🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 8**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim~Kallonta yayi dukda yaji sunan data Kira har cikin zuciyarshi amma yace "A,a ya Hafeez Kannena ma haka suke cemin Kinga ai kema kanwata ce, Amma fa kece wacce zan aura Dole asamu babancin Kiran sunana"
Kallonshi tayi Dan Bata gane meyake nufi ba, ganin yarinyar Kamar Bata gane abu, tana Nan Kamar doluwa-doluwa sannan akwai Rashin wayewa da Kuma Rashin shiga mutane a tare da ita yasa cikin sanyinshi yace "ki kirani da Baby Hafeez, zaki iya?"
Wannan manyan idanun nata takara warosu tana kallonshi dasu, ganin Bazata iya ba yasa yace "Toh jeki gida yaushe kikeso nadawo?"
Batasan lokacin datace Gobe ba, dad'i yaji domin ta karb'eshi hannu bibbiyu Kuma ya yaba da hankali da nutsuwanta,
Rakata yayi zuwa bakin kofa sannan yace "Bye Bye Good Night, have a nice dream"
Batasan meya fad'a ba kawai tace "Saida safe nagode" daganan tashiga gida cikin sand'a,
"La'ila ha illallahu Muhammadarrasulullahi sallallahu alaihi wa sallam, Amal Ina kikaje da tsakar darennan? Amal yawon iskanci kika fara? Nashiga uku Ni Aisha yau yarinya zata tonamin Asiri, jama'a yarinya tafara yawon iskanci cikin duhun lailatu"
Baba ne yayi sallama hannunshi rikeda bak'ar leda da Kuma calbi, jin maganar da yake fita daga Bakin Aisha wato mama yasa ya karaso wurinta ya ajiye ledan, cikin tsawa da matukar b'acin Rai ya nunata da yatsa yace "daga yau idan kika Kara Kiran yarinyar Nan da karuwa abakin aurenki, sannan duk lokacin da akazo wurinta indai Hafeez ne kikayi kuskuren hanata to Shima a Bakin aurenki"¹1
Tsit tayi tana rarraba ido, jiki taja ta koma d'aki, Saida tashiga can ciki sannan taciro wata 'yar karamar Nokia dinta ta Danna number datayi saving da Yaya, Ana d'agawa ta fashe da kuka, tace "Yaya Zainabu Asirina ya tono yanzu malam yadaina ganin darajana a gidannan inaga Aikinmu na yanzu beyi ba, wallahi ya daina tsorona yadaina jin maganata hankalinshi yagama dawowa kan 'yarshi tsorona shine kada ya tunano Mukhtar wallahi mutuwa zanyi, niban haihu ba Amma azo Ana shiga tsakanina da mijina na tsani yarannan wallahi musamman wannan Amal din yanzu itace tasani agaba Yaya.."
Kuka takuma fashewa dashi,
Ta d'ayan b'angaren akace "kiyi hakuri Aisha gobe zanje gidan Malam nayi mishi bayani komai zai dawo daidai ke ai kinsan aikina"
Cikin kuka tace "shiyasa ma nakiraki ban Kira yaya mairama ba, Dan Allah gobe da sassafe kijemin"
Saida tagama bayani kafin takashe wayar, Zama tayi abakin gado kafin tace "ai baku isaba wallahi ga Rashin haihuwa ga Bakin cikinku? Kun Isa?"Baba yabaiwa Amal hakuri tareda Mika Mata bakin ledan hannunshi yace "je kici wannan mamana"
Har kasa ta durkusa takarba tace "nagode Baba"
Juyawa tayi ta koma d'akinta, shikuma Baba tsayawa yayi Yana kallonta cikin tausayawa a lokacin yaji Yana kewar mahaifiyarta, "Maryam uwar hakuri, ga hakuri ga nutsuwa Allah yakai Haske kabarinki"
Idonshi ne yacika da hawaye, sharewa yayi yazauna yafara lazimi,Tana shiga d'aki tabud'e ledan ganin kilishi ne Wanda yaji Albasa da cabage ga yajin karago Asama da zafi zafinta yasa yawun bakinta tsinkewa, sa hannu tayi da sauri tafara ci, jin dadi yasa tacinye tass harda Albasan, Saida tagama kafin ta tuna Ashe ba'ason mace taci d'anyen Albasa, sharewa kawai tayi taje Tasha ruwa tayiwa Baba godiya tareda yimishi Saida safe,
D'akinta Takoma ta kwanta akan tabarmarta Wanda yanzu ta cikashi da tsumma yazama Kamar karamin katifa, Tunanin wannan mutumin da batasonyi d'inne yazo Mata zuciya, Tabbas da zata Ganshi babu abinda ze hanata caccaka mishi wuka a wuya Koda hakan zeyi sanadiyyar rasa rayuwarta, ta rantse da Allah gara ta rasa ranta data kyaleshi a raye, kullum Bakin cikin abin Kara Zama sabo yake a zuciyatarta, "Fyad'e" shine abinda ta furta cikin Bakin ciki, runtse ido tayi tace "Allah ka nunamin shi Koda sau d'ayane na kashe shi, Allah kasan Amal bazata iya kashe Koda kwari ba, Amma zuciyarta tabata umarnin ta kashe wannan bawan naka, Allah kada kasa na mutu ban had'u dashi nad'au fansa ba"
Ko kad'an hawaye sun daina zuwa idonta, zuciyarta ya bushe batada buri Kamar taga an had'ata dashi Wanda batama sanshi ba, Shima Kuma tanada tabbacin be santa ba, batasan ta Ina zata fara nemoshi ba, shaida d'aya takeda shi, shine zoben hannunshi datayi kokarin kwacewa a lokacin sabida tasamu shaida, hannu tasa a karkashin tabarmar d'akinta taciro wata zobe kallon zoben tayi sosai sannan tace "insha Allahu saina d'au fansa" buga zoben tayi da kasa sannan ta tashi ta tattaka zoben da kafarta, jitake Kamar shi take takawa, Saida tagaji kafarta har yafara jini kafin tamaida zoben inda take ajiyewa, ganin zuciyarta ze iya fashewa yasa ta d'auko wani jakan datakesa takaddu aciki, dubawa tafarayi sannan ta d'auko wani littafi me suna AMANNA na Marubuciya Jamila Umar Tanko, kwanciya tayi tafara karantawa Nan taji hankalinta yafara kwanciya, littafinne ya d'auke Mata hankali sabida dad'in dayayi, gani take kamar a gabanta abin yake faruwa, (kunsan karatun littafi sai kaji Kamar a gabanka abin yake faruwa ko kuma ka rink'a Emerging, shiyasa wasu 'yammata suke ra'ayi wurin zab'en miji ko saurayi sai taga Kamar na littafin ze zo ya aureta, To True Talk shine ko ita marubuciyar wata mijinta be Kai saurayin naki ko mijinki kyau ba, you have to mind your business)
A hankali ta rinka samun nutsuwa tana cikin karatu har bacci b'arawo ya saceta._Asuba Tagari_
~Hafeez kasan mutuncin dayake tsakanina da mahaifin yarinyar Nan ko?"
Hafeez dayake zaune gefen mahaifinshi ne ya gid'a yace "Eh Abbu"
Cikin yanayin soyayya yace "To banason wasa Kuma kaga yarinyar nitsatsiya ce, kowani uba ze so d'anshi ya aureta sabida ta rike mutuncinta, tunda ta amince dakai to kaje kud'an Saba ku fahimci juna sannan afara maganar aure, inason duk abinda takeso kayi Mata sabida ita abin tausayi ce, duba da yadda tagirma ba mahaifiya sannan kishiyar uwar ba hankali shiyasa nakeso kayi sauri ka aureta kafin wani ya rigaka"
"To Abbu insha Allah"
"Allah yayi maka Albarka"
"Ameen"
Kallon sauran 'yan d'akin yayi sannan yace "ku Kuma kullum maganar danake muku shine ku rike mutuncinku Amma ke Abida yau kin fita babu hijabi kin leka kofar gida, ke Kuma Fatima kinje Unguwa da gyalle a jikinki, kunada hankali kuwa? Kunsan kowa Yana ganin darajana a unguwar Nan ku baku Isa ku zubar min da Mutunci ba ko?"
Shiru sukayi suna rarraba ido kowacce ta sunkuyar da Kai tana kallon tiles na ciki d'akin, cikin fad'a Abbu yace "A matsayinku na Mata ai basai an fad'a muku bama ku kanku kunsan Abu me kyau sannan 'ya mace Abu kad'an takeyi afara yimata wani gani gani, wallahi Abida da Fatima idan baku kiyayeni ba saina b'ab'b'allaku"
Shiru d'akin yayi, sannan a juya wurin wata kyakkyawar Mata wacce takeda d'an jiki fuskarta sanye da farin glass kana ganinta kasan itace ta haifi Hafeez da sauran 'yammatan d'akin, yace "ke Kuma Hajiya kina ganinsu suna fita haka bazaki yimusu fad'a ba?"
Tace "to ai ita Fatima gyallen datasa yanada girma yarufe jikinta gaba d'aya gashinta ne kawai tabar kad'an awaje Shima ai abin yayi ne, suna 'yammata idan basuyi hakaba waye ze auresu Alhaji?"
Wani harara ya banka Mata kafin cikin zafin Rai yace "Wato barin gashin datayi be haramta ba,shi karamin laifine ko?"
Sunnar da Kai tayi kasa, yace "Amsamin zakiyi, bakisan zunubin da ake rubuta Mata ba shiyasa da kinsan zunubin da ake rubutawa wacce tabar gashin kanta Koda kwara d'ayane awaje cikin sani da kowacce mace tafara rufe gashinta, ku iyaye Mata kudaina d'aurewa yaranku gindi suna aikata abinda sukaga dama Kuma ku b'oyewa Uba, domin hakan babban kuskure ne, Ni kunsan inada zafi Kuma bana ganin gaskiya inki fad'a, Kuma yazama Dole nafad'a muku gaskiya, kutashi kubani wuri"
Sum sum suka Mike duka tareda mamansu suka fita daga falon, upstair ne, sauka kasa sukayi duka, Kallonsu tayi tace "kunji ko? Saiku kiyaye"
Abida ce ta leka tace "Mami mun gode da kika taimakemu da yau munsha duka"
Hafeez ne yazo sauka daga kan stair d'in, Kallonsu yayi sau d'aya ya watsar, wucesu yayi fuskarshi ba alamar fara'a, Fatima ce takalli Abida tace "Yaya ma yanata hararanmu muyi sauri mutafi d'aki kafin yadawo"
Dakinsu suka wuce, kowacce tasan tayi laifi.Alhaji Yusuf kenan, mutumin da bayason raini ko kad'an yanada fad'a sosai saide yanada kyauta, motoci yake siyarwa Wanda har kasar waje Yana zuwa siyan mota, ganin kokarinshi yasa masu kampanin marcedes suka had'a hannu dashi, duk wani manyan mota idan ze shigo to dasa hannunshi zai shigo Nigeria, yanada Mata d'aya Hajiya Saratu, Sai Yaro d'aya wato Hafeez, Sai Kuma Twins 'yammata sune Abida da Fatima, duk kud'inshi besa yabar yaranshi suna yin abinda sukaga dama ba, karatu da Kaya dakuma rike kud'i sai yadda sukaso amma ko kad'an bayason abinda ze tab'a mishi Mutunci, hasalima Yana iya Yin komai akan mutuncinshi, daka tab'a mishi mutuncinshi da Kuma Mutunci gidanshi gara ka tab'a mishi dukiyarshi koda ko zaka gama dukiyar ne, Haifaffen garin Kano ne, yayi gadon Arziki daga Mahaifinshi Wanda yadade da rasuwa, duk garin babu Wanda be sanshi ba, d'anshi Hafeez yayi karatu a kasar waje inda ya karanta likitan kwakwalwa, Abida da Fatima Kuma suna University anan kano, Hafeez ya kasance nitsatse saide yanada miskilanci sosai, be fiye magana ba hakanne ma yasa bashida abokai dayawa, yanasa hankalinshi sosai akan aikinshi na Likitanci ta wurin kwakwalwa, hakanne ma yasa Abbu yabud'e mishi Asibiti me suna Hafeez Special Huspital, Mata dayawa suna kawo mishi Hari Amma tun asali shikam idonshi akan Amal yake, Shima Hafeez Yana kokarin kare mutuncin mahaifinshi Kamar yacce yaga mahaifinnashi yanayi, sannan yanason kannenshi sosai, Kuma Yana Shiri da Maminshi wato mamanshi, ba karamin Dad'i sukaji ba lokacin da Hafeez ya amince ze auri Amal sabida Abbu shine yayi mishi maganar, saide basusan sunyi sarane akan gab'a ba, sabida d'ansu yadad'e dafara son yarinyar.
_Wannan kenan_
*Wattpad*
Jiddah S Mapi
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.