🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸_Book one Free_
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 18**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________**Book One Free*
~Safiyar Jumma'a, Fareeda wannan Kitson "ai yayi miki kanana, taya zaki tsefe?"
Amal ce tayi tambaya tana kallon Kitson Fareeda wanda akayishi kanana sosai,
"Banda ke Amal gashin ma ina yake? Ai kune tsifa zaiyiwa wahala amma mukam ai ko yanzu zamu iya tsefewa mukara kitsa wani"
Murmushi kawai Amal tayi, Sajaan Unty Laila tazo dashi, tace "Kawo hannunki na shafa miki dama ban shafaba sabida kada ya goge"
Mika zara zaran hannayenta farare sol masu ɗauke da zanen fulawa tayi, "Unty Laila hakan mafa yayi kyau basai ankara ado ba, kada kwalliyan yayi yawa"
"Lalle Amal yaufa kowani ado za'ayi miki ya dace dake domin yana cikin Ranar farin cikinki na duniya yau zaki fita a sawun Ƴammata Kishiga na Matan aure" tafaɗa lokacin datake shafa mata sajaan ɗin a ƴan yatsunta,
Cikin gidan yacika da jama'a wasu na girki wasu na yanka kayan miya, Mama Aisha da ƴan uwanta suna zaune agefe sun kafa cafta sai hira suke dasunga abin Gulma saisu kwashe da dariya harda Tafawa, babu me kulasu domin ansan Halinsu,"Tunda angama idan ya bushe saikije kiyi wanka kinga mutane sun taru kada kuma azo aga amarya da datti"
Cewar Unty Suwaiba wacce hannunta yake rike da cokalin stew,
Amal tace "Tom"
Amal wanka tayi tasa wani farin leshi batayi kwalliya ba hoda kawai tashafa sai white lipstick, kyaunta na asalin Bafulatana da kuma Buzuwa yakara fitowa sosai, kowa ya kalleta saiya kara juyawa ya ganta,
Wayartace tafara ruri tana dubawa taga Hafeez ne, Gefe takoma ta zauna akan kujera kafin ta latsa Kore,
"Amarya ta"
Shiru kawai tayi dan gaba ɗaya taji kunya, "Ji nake kamar anyimin Albishir da gidan Aljanna yau wai Amal ce zata zama Matata? Allah na godema"
"Nima na godewa Allah dayasa yau zaka zama mijina yaya Hafeez ka rikeni Amana dan Allah"
Cikin sanyin murya yayi magana "Baby idan ban rikeki Amana ba wa zan rike?"
Shiru tayi hawaye yanabin kuncinta,
"Wallahi ina sonki Amal nima ki rikeni da Amana kinji"
"Toh ya Hafeez"
Yace "sai bayan an ɗaura aure zan kiraki sabida mutane sunyi yawa gakuma hayaniya"
Tace "Toh i love You yaya Hafeez"
Cikin tsokana yace "banji ba maimaita"
Dariya tayi da ƴar siririyar muryarta "ilove You"
Lumshe ido yayi yace "your voice is sweet, I love it and I love you my princess"
Katse wayar zaiyi.. "ya Hafeez"
"Yes princess""Ina sonka"
"Nima Ina sonki sosai, bazan iya rayuwa babu ke ba, wallahi idan na rasaki zan shiga tashin hankali da mawuyacin rayuwa dan Allah kada ki gujeni a kowani hali"
Hawayen soyayyarshi taji yana sauka mata daga idanu, "Tabbas yaya Hafeez Kaine kafara nunamin soyayya a rayuwata natashi cikin wahalar rayuwa ban taɓa sanin menene soyayya ba, sannan ban taɓa ɗanɗana zumar soyayya akan harshena ba, kaine wanda kafara ɗanɗanamin, babu wanda yataɓa cewa Amal Ina sonki yaya Hafeez kaine farkon wanda yafara furtamin wannan kalmar bazan taɓa mantawa dakai ba"
Jikin Hafeez ne yayi sanyi sosai, "Insha Allah zan saki farin ciki, zaki manta rayuwarki na baya, bazaki fuskanci komai ba yanzu sai zunzurutun farin ciki da kwanciyar hankali, Zan maidaki tamkar kwai, zan zama miki uwa zan zame miki uba sannan zan zame miki yaya, Amal kece first love ɗina ban taɓa son wata yarinya ba a duniya kamar ke, soyayyarki acikin jinina da jikina yake, duk wani motsi da zanyi sai najiki acikin jikina, Amal duk bugun zuciya na yana bugawane da sunanki, wallahi ina sanki"
Kukane ya kwacewa Amal tacikin wayar, shima Hafeez kasa hanata yayi dan haka kawai yaji shima yanason ya zubar mata hawaye koda sau ɗayane, a hankali wasu Hawaye masu ɗumi suka fara bin lallausan kumatun Namijin duniya, Rabon Hafeez dayayi hawaye tun yana yaro, yau gashi yana yiwa mace wacce zata kasance matarshi,
A hankali tace "Nagode Yaya Hafeez"

YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.