Chapter 22

178 11 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸

      Na
Jiddah S Mapi

*Chapter 22*

     *____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

      

               ~Me ta bambayeki? Cikin tsoro tace "babu" yasani idan kaga Amrish tayi kuka dan an tambayeta baya rasa nasaba da tambayar suwaye iyayenta, Gara yayiwa tufkar hanci, nuna Amal yayi da yatsarshi ta biyu cikin zare idanu da masifa yace "idan kika kara yimata wannan tambayar saina kakkaryaki"
Giɗa kai tayi, ta shige ɗaki cikin rashin gaskiya dan tasan rashi ya ɓaci sosai, samun wuri tayi agefen Inna ta zauna, Inna Tace "ba'a yiwa Amrish da yayanta wannan tambayar sabida shine tambayar da a rayuwarsu suka tsaneta, idan kinaso kici gaba da zama a gidannan kada ki kara kwatankwacin wannan tambayar, idan kika kara koni zan iya sallamanki daga gidannan"
Shiru Amal tayi hakika abinda Inna take faɗa gaskiyane domin gashi ya nuna a fuskarta, da yaddan Allah bazata kuma yin wannan tambayar ba, Amrish ce tashigo tace "muje gidansu Kawata danake baki labari Safiya"
Amal cikin mutuwar jiki tace "A,a Amrish yau inajin cikina yanata motsi sosai kije yau, gobe zamuje" mikar da kafafun da sukeyi mata nauyi tayi yau jin cikin take yana juyawa sosai, hannu tasa tana shafa cikin nata, kaima kanaso ka wahalar dani kamar yadda mutanen duniya suka wahalar dani ko?" Abinda take faɗa kenan a zuciyarta batareda tabari yafito fili ba.

              "Daddy Yaufa Zan dawo urgent meeting ne shiyasa ban sanar dakai ba" shiru yayi yana sauraran daddy dayake yimishi faɗa akan tafiya batareda ya sanar agida ba, sorry Dad bazan Kuma ba, Saida ya lallaɓashi kafin yasamu Daddy ya sakko, dafe kanshi yayi tareda sauke nannauyan numfashi, bayason hayaniya a rayuwarshi ko kaɗan, kwanciya yayi a ringingine kan maƙeƙen bed ɗin dayake shimfiɗe a ɗakin Hotel ɗin, pillow ya ɗauka ya ɗaura kanshi akai sannan yafara latsa wayarshi, contact yashiga sannan ya latsa sunan da akayi saving da Zuby a handsfree yasa wayar sannan bugu ɗaya akayi answer "Barka da warhaka Baby Beel"
Bai amsata ba "kizo ina Marhaba Hotel VIP Room 6"
Katsewa yayi bai jira amsarta ba domin yasan dole zatazo, yasan yadda Zuby Take mutuwar sonshi ko a ina take idan ya kirata zata amsa,
Baifi 50mins ba yaji ana Knocking tashi yayi yafara tafiya, baisa komai ba jikinshi sai wani ɗan karamin Boxer purple, sanin cewa itace yasa ya buɗe tareda juyawa baya zai koma, da sauri ta riko hannunshi, sannan ta rufe kofar, wata budurwa ce da bazata wuce 25year ba, tanada kyau na fuska amma ba sosai na sosai ba, tanada shape sosai domin wandon jikinta yayi matukar kamata hakan ya nuna shape ɗinta, kanta tayi Kitson Attach Wanda ta cika dashi, nails Kuma tasa a yatsunta pink wato kalan wandon jikin nata, rungumeshi tayi ta baya tana shafa kirjinshi me ɗauke da kwantaccen gashi, da sauri ya cire hannunta sannan ya jawota izuwa kan Bed ɗin, rigan jikinta me igiya yafara kuncewa yana kissing ɗinta tareda shafa jikinta da ɗayan hannunshi, saida ya kwance kafin yayi ƙasa da rigan, babu abinda take sai lumshe idanu, tabbas tayi missing ɗin Beel domin ba koda yaushe yake bari ta kusantoshi ba, bakinta takai kan nashi tana kokarin kissing ɗinshi da sauri ya ɗauke kai, cikin ɓacin rai tace "kana kyamata ne Beel?"
"Yeah domin bansan maza nawane sukayi ba I can't do that"
Shiru tayi domin inda sabo tasaba da halinshi, saida yagama shafa jikinta yagama romancing ɗinta sannan ya saketa yatashi zai shiga Toilet, rike hannunshi tayi idanunta har sun canja kala, hawayene suka fara ɓin kumatunta tace "Beel meyasa baka yadda Dani ba? Baka taɓa yadda kashigeni saide kayi romancing ɗina shin kana zargina da wani abu ne?"
Fizge hannunshi yayi cikin ko in kula yafara magana "Zuby kinsan niba mazinaci bane,
I have alot of feelings shiyasa na kiraki Dan naɗan samu relief, and you know what? Kada kitaɓa sawa a ranki zan iyayin abinda yawuce wannan dake, shigewa Toilet yayi, saida yayi wanka sosai kafin yafito da towel ɗaure a waist ɗinshi, Zuby datake kwance idanunta yana kallon pop na ɗakin da sauri ta maida idanunta zuwa kanshi, kallon yanayin jikinshi take hakika wannan gayen ya tara duk wani abu da kowace ƴa mace takeda buƙata a wurin namiji, musamman kirjinshi dayake ɗauke da gashi a kwance lup lup, ko ta halin ƙaƙa sai ta aureshi idan bata aureshi ba dole sai yayi abinda take requesting a wurinshi, the guy is so damn Sexy, Yana lura da ita amma ko kulata bai kara ba har yashirya cikin riga da wando na Shadda, agogo yake ɗaurawa a hannunshi yace "You can Go dan nima yanzu zan wuce Abuja mun gama Meeting tin ɗazu"
Tashi tayi a hankali tafara takawa har zuwa gabanshi rungumeshi tayi niyan yi, da sauri yayi baya "don't squeeze my Dress"
"No kawai kace You hate me, kaifa kayi inviting ɗina Kuma kana nema ka wulaƙantani?"
Taɓe baki yayi sannan yace "You can Go"
Da fishi ta fizgo jakarta daga kan Bed ɗin sannan tasa takalminta me tsini, fita tayi daga ɗakin tareda banko mishi kofar ji kake gummm, kamar kofar zai ɓalle,
Tsaki yaja dan shi yatsani fitsara da raini, saida ya harhaɗa komai kafin yaje yayi submitting na key ɗin yabar cikin Hotel ɗin, Black space ɗinshi yasa hakan yakara bayyana kyawun dayake fuskarshi, Private Jet ɗinshi yahau suka wuce Abuja.

   
           "Cikin jikin Amal sai girma yake babu laifi tana samun kulawa a wurin Inna, duk wani abinda ya kasance uwa tayuwa ƴarta to Inna tana iya bakin kokarinta dan ganin tayiwa Amal, Amrish ma yanzu Amal tafara koya mata wayo, dukda itama Amal ɗin bawani wayone da itaba amma hakan bai hanata koyawa Amrish ɗin wasu dabarun rayuwa ba, yanzu Sadauki yaɗan rage haɗe mata fuska ba laifi yana amsa gaisuwarta da kyau kaɗan yanzu,
Yau ta tashi da kwaɗayin Mangoro tun safe take zaune a karkashin bishiyan daya saba zama, ta buga tagumi domin Amrish ta tafi tallan Nono gashi duk yaran unguwa yau basu wuce ta ba, sai turo baki take tana haɗe fuska, Kamar kullum ya dawo daga daji hannunshi rikeda kibiya dakuma kori da baka, kallonshi take yadda yake tafiya cikin nutsuwa da kasaita, saida yazo kamar zai wuceta sai kuma ya dawo baya, kallonta yayi ya watsar kafin yace "lafiyanki?"
"Wallahi yau sha'awar Mangoro nake gashi Amrish ɗita ta tafi saida Nono"
"Ba nono ake cewa ba Fura"
Shine amsan daya bata, kunya taji sosai, a ranshi yaji dadin yadda takeson Amrish ɗin gashi yanda take magana a shagwaɓe yasa yake sauraranta idan zatayi magana, ɗakinshi yashige wanda yake bakin soron gidan domin kana shiga gidan ɗakinshi zaka fara gani, ajiye Duk kayan yayi sannan ya zauna akan gadon ƙasan dayake shimfiɗe acikin ɗakin nashi, ɗakin tsaf tsaf babu datti dukda ɗakin kasane amma kana ganin kayanshi kasan suna samun kulawa, saida yaci shinkafa da waken da Inna Ta ajiye mishi kafin yafito yayi alwala, yana kallon yadda ta rabza tagumi kamar zatayi kuka, salla yayi sannan yayi addu'a sosai kafin yafito yaja kofar, takalminshi silifas yasa yafara tafiya kamar tace mishi yaje ya tsinko mata amma tana tsoro har kanshi ya ɓace, baifi minti 20 ba yadawo hannunshi rikeda bakar leda, batasa a ranta ledan nata bane taga ya ajiye mata a gabanta, buɗewa tayi da mamaki taga manyan manyan Mangoro nunannu, wani irin Murmushi ta sakar mishi wanda ya bayyana fararen kyawawan jerarrun hakoranta, gefen kumatunta saida ya lotsa tace "Thanks You Hamma Sadauki"
"Is pleasure"
Shine abinda taji yafito daga bakinshi, tafiya yayi yabarta baki buɗe, aina wannan mutumin dayake wuni a daji yasan turanci? Sai yanzu take tunawa yana yawan sa turanci a maganarshi, amma bai taɓa bata mamaki irin na yau ba, to shi wannan wanene?.

_wannan littafin na kuɗine ku biya 300 ta nan 6037523268 Hauwa shuaibumapi Keystone Bank, ku turo katin shaidan Biya tanan 08144818849 masu kati kuma zaku iya tura 300 tanan 08144818849_

   *Wattpad*
Jiddasmapi

MUTUNCINA!!!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant