Chapter 13

285 25 5
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     Na
Jiddah S Mapi

   
  *Chapter 13*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim


               ~A Haka tafara zuwa school, yanzu Kam ta d'inka uniform wandone ruwan ganye sai farin Riga daidai gwiwa da Kuma hijabi Shima ruwan Ganye, Jaka Baki da takalmi sneaker Baki Hafeez ya siya Mata, rayuwarta yafara yimata dad'i yanzu, dukda tana cikin Bakin ciki wani lokacin Amma kyautatawan da Hafeez yake mata yanasa taji dad'i cikin zuciyarta, gidansu Hafeez sun shigo sunyi gaisuwa sannan sun nemi azinin aurenta a wurin mahaifinta, yanzu magana ya zauna Ana zance ranar kawo sadaki dakuma sa ranar aure,
Shak'uwa me yawa ne yake shiga tsakaninta da Hafeez, sun shak'u sosai, Abida da Fatima ma sun Saba da ita domin yanzu har gidansu suna zuwa, Kuma suna waya sosai sannan suna chatting dukda sun girmeta Amma suna kiranta da Unty Amal, tun tana nok'ewa Bata amsawa, har tafara cemusu su daina kiranta da Unty, ki sukayi har saida tafara Amsawa,
B'angaren Aisha Wato Mama tanajin Bak'in cikin abin Amma babu yanda ta iya sabida Baba yayi Mata iyaka da Auren, gashi yanzu asirinta yadaina kamashi gaba d'aya Bata jin dad'i a fuskane kawai take nunawa Amma a zuciyar bahaka bane.
Amal tayi sabbin kawaye a school Wanda suka Saba sosai, musamman kawarta Farida wacce takeda hankali sosai, tana zuwa gidansu Farida sabida Iyayenta sunada mutunci Kuma Koda abinci Farida zatazo school dashi, to a gefe saita zo dana Amal, sai Tace "ga naki inji mama" hakanne yasa Amal shak'uwa da Farida sosai Wanda har idan sun Zauna da Hafeez kullum sai tayi mishi maganar Farida.

Yauma kamar kullum bayan an tashi daga school sun fito tareda Farida suna Hira, dariya Amal take itama Farida Haka sabida Wandon wani d'an class nasu ya yage, Amal dukda tanada tsoro Amma Bata ki yin dariya ba, Hangoshi tayi acikin mota Yana jiranta da sauri taja hannun Farida suka karawa wurinshi, ganinta yasa yasaki murmushi, bud'e motar tayi tace "Ya Hafeez?"
Yace "yes Baby Amal"
Dariya tayi Tace "Kaine anan?"
Yace "yau free nake shiyasa nacewa Driver ya huta yau Ni zanzo na d'auki Matata"
Dariya ta kumayi fararen hakoranta suka bayyana, Nuna Farida tayi zatayi magana yace "Wannan itace Farida"
Da mamaki ta waro ido jin yafad'i abinda take niyan fad'a,
Ya d'aga Mata gira yace "yeah nasan abinda yake zuciyarki ai"
Farida ce ta karaso Tace "Ina wuni?"
Yace "mun yini lafiya?"
Tace "lafiya kalau"
"Ya karatu ya su mama?"
"Suna lafiya"
Saida suka gama gaisawa yace "yau Allah yahad'ani da Best Friend na Matata kullum Farida sai yau Allah ya had'amu dake"
Dariya Farida tayi Tace "nima kullum Ana bani labarin Yaya Hafeez sai yau Allah yahad'amu"
Cikin sakin fuska sukayi kyakkyawar gaisuwa, Tace "To Besty nikam zan shiga Napep sai gobe ko?"
Amal Tace "Kizo Yaya Ya saukeki a gida"
Tace "A,a wallahi zan tafi"
Hafeez yace "lalala ai baze yiwu ba dolene yau mu saukeki agida kafin muwuce"
Da kyar de ta yadda tashiga motar, Amal ce agaba, shikuma a mazaunin Driver Farida Kuma abaya, Hira suke sosai Kamar dama sun Saba, da kwatance suka iso gidansu Farida, ajiyeta sukayi sannan tayi godiya, wucewa sukayi zuwa gidansu Amal, a hanya yace "kinsan me?"
Tace "A,a saika fad'a"
Yace "Ranan Friday Abbu ze kawo sadaki daganan asa Rana"
Cikin murna tace "gaskiya naji dad'i"
Da wasa yace "kina yarinya yanzu zakiyi aure?"
Rufe fuska tayi Tace "niba yarinya bace"
Kallonta yayi daga sama har kasa a ranshi yace "Yarinya ce da jikin manyan 'yammata"
Afili Kuma yace "Yarinyace Mana shekaranki fa goma Sha Bakwai San June zaki cika Sha takwas"
Turo Baki tayi Tace "nidai ba yarinya bace"
Kawar da maganar yayi yace "yawwa wani irin fenti za'ayi Miki a gidanki?"
Waro ido tayi Tace "gidana?"
Yace "eh gidan dazamu zauna idan munyi aure mu biyu dake"
Rufe fuska tayi alamar kunya,
Yayi murmushi yaciro wayarshi, hoton wani gida ya nuna Mata yace "ga gidan saide fenti ne ba'ayi ba Kuma nafison ki fad'amin favorite color d'inki"
Kallon gidan tayi ganin kamar ba anan Nigeria bane yasa Tace "A kasar wajene wannan wurin?"
Yace "A,a kinason Zama a kasar waje ne?"
Tace "A,a Naga gidanne Kamar a kasar waje"
Murmushi yayi yace "a Abuja gidan yake acan zamu zauna sabida aikina"
Tace "Ni gaskiya bazan iya zama a wannan katuwar gidanba saide ka kamamin haya me d'aki d'aya da kitchen d'aya Sai Kuma d'akinka, wannan gidan yayi girma"
Dariya yayi sosai kafin yace "ai ad'aki d'aya zamu zauna"
Waro ido tayi Tace "A,a nikam"
Karb'an wayar yayi Dan yasan idan yabiye tata bazata fad'i komai ba sai shirme yarasa meyasa Amal batada wayo kamar karamar yarinya dukda Yana school,
Amal kuwa ta b'angaren ta tasan kawai zuwa school d'in take Dan Bata gane komai, Koda tasa hankali ta koya Bata iyawa kyaun ne kawai ba kwakwalwa,
Saida suka iso ya ajiyeta sannan yace "Baby Amal? I love you"
Tace "Love you too"
Murmushi yayi jin tafara koyan magana da turanci,
Tace "have a nice day"
Waro Ido yayi yace "Me kikace?"
Dariya tayi tagudu, dad'i yaji Dan tafara koyan wasu abubuwan, ranshi fess yabar unguwar.

 
               "Nabil Muhammad Mailafiya mun amince da bukatarka na had'a hannun jari damu cewar Mr Gang, mutumin dayake da company a Egypt, Wanda ya amsa gayyatar Nabil,
Hawaye ne suka taru a idanun Nabil abinda be tab'a yiba kenan, yau ba karamin Dad'i yajiba jin Mr Gang ya yadda zasu had'a hannun jari, tashi yayi ya rungume shi sannan yayi godiya, Mr Gang cikin harshen turanci yace "saide inada sharad'i"
Nabil yace nayadda da kowani sharad'i naka, Mr Gang yace "Banason cin Amana, banason kaci amanata duk Wanda yaci amanata a harkan kasuwanci bana barinshi yaji dad'in Duniya"
Amsawa Nabil yayi yace "na amince"
Har airport yarakashi saida jirginsu ya tashi kafin Nabil yashiga motarshi cikin jin dad'i yanufi gida, yau farin ciki yake sosai, yana shiga falo ya hango Ammi tsaye tana waya, rungumeta yayi da karfi Yana murna, Ammi cire hannunshi tafara daga jikinta Tace "meyafaru?"
Kin sakinta yayi sai murna dayake,
Ammi tureshi tayi Tace "lafiyanka?"
Yace "Ammi nayi nasara"
Tace "nasaran me?"
Yace "Mr Gang na Kasar Egypt ya had'a hannun jari da Company d'inmu"
Ammi cikin farin ciki Tace "da gaske kake?"
Wallahi da gaske nake gama hotonmu dashi yau a office d'ina, nuna Mata yayi Ammi cikin jin dad'i Tace Allah yayi maka Albarka d'ana"
Yace "Ameen"

"Congratulations my Son dama nasara a jikinmu take"
Cewar Abba dayake saukowa daga Upstairs cikin Shirin manyan Kaya, hannunshi rikeda Jaka da alama office ze tafi, zuwa yayi wurinsu ya rungume Nabil yace "nasan bakyajin magana Amma nasan akwai nasara da sa'a a tattare dakai domin kanada tunani, Naga Mr Gang yasa a shafinsa na Instagram cewar yahad'a hannu da Mailafiya Sugarcane Company, ba karamin Dad'i naji ba, domin hakan ze Kara bunk'asa kasuwancinmu a Duniya sannan Mutuncinmu ze Karu a idon duniya, Allah yamaka Albarka"
Ameen Nabil yafad'a,
Abba yace "Asanadin wannan farin cikin daka sani Nabaka kyautar Private jet"
Wani irin tsalle Nabil Yayi ya rungumi Abba yace "thanks you Abba"
Abba yace "nine da godiya Dana samu d'a Kamar Kai Ina Alfahari dakai".

  *WATTPAD*
Jiddah S Mapi

MUTUNCINA!!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora