Chapter 5

236 20 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

   
  *Chapter 5*

            ~Amal Saida tayi kwana biyu kafin tasamu saukin jikinta, saide tafison rad'ad'in da kasanta yake mata akan na zuciyarta, domin zuciyarta kamar zata fashe haka takeji, kullum da dare saita tashi tayi sallah, rokan Allah take dayabi Mata hakkinta duk Wanda ya tab'a Mutuncinta to Allah ya saka Mata,
Yau da safe ganin Mama tayi tana tace Awara, shiru tayi Dan tasan yau dolene tafita tallan Awara ko taki ko taso, Mama ce ta kwala Mata Kira, da sauri tafito daga d'aki taje ta durkusa tace "gani Mama"
Kallon sama da kasa tayi Mata kafin tace "Ni kikeso na soya awwran? Sannan Ina 'Dan kwalalinki? Kodan Kinga kinada gashine yasa kika fito ba d'ankwali ko yadda kikayi kika ja ra'ayin yayanki haka kikeso kiyj domin kija na Ubanki?"
Cikin kid'ima ta d'ago manyan idanunta ta kalli mama, ranta ya b'aci sosai, ganin maganan yayi ciwo sosai sannan wannan maganar Bata dace ba yasa tace "Koda zanyi wani abinda be daceba kisani bazanyi da mahaifina ba Kuma bazanyi da yayana ba"
Buge Mata Baki tayi tace "Ina magana kina magana Amal? Sa'arkice Ni? Ni kike mayarwa zance" yau zanci Ubanki Amal, muciya taje ta d'auko Amal kuwa ganin zatayj Mata Rauni yasa ta Mike da gudu tafita waje, ta firgita sosai Dan tasan Mama zata iya ji Mata ciwo, Zama tayi a kofar gida tana rarraba ido gaba d'aya jikinta Yana rawa, Mama ce ta leko tace "saide ki kwana a waje, kuma yau zaki fita talle Dan bazaki sani asara ba, kije duk inda zakije acikin garin Kano zaki dawo ki sameni ne"
Kuka tafara tana rokanta gafara Amma ko sauraronta batayi ba tashige gida,
Saida Tasha kuka me isanta duk masu wucewa sai sun tambayeta "lafiya" shiru kawai takeyi musu,
Wata yarinya ce tazo wucewa sa'ar Amal ce, ganin Amal haka yasa ta karaso wurinta tace "lafiya Amal?"
Kallonta Amal tayi tace "lafiya lau Dije"
Tace "A,a ba lafiya ba, ganinki haka ya d'agamin hankali Amma Ina tsoron zuwa wurinki sabida mamana tace kada nakara tafiya dake, Dan Allah Amal ki gafarceni bazan iya taimaka Miki ba wallahi Ina tsoron fishin mamana, zan Baki shawara da ki tashi ki koma cikin gida Koda kasheki zatayi, domin zamanki a waje haka ze iya tab'a Mutuncinki"
Kallon Dije tayi idonta acike fal da hawaye tace "Mutunci Kuma na nawa Dije? Taimakon da kikamin a bayama na gode, ki tashi anan kada afadawa mama an ganki Dani"
Tashi Dije tayi tana kuka domin Amal tana Bata tausayi, ganin bazata iya tafiya ta barta ba yasa yaciro d'ankwalin kanta tinda tanada hijabi, matsowa wurin Amal tayi sannan ta d'aura Mata d'ankwalin taciro naira Hamsin ta ajiye Mata akan cinyarta, bazata iya magana ba sabida kuka, hakan yasa ta juya tana kuka tabar wurin,
Amal d'aukan Hamsin d'in tayi tarike a hannunta sannan tayi sallama tashiga gida, tasan gaskiya Dije tafad'a zamanta a waje ze iya zubar Mata da Mutunci, saide Ina mutuncin ma? "Allah ya isa bazan tab'a yafe maka ba"
Shine abinda ta furta a fili,
"Ni kike cewa Allah ya isa Amal?"
Amal tace "a,a ba dake nakeba"
