🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 14**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*~Ranar Jumma'a da Dare bayan sallan Isha, Abbu da Abokansa dakuma Yayyunsa suka had'u agida, motoci na Alfarma suka Shiga dukkansu sanye da manyan Kaya, Kai da ganinsu kasan sun jiku da Naira, Kuma da ganinsu kasan sunyi nisa da Talauci, Gidansu Amal suka nufa domin kai kuɗin Aurenta, tun a hanya wani Abokin Abbu yace "kai kuma da kuɗinka da ɗaukakarka miye ya kawo ɗanka neman aure a wannan dirty area?"
Abbu yace "Toh Yarone ka haifeshi amma baka haifi halinshi ba, shi Hafeez idan yanason abu dolene ayi mishi saboda shi kaɗai ne namiji wanda Allah yabani, fatana dagashi har matar da zai aura su tayani tsare Mutuncina dakuma nasu"
Shiru abokin nashi yayi domin yasan gaskiya yafaɗa duba da yadda aka rinƙa yiwa Hafeez ɗin tallan ƴammata daga manyan gidaje waɗanda iyayensu suke rike da makamai na gomnati,
Sun tsaya a kofar gidansu Amal suka fito dukkansu tareda yin sallama,
Baba dayake zaune a cikin gida yana jin redio ya amsa sallaman tareda mikewa,
Fita yayi yaga Alhaji Yusuf tareda wasu manyan mutane, Da sauri yace "Alhaji meyasa kazo da kanka, ai da aikawa kayi inzo da zanzo basai kunyi gajiyar Zuwa ba"
Alhaji Yusuf cikin Murmushi yace "Mu muke neman Abu a wurinka mune yadace muzo, idan muka kiraka kuma ai raini yashiga"
Baba yace "mushiga daga ciki"
Shiga sukayi da sallama a bakinsu, Mama A'isha ganin manyan mutane acikin gidan yasa ta ɗauko tabarma tana gaishesu cikin fara'a da washe haƙora, Zama sukayi aka gaggaisa cikin mutunci da girmamawa,
Yayan Abbu ne yace "Toh Mu kam ba komai bane ya kawomu sai maganan sa ranar bikin danmu Hafeez da kuma ƴarka Amal, sai Kuma kuɗin aure da muka kawo"
Hannu yasa cikin Aljihu ya ciro wasu kudade masu yawa ya ajiye agaban Baba,
Yace "Gashi nan Dubu ɗari biyar ne"Zaro ido Baba yayi yace "Dubu ɗari biyar?"
Abbu yace "Eh ayi hakuri""Gaskiya Dubu ɗari biyar yayi yawa ina laifin dubu talatin?"
Abbu yace "A,a Amal tawuce haka a wurinmu, yanzu munaso asa mana Date wato ranar Bikin"
Baba yace "idan nan da wata ɗaya yayi muku Toh"
Cikin jin Dadi Abbu yace "mun gode Allah yasaka da Alkhairi""Ameen"
Duk sukace sannan suka tashi,
Mama ce tace "Angode Alhaji"
"Ba komai mune da godiya" cewar Abbu.Bayan Tafiyarsu Abbu yakira Amal wacce ta laɓe a ɗaki tana sauraronsu,
Cikin sunkuyar da kai tazo tace "Gani Baba"
Kallonta yayi idonshi cike da hawaye yace "Amal Kinga inda Allah ya kaiki? Nayi fatan da Mahaifiyar ki tana raye, Amal ki godewa Allah sannan ki rike mutuncinki, kinsan Alhaji Yusuf babu abinda yatsana kamar a zubar mishi da mutunci ko?"
Giɗa kai tayi cikin hawaye, "yace nasan halinki kuma ina alfahari dake, nasa Aurenku nanda Wata ɗaya kenan saura Jumma'a Uku ana huɗu zaki zama matar Aure, ina fatan ki kasance mace ta gari awurin mijinki"
Kuka take na fili dana zuciya, Baba ma yana shirin kukan yace "Tashi kije"
Tashi tayi takoma ɗaki, faɗawa tayi akan katifar ɗakin har Saida taji ciwo a jikinta, sabida katifar gyarawa tayi, kuka tafashe dashi me tsuma zuciya gaba ɗaya jitayi ta tsani kanta, cikin muryan kuka tace "Ban dace da wannan sadakin ba, Wallahi ban dace dakai ba Hafeez"
Har kanta yafara ciwo tsabar shesheƙar kukan datake, mikewa tayi idonta duk ya kumbura fuskarta tayi jajir, musamman karan hancinta wanda yakara tsayi tsabar janshi datake idan tana kukan, zama tayi agefe tana goge idonta da hijabin dayake jikinta, dafe kanta tayi da hannunta dan ji take kamar ze faɗo kasa, wayarta ce tafara Ruri, a hankali ta ɗago kai tana kallon sunan dayake yawo a fuskar wayar, ganin My Love Yana yawo kiri-kiri a fuskar wayar yasa tasa hannu ta ɗauko, jitayi kamar kada ta ɗauka sai wata zuciyar tace ki ɗauka kawai,
Ɗagawa tayi cikin sanyin murya da alamun ta gaji da kuka tace "Hello"
Hafeez dayake zaune a ɗakinshi wanda jin labarin ankai kuɗin Aurenshi tareda sa rana yasa yakasa zama wuri ɗaya, cikin muryan jin Daɗi da nuna yana cikin murna yace "Baby Ina cikin Murna da jin Dadi saura one month aurenmu?"
Amal da kuka yakara kwace mata da sauri tasa hannu ta toshe bakinta tana kokarin ɓoye mishi,
A hankali yace "Baby meya faru?
Kuka kike?"
Batayi magana ba kuma bata daina kuka ba.
Rikicewa yayi yafara tambayanta "Baby Amal? Bakya sona ne?
Idan bakya sona ki faɗamin Please, me akayi miki..?"
Da sauri tace "ina sonka"
Sauke ajiyan Zuciya yayi sannan yace
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.