Chapter 4

243 17 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

   
  *Chapter 4*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim

  

             ~Bayan wasu mintuna Inna tagama had'a komai na abinci, da sallama tashiga d'akin takalli Ammi cikin girmamawa tace "Hajiya an gama abinci"
Ammi murmushi tayi Mata sannan tace "An gode Inna Allah yabiyaki"
Inna cikin girmamawa tace "Tabbas Allah yabiyani tunda ya kawoni gidanku, domin Alkhairin da kukayimin a rayuwa bazan iya saka muku dashi ba, Allah de yakara arziki"
"Ameen" cewar Ammi, fita Inna tayi, Nabil dayake kwance kamar me bacci yace "kawomin abincin Anan zanci"
Inna tace "Toh"
Fita tayi sannan tadawo da wani katon warmer da plate babba a hannunta, ajiyewa tayi akasa takara fita ta d'auko Zobo data had'a daga frij tazo ta ajiye, sannan tace "Aci lafiya"
Ko kallonta beyiba ya sakko daga kan gadon yazauna akasa,
Inna ce tahau sama tasamu Noor akwance tace "nakai Abincin suna jiranki"
A hankali tace "To Inna an gode"
Mikewa tayi ta ajiye wayar tata, sauka tayi tashiga d'akin dasuke da sallama ta zauna a gefen Nabil dayake cin soyayyen Dankali Yana Juya Tea d'in cikin Cup, plate ta d'auka itama tasa Dankalin tafara ci, kallonta yayi Dan ganin Bata d'ibi Tea ba, itama kallonshi tayi, yasan me take nufi indai zasuci abinci tare to jira take yasha Tea ya rage Mata, Bata Shan tea se Wanda yasha yarage, tun Yana had'e fuska har yazo yasaba da hakan, Saida yasha ya rage Mata badan ya isheshi ba, wayarshi ce tayi ringing ya d'aga, murmushi yayi sannan ya amsa ya Kara a kunnenshi tareda cewa "AK Mugun karfe, idan naji Kira daga wurinka samune ko Kuma an sameka"
Ta d'ayan b'angaren yace "Guy wlh yarinyar Nan ta dameni"
Dariya Yakuma yi kafin yace "kaiko saikace baka Saba guga ba ai idan ka goge kaya kaga yaki goguwa to jikawa ake idan yaki har yanzu tofa kayan baze gogu ba, saika tureshi gefe ka d'au wani sabon kayan"
Dariya suka kwashe dashi dukansu kafin yace "dad'ina dakai akwai saurin d'aukan karatu"
Saida suka Kara dariyan kafin ya katse wayar, Noor se hararanshi take ta kasan ido, a ranta tana cewa "idan kaji Yana dariya to banzayen abokan nashine suka kirashi"
Kallonta yayi ganin babu Wanda ya fahimci yaren dayayi yasa yaji sanyi cikin ranshi daganan ya had'e fuska sannan yaci gaba dacin soyayyen Dankalinshi, Yana gamawa yakalli Ammi yace "Ammina Bari nayi kamar zan tafi"
Ammi tasaba da maganarshi baya taba yin magana Me kyau saiya juya, tace "To Allah taimaka"
Tafiya yake da takama da Isa Yana Bouncing, wandon jikinshi guntune da kadan ya wuce gwiwa, sai Armless dayasa dawani siririn sarka a wuyarshi Yana shining sosai sarkan, wurin parking na motoci yaje sannan ya bud'e wata bak'ar mota me kyau, tinted Dan be fiye Hawa mota me nuna mutum ba, sede Wanda zega kowa Amma shi baza'a Ganshi ba, horn yayi da karfi, jikin Baba me gadi yana b'ari yatashi ya bud'e get, fita yayi agidan, wayarshi yabud'e yayi connecting da jikin redio d'in Motar, waka ya kunna daganan yafara bin Bakin mawakin Yana rufe ido Yana enjoying, wayar ce tafara vibrating kallon wayar yayi ganin sunan Mr Guga yasa yayi dariya yad'aga, "Mr Guga"
"Baaba na d'an rage gugannan fa kayan ba squeeze yanzu sosai"
A hankali yace "kodai ka k'ona kayane?"
"Na k'ona da kyar nasamu na gyara"
Nabil yace "Amma Kai shegene Abdul, yaushe zaka shigo Kano?"
"Vary soon Kai Kam akwai de ion ko?"
Nabil yace "baza'a rasa ba saide ka taho da kayan da zaka goge"
Dariya sukayi suka kashe wayar"
Daidai wani lafiyayyen gida me kama da Aljannar Duniya Nabil yayi Horn, Getman ne yaleko ganin motar yasa ya bud'e da sauri yana daga mishi hannu, daidai yayi parking Getman ya iso yafara yimishi kirari, kud'i Nabil yaciro daga aljihunshi batareda ya duba ba, ya watsawa Getman, cikin girmamawa yakara fara gode mishi, Nabil yanason girma sosai hakan ne yasa yake Shiri da Getman din gidan Addanshi, duk Randa yazo sai yayi mishi kyauta,
Shiga ciki yayi, yace "Salam"
Unty Akeela datake zaune tanacin Abinci, tace "wasalam kamar muryan Nabil d'ina"
Nabil yace "Kamar?"
Dariya tayi tace "tsokanarka nake shalelen Ammi"
Zama yayi a kasa gefenta, hannu ya Mika Mata suka gaisa sannan yace "Unty Akeela wurinki nazo"
Tace "to Bari nakawo maka abinsha"
Yace "A,a a koshe nake zauna kawai muyi magana"
Rufe abincin tayi sannan tajuyo tana fuskantarshi hankalinta gaba d'aya ta mayar kanshi sannan tace "Ina jinka Nabil meya faru?"
Matsowa yayi kusa da ita sannan yacire picap d'in dayasa akanshi, Nan gashin kanshi me sheki da yauki ya bayyana, yace "Unty Akeela? Dan Allah ki taimaka kisamin Baki inason Abba ya siyamin private jet Acikin wannan week d'in, wallahj wani abokinane aka siya mishi Kuma Abba yafi Babanshi kud'i Amma gaba daya naga kanshi yafara rawa Kuma kinsan nine jagoran abokanmu so kike a Raina Miki kani?"
Kallon cikin idonshi kawai take ganin yadda yau yasaki baki Yana surutu, Saida ya gama kafin tace "Abba yace kafara aiki kafin yayi maka duk abinda kakeso ki Kuma Nabil kaki yadda, zan ce mishi yasiya maka Amma da sharad'i"
Matsowa yayi yace "sharad'in me?"
Tace "sai idan ka yadda gobe kafara zuwa aiki a company din da Abba yace kaje"
Yatsine fuska yayi sannan ya turo karamin bakinshi cikin shagwab'a yace "Amma kinsan banason datti ko? Kuma wlh banson surutu shiyasa naki karban company d'in"
Kallonshi tayi sannan tace "Nabil? Kasan Kai kanina ne, bazanga kana cutuwa Kuma in kyale ba, Nabil kud'in mahaifi ba kud'inka bane, Abba Yana kokarin ya dauraka akan komai nashi Amma Kai baka gani, Nabil ka dubi wannan guntun wandon jikin naka, ya dace karinka yawo dashi? To a ajiye wannan zancen ma, mijina sirikinka ne, zaka iya had'a ido dashi da wannan armless shirt da gajeran wandon idan yashigo?"
Matsawa yayi daga gefenta sannan yace "Kinga abinda yake hanani zuwa gidanki ko? Dan kawai nace kisamin Baki a magana shikenan saiki faramin wasu wa'azi? Mijin naki ai yasan Ni kaninki ne, ko shine yace nadaina shigo mishi a haka"
Cikin yanayin son Fahimtar dashi tace "ba haka bane, yanzu idan 'yan uwanshi sukazo suka ganka haka ai Mutuncinka ze tab'u, nanfa Kano ne garin musulmai, garin Hausawa da Fulani, garin masu kunya da son Addini, Nan Ba London bane, sannan ba Egypt bane, mijina Kuma be hanaka shigowa haka ba nice naga dacewan hakan"
Yace "to Koda ya hanama bazan hanu ba, sabida gidan yayata ne, idan ma shine to zaki ga yadda zamuyi dashi.."
Kafin yakarasa maganar saiga sallaman mijinta, wani madaidaicine Kuma da ganinshi kasan kud'i ya jikashi, domin jikinshi kadai ze nuna maka hakan, murmushi tayi sannan ta Mike tace "Habiby Barka da dawowa"
Shima murmushin yayi yace "Habibty kema barka da gida"
Kallon Nabil yayi sannan ya bud'e mishi hannu alamar su rungumu, karasawa Nabil yayi sannan ya rungumeshi, yace "Nabil Namijin Duniya yau Kaine agidan namu da yammaci?"
Nabil yace "nine ya gajiya"
Sun gaisa sosai kafin Nabil yace "to nikam zan wuce"
Zuwa yayi wurin Unty Akeela ya rungumeta sosai kafin yace "Bye Bye"
Itama tace "Bye ka gaidasu Ammi da Noor"
Fita yayi dukda ranshi a b'ace Amma be nuna hakan ba, Dan yasan Unty Akeela zatasa Baki, motarshi yakoma, bayan ya zauna yakira number din Abba na Kasar waje, "Abba na"
Abba yace "nayi fishi dakai Nabil tunda kaki kirana"
Nabil cikin shagwab'a yace "sorry Abba"
Abba yace "yagida komai lafiya dai kam?"
Yace "lafiya kalau Abba, dama nakira ne domin nace maka zan fara zuwa aiki Gobe"
Cikin murna Abba yace "gaskiya ka birgeni yau my son, Kuma nabar maka company yazama naka kayi duk yadda kakeso dashi, nasan halinka Nabil, Zakayi Abin arzikine bana tsiyaba, abinda zan zageka dashi shine Dressing d'inka da fatan kafara gyarawa sabida turawa sunce the way you dress the way people will Address you, sabida haka ka gyara dressing d'inka domin nasan Kai mutumin kirki ne, Kuma har yau Ina Addu'a Allah yakara shiryamin 'ya'yana"
Cikin jin dadi yace "nagode Abba"
Kashe wayar yayi cikin jin dadi sannan yanufi hanyar gida.

    *Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

MUTUNCINA!!!Where stories live. Discover now