar biki"
Amal tace "Ameen"
Tafiya tayi dan taso taji Gulma amma bata samu taji ba,
Amal abun mamaki yake bata, mutane basa kunyar Gulma basa tsoron Allah suna yaɗa maganganun dayayi musu daɗi kawai, jin wayarta yana Ruri da sauri ta duba taga Fareeda Kawata yana yawo akan wayar, ɗagawa tayi tace "Farida ya kike?"
Farida tace "Lafiya Lau Mrs Hafeez ya Gajiya"
Amal tace "ba gajiya jiya nakiraki baki ɗaga ba, an kawo kuɗin aurena ansa rana saura 3weeks yanzu"
Farida cikin murna tace "Wow kice munada babban Biki"
Dariya kawai Amal tayi,
Farida tace "Yanzu zanje group nazaɓo zani me kyau zamuyi anko, Kinga su Fatima Aliyu sunce acire anko da wuri"
Amal tace "eh to nabar komai a hannunki"
Farida tace "zamuyi kamu ranar Alhamis idan yaso sai mucire ankon Kamu duka rana ɗaya ko?"
Amal tace "Eh idan kin cire ki turamin zan turawa Kannenshi su Abeeda dan sunce zasuyi"
Farida tace "Tom ba matsala"
Sallama sukayi sannan suka kashe wayar, daɗi Amal taji ganin har akwai wacce tadamu da ita har zasu cire anko.

MUTUNCINA!!!Onde histórias criam vida. Descubra agora