Chapter 11

206 19 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

   
  *Chapter 11*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim

              ~Ya Hafeez kwana biyu munga ka canja mana ba Kamar yadda muka saba ba, wallahi bamajin dad'in hakan, cewar Abida wacce take zaune a gefen Yayan nata, kawar dakai yayi bece komai ba, tace "Ya Hafiz mun sanka da hakuri Dan Allah kafad'a Mana laifin da mukayi"
Shiru Yakuma yi, ganin tanata rokanshi yasa yace "bakumin komai ba Amma meyasa kuke fita ba d'ankwali?"
Abida tace "kayi hakuri Dan Allah"
Yace "ya wuce Amma ku kiyaye gaba"
Cikin jin dad'i sukace "to yayanmu mun gode"
Tambayarsu yayi yace "Ya school d'in Yana tafiya daidai Kam?"
Fatima tace "gaskiya school akwai wahala Kuma inajin kishin kishin wai za'a shiga trike"
Yace "shiyasa nacewa Abbu yakaiku kasar waje kuyi karatu lamarin karatun kasar Nan akwai matsala wallahi, trike ko da yaushe ya sukeso 'ya'yan talakawa suyi ne fisabilillahi?  In this week wani aka kawomin wani patient wai yanada matsalar kwakwalwa, idan kunga yadda yake wallahi Zakayi tsammanin da gaskene yanada tab'un hankali, bayan naduba nayi bincike saina gano lafiyarshi kalau babu abinda yasamu kwakwalwarshi, nace ya sameni a office zamuyi magana, bayan munje office naje yazauna, nace bawan Allah meyasa kake karya da tab'in hankali bayan gashi kanada Yara da Mata?
Mutumin Nan yarinka kuka wallahi har jikina ya mutu, Saida yagama sannan yace wallahi narasa yadda zanyi ne, talauci yayimin yawa, yarana babu karatu matana banida kud'in kulawa dasu, gaba d'aya abinda yake kaina yafi karfin kaina din shiyasa naga banida mafita daya wuce in fara karyar tab'in hankali, Amma Dan Allah ka taimaka kada ka fadawa kowa Ni zan warke da kaina"
tausayin daya bani Saida nayi kuka"

Abida da Fatima jikinsu yayi sanyi sukace "Amma ka taimaka mishi?"
Yace "nabashi miliyan Biyu nace yaje ya taimaki kanshi, lamarin kasar sai a hankali, Dan Haka ku rinka godewa Allah a duk inda ya ajiyeku kada kud'in Abbu yasa ku daina ganin darajan mutane domin su mutane rahama ne"
Hira suka d'anyi Wanda cikinsa duk Nasiha ne Hafeez yake musu, jin Ana Kiran salla yasa duk suka tashi sukaje sukayi salla, bayan sun idar Abida tace "Ya Hafeez bamuga untyn tamu ba"
Kallon Abida yayi yace "Amal?"
Tace "Eh"
Murmushi yayi Dan Kamar sun sani itace yanzu Haka yake tunawa, wayarshi yaciro daga Aljihu yakunna gallery yashiga sannan yamika musu, kallon screen d'in sukayi duka suka sa ihu, Fatima tace "what a Cute and Beautiful Lady"
Abida tace "wow Yaya wallahi ka iya zab'e kaga wani ruwan kyau? Yaushe zaka kaimu mugaisa?"
Yace "duk Randa kuka shirya"
Fatima tace "Jibi Yaya"
Yace "Allah ya kaimu"
'Dakinshi yaje Yana kallon hotonta, Zama yayi akasan tiles ya d'aura kanshi akan center table d'in dayake tsakar d'akin, baya gajiya da tunanin yarinyar, gashi yaji dad'i da kannenshi suka yabeta, wani miskilin murmushi yayi sannan yace "Allah ya nunamin ranar dazaki zo d'akina da sunan Mata, aranar zanyi kyautar kujeran makka wa mutane dayawa"
Lumshe ido yayi tuna yadda take magana leb'en bakinta yana motsawa, jiyayi jikinshi yafara mutumuwa, a hankali ya karasa kan lallausan Chinese Capet d'in dayake shinfid'e cikin d'akinshi throw pillow yad'auko me gashi ajikin da laushi sannan yasa a kirjinshi ya rungume, hotonta ya tsurawa ido jiyake Kamar yafito da ita ya had'iye ko zaiji saukin abinda yake damun zuciyarshi, ji yayi baze iya hakura dajin muryanta ba a wannan lokacin, shiga Contact yayi sannan yashiga sunanta Wanda yayi saving da My Amal da Alamar heart dakuma makulli, dannawa yayi Nan yakara a kunnenshi,
Amal datake bangida tana wanka jitayi wayarta tana Kara, da sauri ta watsa ruwan tafito da gudunta, bayanta duk kunfa, bataso wayar ya yanke Dan Bata iya Kira aciki, daidai da Kara shigowan Kiran ta karasa d'akin, Ganin sunan Yaya Hafeez Yana yawo yasa tayi murmushi sannan ta Danna green alamar amsawa, karawa tayi a kunnenta tace "Salamu Alaikum"
Hafeez dayake kwance akasa yaji muryanta ya daki kahon zuciyarshi a hankali yace "Wa alaikissalam My Amal, I Miss you so much"
Shiru tayi batace komai ba, yace "Ina kewarki sosai yau"
Cikin jin kunya tace "nima nayi kewarka"
Yace "ban yadda ba tunda Baki kirani ba"
Da sauri tace "Allah da gaske nayi kewarka ya Hafeez"
Yakuma cewa "ban yadda ba"
Kamar zatayi kuka "Tace bafa karya bane da gaske nake" a shagwab'e tayi maganar, this is the first time da tayi mishi shagwab'a dukda tanada zubin shagwab'ab'b'u Amma Bata fiye yimishi ba sabida Rashin sabo, jiyayi har cikin jikinshi ya amsa wannan shagwab'ar, da zazzakar muryanshi yace "ki Kara yimin shagwab'an My Amal ya birgeni"
Ganin Kamar Raina Mata hankali yakeso yayi yasa cikin murya Kamar zatayi kuka Tace "Dan Allah ka yadda"
Shiru yayi mata, ganin hakan yasa ta zauna akasa dirshan tafara kukan shagwab'a harda bubbuga k'afa, Kamar yashiga wayar ya sace Amal haka yakeji ajikinshi, Saida yaga da gaske take zatayi kuka yace "Sorry shikenan na yadda, tashi to"
Tashi tayi ta zauna me kyau yace "Good Girl, na yadda kinyi kewata, munyi magana da Abbu yace zeje yasamu Baba suyi magana akan makarantarki"
Cikin jin dad'i tace "toh nagode ya Hafeez Allah yabiyaka da gidan Aljanna"
"Ameen"
Hira suka fara me dad'i, sun kashe badan sun gaji dajin muryan juna ba, saidan Kiran salla da ake a masallaci,
Amal Yana kashewa tace "Ina sonka sosai Yaya Hafeez"
Sai a lokacin ta kukada yanda omo ya Bata Mata jiki, cuno Baki tayi tana kallon jikin nata, tashi tayi Takoma Toilet ta wanke jikinta, Yana katse wayar fuskarshi cikeda Annashuwa yace "Ashe Baby Amal ta iya shagwab'a haka, Har tafara rikitamin lissafi"
Tashi yayi yawuce d'akin Mami, ganin tana zaune yasa ya karaso wurinta ya zauna gefenta, tace "Hafeez yanaga kana cikin farin ciki?"
Hafeez yace "babu komai"
Mami murmushin manya tayi Dan tasan Hafeez soyayya ce take d'awainiya da zuciyarshi Kuma ba soyayyar kowace mace bace face na Amal, hakanne yasa yarinyar take kara Shiga cikin zuciyarta, Tace "nunamin hotonta"
Da mamaki ya kalli Mami yace "wace?"
Tace "wacce take saka murmushin"
Kunya yaji sosai sannan yabud'e wayarshi ya nuna Mata hoton Amal "kaii masha Allah surikar tawa kyakkyawa ce tabarkalla"
Murmushi yayi kawai najin dad'i, Mami tace "gata da Haske ga gashi Dan daganin goshinta zatayi gashi"
Baice komai ba sabida kunya, Mami Tace "Wannan Ni da kaina zanje Dubai na had'a Mata lefe, sannan zamuyi gagarumar biki Wanda duk garin Kano sai sunsan d'ana yayi aure, ga amaryar kyakkyawa ta nunawa a Duniya ai kaikam kazo Duniya da sa'arka"
Hafeez ji yayi kamar yatashi yayi tsalle tsabar farin cikin dayake ciki, Amma be nuna hakan ba sai murmushi dayake, Mami Tace "kayi kokari tafara zuwa school sabida tad'an Kara wayewa kaji?"
Yace "To Mami ran Monday ma nakeso tafara zuwa"
Mami Tace "Masha Allah yanzu zan hau online anjima na duba wasu kayayyaki Wanda za'a zubasu duka acikin lefen"
Godiya yayiwa Mami sannan yatashi yakoma d'akinshi, Shiri yayi da uniform nashi na doctor, Saida yayiwa 'yan gida sallama kafin yawuce (Hafeez Special Huspital Wanda Asibitin yake mallakinshi ne)
Yana parking mutane suka fara mika mishi gaisuwa tsayawa yayi suka gaisa cikin mutunci kafin yawuce office d'inshi, bai dad'e a office ba yafara zagayawa Yana duba marasa dasuke kwance a d'akunansu, kowa na wurin gaisheshi yake, sakin fuska yayi domin shi idan Yana cikin patience d'inshi farin ciki yake koba komai zaka Kara Imani idan kana zuwa Asibiti, zaka godewa Allah da lafiyan daya baka.

_wannan kenan_

 

     *Wattpad*
Jiddah S Mapi

MUTUNCINA!!!Where stories live. Discover now