🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸*BOOK ONE FREE*
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 17**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*~Bayan ankawo Kaya ƴan uwan Baban Amal suka kirata suka sata a tsakiya suka Zazzauna, Unty Suwaiba itace yayar Baban Amal wacce tasha Nono tabar mishi, Tace "Amal munaso kibamu nutsuwanki da kuma kunnuwanki anan"
Amal wacce duk jikinta ya mutu tasha wani bakin abaya me Adon duwatsu ajiki da ɗan kwalinshi akanta, tayi kyau sosai idan ka ganta kamar kasace ka gudu, a hankali tace"Nabaku Unty"
"To Kinga mu ƴan uwan Babanki ne bazamu taɓa cutar dake ba, kinga gidan da kike Aure aciki?"
Amal tace "Eh"
"To duk zuri'armu babu wanda yakai kwatan kuɗinsu balle Rabi, ko dukkanmu zamu saida kadarorinmu bamu isa mu biyasu abinda sukai mana ba, abinda mukeso dake shine idan kinje gidansu Banda Girman kai, Banda Raini, ki sauke kanki domin ko matsayin ƴar aiki baki kaiba, Ikon Allah ne yasa suka soki a matsayin Suruka, kada kibamu kunya, kinji Amal? Yau nasan da mahaifiyarki tana raye ba karamin faɗa zatayi miki ba domin taga kin kwantar da hankali kin zauna a ɗakinki, Allah dai yaji kanta da Rahama..ya kuma..."
Kuka Unty Suwaiba tafara wanda ya hanata karasa maganar, Unty Laila tace "ki kwantar da hankali ki zauna a inda Allah ya kaiki Amal kinji?"
Amal tace "Nagode" cikin kuka itama tayi maganar._Ranar Alhamis_
Kawayen Amal na Makaranta dana unguwa, ciki harda waɗanda iyayensu suke nisantasu da Amal ɗin, sun taru a gidansu Ankira masu Makeup, sunayi musu,
Amal kuwa Tafeeda Glamour aka kira itace zatayi mata kwalliya, zaune suke a ɗakin Baba Wanda yabata a matsayin suyi shirinsu ciki, Kwalliya nagani na faɗa akeyiwa Amal Wanda kafin agama har mutane sun fara zuwa lekawa ta window da kofa, saida suka rufe kofa kafin suka iya cigaba da kwalliyan,
An gama na kawaye sunyi kyau sosai, kowacce tasa kayanta wanda sukayi ɗinki iri ɗaya dogon Riga fitet gown da gyalle jaa, sunyi kyau sosai,
Can na hango Fareeda tafito daga ɗaki idan ka ganta zaka rantse ba ita bace tayi kyau sosai itama cikin dressing ɗin dakuma Makeup ɗin daya kara fitar da kyawunta, dogon takalmi tasa da ƴar mahuci a hannunta, jakan hannunta jaa, sunyi kyau sosai,
Amal an gama Makeup wani bakin dogon riga wedding Gown tasa, abuɗe sosai sai ɗankwali da aka ɗaura mata step by step, ɗan kunne Red tasa, Igiyar rigar ma an ɗaure da Red, takalminta half cover Red dakuma karamar post shima Red Color, Unty Laila wacce tasha Shadda Fari da Red na ɗankwali itace tazo tayi kyau sosai, rungume Amal tayi tace "kinyi kyau sosai"
Amal tace "Nagode Unty Laila"
Rike bayan rigarta tayi suka fito cikin gida, ganin Kawayenta musamman Fareeda sunyi kyau sosai yasa Amal tasaki wani murmushin daya kara nuna kyawunta, turaren wuta aka bunkasa acikin gidan nasu kamshine yake tashi tako ina, akan wani bench ta zauna, suna jiran karasowan Su ango."Amma Hafeez ka rainamu wallahi, ina kataɓa ganin angon daya riga kowa shiri?"