Gaba d'aya matar Baban nata tafice Mata a rai, ta sanadiyyar ta ne akayi Mata fyade, wallahi ta tsaneta kawai batada wurin zuwane yasa ta zauna, Kuma domin ta kare mutuncinta, Zama tayi tafara soya awaran saida tagama kafin taje ta shirya tasa wani hijabinta Wanda dagani kasan hijabin ya gaji, tana gamawa tad'au robar awaran ta d'ora akanta, "kada kidawo gidannan da ko guda d'aya na dubu dayane"
Fita kawai tayi tanufi hanyan kasuwa, abakin kasuwa suke Zama suna siyar da Abinda sukazo dashi, ganin abokan sana'arta sun fito yasa tasaki fuska tana murmushi tace "Kande, Fati, Duk kun fito?" Ba yabo ba fallasa
Sukace "eh"
Kowace ta d'auke kanta, inda sabo tasaba da hakan, sukuma haushi sukeji Dan tafisu kyau, wasu nasiyan abinta sabida kyaunta,
Wanine yazo wurin yayi parking na wata dank'areriyar mota baka, bud'ewa yayi yafito, babban mutum ne ga tunbi ga tsayi gashi Kuma Baki Kirin, saide da ganinshi kasan yana harka da daloli, wurinda Amal take zaune yaje yaciro wasu rapan dubu d'aya yamika Mata tareda cewa "inason Awara malama Amal"
Kawar da kanta tayi gefe, ta had'e fuska Kamar Bata tab'a dariya ba a Duniya,
Yace "Malama Amal magana fa nake Miki"
Shiru tayi mishi da akwai hali data yiwa wannan mutumin Rashin Mutunci Dan wallahi ya takurawa rayuwarta, matsowa yayi wurinta da sauri ta matsa, Kande ce ta washe hakora tace "sannu dai Alhaji anfito?"
Kallon kande yayi yace "sannu Kande ga Alalan yayi kyau, kawomin na dubu d'aya a mota Ina jiranki"
Komawa yayi cikin mota, Nan Kande ta d'auko roba ta zuba alale cikin rawan jiki takai mishi, bud'e Mata motar yayi tashiga, Saida tayi kusan Rabin awa a motar kafin tafito tana gyara hijabi, hannunta rikeda wasu sabbin dubu d'aid'ai tana washe hakora tana wani palli da d'agun Kai, tana zuwa ta rabarwa yara alalenta tabawa Fati dubu biyar aciki sannan ta kulle sauran a Bakin zaninta, tace "Fati nikam natafi gida"
Fati tace "kekam kawata yau kinyi sa'a, kullum ma da sa'a kike fita"
Cikin iyayi tace "saikin karaso"
Tafiya tayi, Amal ganin ta tafi yasa ta matso wurin Fati tace "Fati nikam inason muyi magana idan ranki baze b'aci ba"
Fati tace "inajinki"
Amal tace "kada ki biyewa Kande da irin wannan rayuwar wallahi hallaka kanki zakiyi, Ina fad'a Miki hakanne sabida naga ke bakiyi nisa ba, Kuma Ina sonkine shiyasa nafada Miki kiji tsoron Allah a duk inda kike"
Fati tayi salati tace "Yanzu Kande d'ince 'yar iska? Ai wallahi gobe saina fad'a Mata"
Ganin Bazata fahimci zancen ba yasa tayi shiru da bakinta,
Saida kusan mangrib kafin tasaida awarar, gida ta tafi tabaiwa Mama , mama ganin an kawo kudin cif yasa ta washe hakora tace "yawwa da kina haka ai da mun shirya, jekiyi wanka kizo musha Hira"
Wanka taje tayi lokacin data fito Baba ya dawo, tace "sannu Baba"
Yace "yawwa Mamana ya gida?"
"Lafiya kalau" shine abinda tace kafin tashige d'aki ta kwanta, Nan tafara aikin da kullum sai tayi wato "Kuka"

   *Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

MUTUNCINA!!!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang