Chapter 12

235 20 5
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

   
  *Chapter 12*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim


               ~Cikin tausayi sukace "hakane Allah ya kyatata farkonmu da karshenmu"
Yace "Ameen"

        ~kwana biyu tana d'an farin ciki domin Hafeez baya barinta cikin damuwa, yau tana zaune ad'aki Baba yakirata yace Hafeez sunyi magana yace ze kaita makaranta anashi beso hakan ba yafiso abari saj idan ya aureta, Amma mahaifin Hafeez yace Sam Sai tafara zuwa sabida kada ab'ata lokaci, ganin Haka yasa ya yadda yace to ba matsala Allah yashige Mana gaba, "yanzu gobe kishirya Hafeez zai zo sai kuje kuyi register, maganar dazan yi Miki Kamar kullum ne shine ki rike mutuncinki, Kinga wad'annan mutanen sun soki sosai sabida haka kema kiyi kokari kiga kin kama darajanki sannan Suma kibasu tasu darajan"
Sunnar dakai tayi kasa Saida yagama tace "Toh Baba nagode"
"Tashi kije Allah yamiki Albarka sannan Allah yajikan Mahaifiyarki"
A hankali tace "Ameen" cikin zuciyarta ko cewa tayi "sannan Allah ya bayyanamin yayana ya Mukhtar"
Mikewa tayi tawuce d'akinta Zama tayi agefen katifar sannan ta d'au wayar daya Bata tana dannawa batareda tasan Ina take Shiga ba, tarasa wace irin kwakwalwa ce da ita Sam Bata gane abu dawuri,

Da dare Hafeez yakirata Yakuma shaida Mata cewar zasu je register gobe a ka'ab bin maleek school, makaranta ne me had'e da islamiya, murna tayi sosai sannan tayi mishi godiya, cewa yayi "ki daina godemin nine da godiya da Allah ya had'ani da mace kyakkyawa Kuma me kamun Kai Kamar me"
Shiru tayi batace komai ba, Hira yad'an jata dashi daganan tabud'e Baki tafara zuba mishi surutu, shiru kawai yayi ya lumshe idanu Yana sauraran zazzak'ar muryanta,
Be dawo hayyacinshi ba Saida yaji Tace "kaifa"
Da sauri yace "Ni me?"
Turo Baki tayi aranta Tace be jini bane ko me?
Yakara cewa "nifa me? Baby Amal?"
Tace "kaima kanaso?"
Yace "me nakeso?"
Dad's cuno Baki tayi wato duk surutun datakema baya jinta?
Yace "Sorry Princess nad'an shagalane da tunaninki, me kike tambaya ta?"
Tace "cewa nayi kaima kanason karatun littafi?"
Murmushi yayi sannan yace "nikuma namiji meya had'ani da karatun littafi? Wannan ai saiku Mata, gara da ma Naga wani a hannun Abida sunanshi AMANNA na karanta har karshe sabida kishin Mata, yayi dad'i sosai, daga kanshi ban kara karanta littafi ba"
Cikin sakin fuska tace "nima ai na karanta AMANNA na Jamila Umar Tanko"
Yace "Ina nasani"
Hira sukayi sosai Saida tafara jin bacci kafin yace "good night have a nice dream of me"
Murmushi tayi dukda Bata ji meyace ba Amma ta fahimci inda zancen ya dosa"
Katse wayar yayi, Nan tayi Addu'a tafara bacci,
Shima Addu'an yayi sannan yafara bacci da niyyan gobe da safe ze jeshi gidansu yaje yayi Mata register.

_Washe gari_

Hafeez ne yazo da sassafe yashiga har d'akin Baba yaje suka gaisa sosai, kafin yafito ya hango Mama a tsakar gida tana gyara shinkafa, durkusawa yayi har kasa yace "Ina kwana Mama?"
Bata kalleshi ba Tace "mun tashi lafiya?"
Mikewa tayi zata bar wurin, yace "lafiya kalau" hannu yasa a Aljihu yaciro wasu kud'ad'e d'ari biyar biyar ne sabbi ya ajiye Mata yace "Ayi hakuri"
Ganin kud'i yasa taji Kamar ta zauna, kujeran data tashi akai ta Mika mishi Tace "ga wuri ka durkusa akan kafarka? Ka zauna Dan Allah, yasu Alhaji dasu Hajiya?"
Yace "lafiyansu kalau"
Cikin sakin fuska tace"agaidamin su" da karfi tace "ke Amal me kike har yanzu acikin d'aki? Ko bakisan anata jiranki bane?"
Amal ce ta fito da d'an gudunta hannunta rikeda Hijabi ga wayarta a hannunta ba shiri dama tafito, zuba Mata idanunshi yayi tana kallon yanda tayi kyau cikin dressing d'in, bawani Kaya me tsada bane Amma ya karb'i jikinta sosai, domin rigan bakine da adon duwatsu ajikin saita d'aura kanta da Bakin d'ankwali powder tashafa da lip balm Wanda yasa bakinta shek'i dakuma fuskarta yakara Haske,
Tana ganinshi ta sakar mishi murmushi Shima mayar Mata yayi tareda d'auke kanshi, mikewa yayi yacewa mama "sai anjima"
Cikin jin dad'i da murna taga kud'i tafara tura Amal Tace "kibishi Mana kk sai kin b'ata mishi lokaci?"
Amal hanyan fita ta nufa Baba yace "Hijabinta?"
Kallon Hijabin tayi sannan tasa Tace "natafi"
Yace "adawo lafiya ki kula da kanki ki kama Mutuncin ki"
Tace "insha Allah"
Da sauri taje wurinshi tabud'e motar Shiga tayi tana murmushi Tace "Ina kwana ya Hafeez?"
Kwantar da Kai yayi ajikin seat sannan yazuba Mata wannan idon nashi dabata iya jure kallon cikinsu, wasa tafara da yatsan hannunta, yakalleta sosai Yana kallon yanda take wasa da hannun nata, a hankali takuma cewa "Ina kwana?"
Still beyi magana ba Kuma be daina kallonta ba, Baki ta d'an turo Tace "ka daina kallona"
Sai a sannan yace "idan ban kalleki ba wa kikeson na kalla?"
Tayi shiru, kunna motar yayi yad'au hanya, Saida sukayi nisa kafin yace "kin tashi lafiya?"
Tace "lafiya kalau"
Shiru motar yayi, ganin anyi shiru yasa yakunna yayi connecting wayarshi da redio d'in cikin motar ya kunna wakar Umar m Sharif Wanda yake cewa "nagama zab'ina, kuyi murna dangina, daso samuna, yanzu mu karkare dake, inyo aure nakosa, inba keba nafasa, Ni katako ke kusa, sonki a Raina kin cusa, kyakkyawa ce na dace ta sace zuciyata..."
Bin wakar yake Kamar shine ya rera, kallonshi take tana dariya dan ba karamin birgeta yayi ba,
Ganin tana kallonshi yasa Hafeez rage volume sannan ya kashe Mata ido yace, lafiya 'yammata? Naga kinata kallona,
Kawar da Kai tayi batace komai ba, hannu yasa a kwantaccen suman kanshi Wanda yasha gyara sosai sannan yace "gashina kike kallo Dan yafi naki tsawo ko? Ko dai Sajen fuskata kike kallo sabida yanda yakeda kyau?"
Batayi mishi magana ba har yanzu sai murmushi datake, yace "naganoki cewa kike da in rasa wannan kyakkyawa saurayin gara nafad'a a rijiya"
Juyowa tayi tafara dariya sosai hadda toshe Baki, kallonta yake domin be tab'a ganin wacce dariya yake karawa kyau sosai kamarta ba, musamman da gefen kumatunta suke lotsewa ga fararen hakoranta dasuka bayyana, sai kananan lips d'inta dasuke shining, ga dogayen yatsunta farare kat kat datake sa hannu tana rufe Baki dashi, Saida tayi dariya me isarta kafin Tace "Kai d'innan bak'i d'inne har zan fad'a a rijiya?"
Cikin wasa tayi maganar, Shima da wasa yace "Ai Baki Saida fara, Fari Kuma Saida bak'a"
Dariya sukayi duka, abakin makarantar ya tsaya yayi parking, fita yayi ya bud'e Mata tafito fuska a sake sabida dad'in zataje school, da Getman na school d'in suka gaisa kafin suka shiga ciki, office na headmaster sukaje bayan sun gaisa yayi mishi bayanin cewar register sukazo yi, Saida akayi Mata passport sannan ya cike Mata form, Nan aka Bata Jss 3, bayan an kammala komai headmaster yace akaita class, tareda Hafeez akaje aka nuna Mata class d'inta, ganin mutane dayawa a class d'in yasa tafarjin jikinta yayi sanyi, batason cikin mutane ko kad'an, Fahimtar Haka da Hafeez yayi yasa ya matso kusa da ita yariko hannunta, d'ago Kai tayi ta kalleshi yace "kada kiji tsoro kisa a ranki ke kad'ace a cikin class d'in"
Shiga da ita yayi sannan ya ajiyeta a benci kusada wata yarinya wacce yaga kamar bazata fiye surutu ba, gaida malamin class d'in yayi kafin yajuya yatafi, be jimaba yadawo yakirata, fitowa tayi yaciro kud'i yabata sannan yace "nikam Ana nemana a Asibiti gashi zanzo na d'aukeki idan kun tashi"
A hankali tace "nagode"
Saida yajuya ze tafi tace "Ya Hafeez?"
Juyowa yayi ya d'aga Mata gira, Tace "Zan bika" idanunta fal da Hawaye tayi maganar, "Kai Amal saikace yarinya?"
Matsowa wurinta yayi sannan yariko hannunta Yana murzawa yace "kalleni Nan"
Kallonshi tayi, yace "Haka kikeso kizama me ilimi?"
Tayi shiru, yace "idan bakiyi karatu ba bazakisan me Duniya take ciki ba, karatu Yana taimakawa rayuwar mutum, musamman idan 'ya mace tayi karatu, ki kwantar da hankalinki Suma 'yan ajin naku dahaka suka Saba kinji?"
Gid'a Kai tayi yace "yawwa Baby Amal, yimin murmushi"
Dariya tayi kad'an yace "Good girl to tafi class"
Komawa class d'in tayi ta zauna, ranta fess.

    *Wattpad*
Jiddah S Mapi

MUTUNCINA!!!Where stories live. Discover now