Wani kyakkyawan saurayine yake maganar yana kokarin sa riga, Shadda ne Red Wanda yasha ɗinkin omo, sauran abokan suma shiri suke sosai, Tsaki Hafeez yaja, yariga yagama shiri cikin Shadda Black color dakuma Red na takalmi da hula shima Red Color, sajenshi yasha gyara sai kyalli yake, da ka ganshi kasan wannan ango ne, hannunshi rikeda wayarshi yanata trying na wani Number, gaskiya Hafeez ya haɗu iya haɗuwa, kallon Abokin nashi yayi yace "kai Muneeb Yaufa kamu na ne, kasan wahalan danasha kafin nakamo Baby Amal kuwa?"
Muneeb wanda ya shirya yanzu yace "To shine akace ka rigamu shiri dan zumuɗi?"
Muneeb ɗinma Wani Ajebo ne kana ganinshi kasan daga gidan kuɗi shima yafito, kallon Hafeez yayi yace "kasan gajiyan danayi daga Airport zuwa nan?"
Hafeez yace "dan Allah Guys kuzo mutafi tunda kun shirya"
Dukkansu Ankon Shadda sukasha Red Color da hula Black ba karamin kyau sukayi ba, kowanne ya ɗauki makullin motarshi suka fita zuwa waje,
Abeeda ce tafito jin sun fara tada mota, itama ankon gidansu Amal tasa, can Fatima ma tafito da gudu dan kada sutafi subarta, itama Fatima tayi kyau sosai, Mami ma tace zataje Amma sai an fara,
Abeeda motar Muneeb suka shiga tace "Ya Muneeb tafiya zakuyi kubarmu?"
Yace "Wallahi Hafeez ne gaba ɗaya ya damemu yahamu shiri me kyau ma wallahi"
Tace "kai Yaya Hafeez akwai zumuɗi idan yayi hakuri fa Gobe za'a daura auren"
Bayan sun iso kofarsu Amal sukayi parking gaba ɗaya motocin tinted ne, Sunkai ashirin da biyu, layin su Amal har yacika da motoci, kowa yana mamakin Inda Amal tasamo miji me kuɗi haka, kowacce sai tura ƴarta take zuwa wurin bikin,
Jin karan tsayuwar motoci yasa Unty Laila da Fareeda suka kara ɗauko kaskon turare suka fara bunkasa hayakin, wani irin kamshine yake zagaya unguwar gaba ɗaya, Mama A'isha nagani ta ɗauko mayafi da makulli alamar da ita za'aje Wurin, Yayarta wacce suke kulle kulle tare itama tana wurin tasha wani atamfa tana rarraba ido, abinda yafi karfinka saide ka zuba mishi ido, ganin Amal ɗin ma kwarjini take musu yasa duk sukasha jinin jikinsu suka fara shirin tafiya kamu,
Amal da Fareeda sune agaba ita Fareeda ta rike bayan rigan Amal ne, jakanta yana hannun Maryam Haidar wato Class monitor ɗinsu,
Sauran kawaye suna biye dasu abaya, tana fita bakin Kofa Hafeez ya hangota, kasa zama yayi a motar atake ya buɗe ya fito, wani abokinshi yace "Please control your self Feez"
Hafeez yace "I can't"
Takawa Amal take aka kawota har gaban Hafeez domin a motarshi zasu tafi,
Riko hannunta yayi sannan yabuɗe mata marfin motar yace "Bismilla mrs Hafeez Yusuf, ɗaga kafarta dayasha kunshi jaa da baki tayi sannan tasa a motar cikin nutsuwa tashiga, rufewa yayi sannan ya zagaya shima yashiga, a gefenta ya zauna jiyake kamar ya haɗiyeta ko zai huta,
Kowa yashiga mota an gama shirya komai, tafiya aka fara cikin nutsuwa da tsari, Direct wurin Kamu aka nufa,
Ango sai kallon Amaryarshi yake jiyake kamar ace an ɗaura auren yau, gani yake kamar gobe bazai zo ba,
Ana isa wurin kamu amarya da ango suka fito, already mutane sun taru a wurin, kawaye da abokai sun fito suma sun jeru abayan ango da amarya, su Unty Laila Kuma suna baya, A hankali suka fara takawa zuwa cikin Hall ɗin, Mc yana ganinsu yace "Ango da Amarya sun samu damar isowa Dj kasa musu sauti me ratsa zuciya"
Sauti aka sakar musu na mutanen sudan, Kawaye sunaɗan Rawa da abokai sukuma suna takawa a hankali, saida akayi musu iso akan kujerar da aka tanada musu wanda yasha ado kamar agidan sarauta, Abeeda ce tazo tabayan Amal tace "Unty Amal wallahi za'ace daga Saudiyya aka ɗaukoki"
Amal taɗan Kai mata duka tace "banson tsokana"
Tace "kiga yanda yaya Hafeez ya Ruɗe gaba ɗaya yakasa ɗauke idonshi akanki"
Dariya kawai Amal tayi,
An fara gudanar da Kamu, Abinci aka fara shigowa dashi Mc yace "Jama'a atafawa Abinci"
Tafi aka fara ana dariya,
Biki na tafiya yadda aka tsara, Ankira amarya da ango sun shigo suka rawa cikin nutsuwa Amal dukda Bata iya rawa ba, amma tadanyi kokari,
Abokai da kawaye sun shigo yanzu anfara asalin Kamu, kuɗi ake ɓararwa awurin kamar ba Gobe, su Mama A'isha sun fake agefe sunacin abinci,
Mami ma tazo wurin cikin wani shiga na Alfarma, tana zuwa tazo ta rungume Amal tace "kinyi kyau ƴata"
Amal tace "Nagode Mami"
Hafeez Kallon Mami yayi a shagwaɓe yace "Mami nifa? Banyi kyau bane?"
Tace "kayi kyau mana amma ƴata tafi kyau"
Haɗe rai yayi alamar yayi fishi,
Kiransu akayi a fili sannan Mami tazo tafara liki, kuɗi take ɓararwa bana wasa ba,
Bayan tagama sun koma kowa ya zauna, Mc yace "inada Babban Albishir"
Kowa yayi shiru sannan yace "Ina gayyatan Babban Bakonmu wato Baban Ango"
Tafi wurin ya dauka ganin Abba yana shigowa cikin manyan kaya fari yana dariya,
Hafeez da sauri yatashi yaje ya rungumeshi yace "Daddy you surprised me"
Abba cikin murna yace "Dolene nazo yau yana daga cikin ranar farin cikinka a rayuwa shiyasa na dakatar da duk wani aikina nabi flight nazo"
Yace "Thanks You Abba"
Kiran Amarya da ango aka kumayi a fili, Abba yashiga yafara ɓarin dukiya, Saida Hafeez yafara Hawaye Abba ma ganin haka yasa shima idonshi yafara cika da hawaye, su Abeeda ne suka shigo da Fateema, Mami ma ganin haka yasa ta shigo, kuɗi suka fara likawa junansu, Amal dukar da kai kawai tayi tanajin sani farin ciki yana ziyartar zuciyarta tabbas tayi sa'a a rayuwarta,
Abokan ango da kawayen Amarya sun cashe,
Muneeb dayake ta Neman hanyan Magana da Fareeda shine yafara watsa mata kuɗi a fili, Hafeez yakalli Amal yace "Abokina yayi kamu ranar Kamu na"
Amal murguda mishi Baki tayi tace "Kawata dai tayi kamu ranar Kamu na"
Murmushi suka sakarwa juna,
Bayan an tashi daga Kamu aka maida kowa gidansu Amal, Hafeez yakalleta yace "Ki Hug me Please"
Shiru tayi itama farin cikin datake ciki yasa taji tanaso tasamu wanda zata runguma tayi kuka koda na lokaci guda ne,
Tasan da Mahaifiyarta tana raye da yanzu tana rungume a jikinta,
Buɗe baki yayi yace "Please..."
Kafin yakarasa tawani rungumeshi da karfi, kuka tasaki harda shesheƙa, a hankali yayi mata raɗa a kunne yace "Meyasa kike kuka? So kike nima nayi?"
Girgiza kai tayi, yace "yau yana ɗaya daga cikin ranar farin cikinmu dan Allah kidaina kuka kinji?"
Giɗa kai tayi, yaɗan ɗagota, Share mata hawayen yafara yana cewa "stop crying"
Daina kukan tayi, yace "Sai Gobe ko?"
Tace "eh"
Yace "ki kulamin da kanki"
Kamar zata fita sai kuma takara juyawa ta rungumedhi tace "i love You Yaya Hafeez"
Jikinshi ne yayi matukar mutuwa yarinyar tana bashi tausayi sosai duba da yadda ta taso cikin wahala da rashin mahaifiya, shima rungumarta yayi yace "i love You more Baby na"
Sakinshi tayi tace "Good Night"
Yace "tun yanzu bazamuyi waya bane?"
Tace "Zamuyi"
Yace "Tom sai Anjima Kishiga gida"
Fita tayi lokacin har motocin abokan ango sun watse sai Muneeb daya rage suna hira da Fareeda, har Bayaso su rabu tsabar yanda yakejin dadin hira da ita,
Hafeez ne yakirashi awaya yace "idan kagama saika kunna mota mu wuce"
Yace "banasan hanya ba? To katafi kawai"
Hafeez yace "Dan Allah kawuce mutafi kada kazo ka ɓata"
Fareeda tace "bari nashiga gida sai Gobe"
Yace "zamu haɗu a wurin dinner Kuma idan kin bani dama zamuyi waya Anjima?"
Tace "Tom"
Yace "Anan zaki kwana"
Tace "Eh"
Yace "Good Best Friend Amma kin iya rawa"
Dariya tayi sannan tabuɗe motar tafita"
Suna shiga gida da Amal sukayi Alwala sallah sukayi mangrib da isha, kafin sukaci abinci, a ɗakin Amal suka zauna, da sauran kawayensu waɗanda aka tambayi iyayensu zasu kwana,
Hira aka fara na wurin Kamu Amal daga eh sai A,a sai dariya kawai takeyi,
Maryam Haidar ce tace "Ana magana amarya kinyi shiru me kike tunani ne haka?"
Wata kuma Khadija tace "tana tunanin Gobe War haka tana hannu Hafeez yana fanshe sadakinshi"
Dariya suka kwashe dashi, Amal Banda Amal dataji zuciyarta ta buga,
Fareeda tace "ai kawata dama ga raki ga tsoro kuma budurwa dole taji zafi a first night ɗinta kunga dole tayi tunani"
Dariya suka kara kwashewa dashi,
Maryam tace "Kuma yanda naga Hafeez yana rawan jiki nasan wallahi bazai iya kyaleta ba"
Kirjin Amal har wani bugawa yake tsabar tsinkewar zuciya, da sauri ta mike tafita daga ɗakin, suna tambayarta tace "Toilet zanje"
Dariya sukayi mata sun san ta tsorata,
Buta ta ɗauka tsnufi Toilet, tana shiga ta rufe batasan sanda ta sulale kasa tafar rabza kuka ba, da murya tace "nashiga uku Ni Amal waye zan faɗawa wannan sirrin nawa?"
Toshe bakinta tayi tafara kuka me tsuma zuciya, tasan Hafeez ya yadda da ita, Gobe idan yajita ba Virgin ba Taya zata fara yimishi bayani?
Da karfi tace "Ka cuceni Allah ya isa aduk inda kake Allah ya saukar maka da Bala'i da masifa da tashin hankali fiye da wanda nake ciki a yanzu"
Unty Laila ce tace "Wayake kuka a Toilet ɗin tun ɗazufa nake son shiga"
Amal da sauri ta mike ta goge fuskar ta ruwa ta wanke fuskar dashi kafin tabuɗe kofar Toilet ɗin cikin son gyara muryanta tace "Unty Laila"
Kallonta tayi tace "kece kike kuka a Toilet? So kike ki kama hawan jini? Kekan bazaki raba kanki da kuka ba Amal, auren ne bakyaso? Ko mun ɓata miki Rai?"
A hankali tace "ko ɗaya"
Unty Laila tace "to me yasameki?"
Tace "ina kewar mahaifiyata ne"
Shiru Laila tayi tace "kiyi hakuri kije cikin kawayen ki kisaki jikinki komai zai wuce Allah yaji kanta da Rahama, addu'a take bukata ba kuka ba kinji?"
Giɗa kai tayi tace "Allah miki Albarka jeki"
Fita tayi tanufi ɗaki ranta a dagule,
Tana shiga taga saura sunyi bacci sai Fareeda datake waya da Muneeb,
Itama wayarta taciro daidai lokacin Hafeez yakirata, tana ɗagawa suka fara hira,
Shima Hafeez gidansu yau acike da manyan Baki,
Yana cikin wayar Wata kyakkyawar budurwa tashigo ɗakin, fara sol siririya da farin glass a idonta, Yana ganinta yasaki murmushi yace "Azeezah"
Dariya tayi tace "Halan waya kake da untynmu?"
Yace "Eh"
Karasowa tayi tace bani mu gaisa, amsar wayar tayi tace "Barka dai Untynmu"
Amal tace "Amal dai ba Unty ba"
Dariya tayi tace "Ni karwarsa ce, Mom ɗina da nashi uwa ɗaya uba ɗaya"
Amal tace "yayi kyau inajin sunanki a wajenshi sai gashi ganinki yafi jinki"
Dariya Azeezah tayi tace "thanks You"
Amal tace "nice da Godiya"
Tace "Till we meet tomorrow a wurin Dinner"
Amal tace "Nagode"
Amsar wayar yayi suka cigaba da Hira ita kuma Azeezah takoma wurinsu Abeeda suka fara shirya kayan zuwa Dinner ɗinsu, ankone sukayi na leshi wanda dukka Family da yara da manya sunyishi leshi Blue ne da takalmi golding sai Mayafi Shima Golding, Saida suka shirya komai kafin sukayi Bacci,
Mami da akayi mata lalle jaa da baki, ɗakin Abba taje domin yimishi sannu dazuwa, yace "ashirya abinci na alfarma wanda ba'a taɓa yiba a garin Kano domin abokanshi sunzo kuma suna Hotel duk bikinne ya kawosu, ciki harda waɗanda suka jima basu haɗu ba da masu aiki a kasar waje dana nan Gida Nigeria, a daren Mami takira waya tabada sanarwan ayi snacks da cakes masu yawa, su Alkubus dasu fankaso suma Gobe da safe ayi, harda su sinasir, suma anan gida zasuyi amma yadace ayi dayawa,
Kawayenta duk sun cika ɗakinta matan manyane ƴan kasuwa dakuma ƴan siyasa,
Hajiya Amina matar mataimakin Governor tace "Keko Hajiya Zainab meyasa kika yadda ɗanki yake aure agidan talakawa haka?"
Mami ce tayi murmushi tace "Hajiya Amina kenan to idan masu kuɗi basu auri talakawa ba taya talakawa zasu mori arziki suma? Kuma ai yaro idan yanason abu Gara kayi mishi akan azo ana dana sani"
Shiru Hajiya Amina tayi, daga bisani tace "Hakane amma fa yaran talakawan idan suka samu wuri sunfi yaranmu iyayi"
Mami tace "Banda Amal domin yarinyar akwai nutsuwa da shiga Rai"
Hajiya Amina tace "To Allah ya taimaka"*Asuba Tagari*
_masu son watsapp Group suyimin magana ta wannan number 08144818849_
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.