🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 15**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*~Saida suka shiga wani lafiyyayen Falo kafin taga wata kyakkyawar mace fara sol gata da kiɓa tana murmushi, kana ganinta kasan ta jiku da arziki, fatar jikinta na hutune sosai, hannu ta ɗagawa Amal tace "Oyoyo ƴata"
Amal da murmushi a fuskarta ta sunkuyar da kai,
Karasowa Mami tayi ta rungume Amal, tanayi Mata sannu da zuwa, gaba ɗaya jikin Amal yayi sanyi ganin yadda masu Kuɗi irin wannan suke tarbanta kamar badaga gidan talakawa ta fito ba,
Mami tariko hannunta tace zaunar da ita akan Sofa, kokarin sauka kasa Amal tafara da sauri Mami tace "A,a banason bakunta, keba bakuwa bace a gidannan kamar yadda su Abeeda suke haka kema kike acikin gidannan kinji?"
Giɗa kai tayi takoma ta zauna a ɗan takure,
Fateema ce tashigo da katon plate a hannunta wanda ta cika da kayan drinks da snacks, ajiyewa tayi da murmushi a fuskarta tace "Unty Amal You are Welcome"
Murmushi tayi mata tace "Nagode"
Abeeda tace "Fatima kiga yadda anty Amal tayi kiɓa da haske?"
Fatima tace "Wallahi abinda nakeson faɗa kenan harta zama wani yellow, Gashi tayi kiɓa"
Mami tace "banson sa ido ku waya hanaku kuyi kiɓar?"
Shiru sukayi,
Mami tashi tayi tace "idan tagama ku Kaita Up Ina jiranta naga ta kasa sakewa a gabana"
Hawa sama tayi, Su Abeeda matsowa sukayi wurinta suka fara Hira, nan da nan ta saki jiki harda shan Ruwa da Doughnut,
Hafeez daya canja kaya daga shadda zuwa wani riga da wando na Gucci, yabuɗe kofa ta ɗayan ɓangaren t
Yashigo, yayi kyau sosai amma fuskarshi ba walwala da alama har yanzu fushi yake da ita,
Abeeda suna ganinshi suka mike zasu tafi yace "ina zakuje?"
Fatima tace "Zamu baku privacy"
Tsaki yaja yace "ku koma ku zauna banson munafinci"
Komawa sukayi suka zauna itakuma Amal tayi shiru tana kallon kasa, Da Mamaki taga ya Zauna a gefenta har jikinshi yana taɓa nata, da sauri taɗan matsa, ɗago kai yayi ya kalleta,
Su Fatima ne suka fara janta da fira, buɗe baki tayi tafara basu labarin school ɗinsu da yanda wandon wani yaro ya yage yau, itada Kawarta sukayi ta mishi dariya,
Tana bada labarin tana dariya kamar a lokacinne abin ya faru, shagala yayi da kallonta, gaba ɗaya hankalinshi ya mayar kanta, yanda take dariya tanasa hannu a baki hadda rike ciki shine yake birgeshi,
Da alama tama manta inda take,
Tuno ba'a gida takeba yasa tadawo hayyacinta da wuri,
Kallonshi tayi har zara-zaran gashin idonta yafara jikewa da hawaye tsabar dariya, signal tayi mishi Alamar yadai?
"I love You"
Shine abinda yafito daga bakinshi, kawar da zancen tayi tace "Teema yaushe..."
Da sauri yakuma cewa "I love You Baby Amal"
Kallonshi tayi, shin ya manta dasu Abeeda a wurin ne? Shine tambayar datayiwa Kanta.
Yatsa ta ɗaga a hankali tana nuna mishi su Abeeda, riko yatsan yayi yasa a bakinshi yace "Wallahi Ina sonki Amal, Zuciyata zata fashe idan baki taimakaketa ba, dan Allah kisoni koda rabin yadda nake sonki ne"
Janye yatsanta ta fara, shikuma yaki saki,
Abeeda da Teema ne suka mike sulum-sulum suka fara tafiya, da sauri suka hau sama ba wanda yakara juyawa a cikinsu,
Saida taga sun tafi kafin taja hannunta da karfi ta tureshi tace "Dan Allah baka ganinsu Teema ne?"
Yace "Ni ke kaɗai nake gani"
Haɗe fuska tayi alamar yasata a kunya,
Matsowa yayi kusa da ita yace "Baby Dan Allah kice kina sona"
Turo Baki tayi itakam tarasa meyasa ya canja tunda akasa musu rana gaba ɗaya ya rikice yafara koma mata me suffan ƴan iska,
Yace "Baby fa"
Ganin tayi shiru yasa yace "wallahi idan baki faɗa ba zan rungume ki"
Da sauri tace "I love You"
Daɗi yaji sosai yace "ƴan Class naku sunada ilimi?"
Tace "Eh Ana koyo gaskiya a school ɗin"
Nan tafara bashi labari, ya fahimci tanason hira sosai kawai girman takurane yasa tazama shiru-shiru
Labari take bashi suna dariya acikin labarinta yagane akwai yarinta a kanta sosai, biye mata yayi sunata hira, yace "Baby kinason bada labari"
Tace "Sosai ma kaima naga kanason jin labari"
Yace "sai munyi aure zaki rinƙa bani labari me daɗi ko?"
Giɗa kai tayi,
Yace "Amma saina kwanta a cinyarki kina shafa wannan Black hair ɗina kina bani labari"
Da sauri ta kawar da kanta jin Abinda yafaɗa gaba ɗaya kunya yake sata ji,
"Ƴata ya bakisha komai ba"
Mami ce tayi magana yayinda take saukowa daga upstair, da sauri Amal ta tashi tazauna a hannun kujera dan sunyi kusa sosai,
Murmushi Mami tayi tace "Taho muje"
Riko hannunta tayi suka fara hawa sama, ɗakin Mami suka shiga, Amal nata ido, sai kallon komai takeyi da idanunta,
Suna shiga Mami ta rufe kofar ta kuma riko hannunta suka karasa ciki, a bakin gado ta zaunar da ita sannan itama ta zauna a gefenta, Drawer dake gefen bed ɗin ta buɗe taciro wani Babban leda, kwance ledan tayi sannan taɗau wani siririn sarka me kyawun gaske tabuɗe, tashi tayi tasawa Amal a wuya ganin yayi mata kyau yasa tace "nabaki kyauta"
Cikin girmamawa Amal tace "Nagode Hajiya"
Mami tace "ki kirani da Mami"
A hankali tace "Nagode Mami"
Zama tayi ta ɗauko ledan ta buɗe taciro wani abu acikin Roba babba, tace "Kinga wannan? Zaki rinƙa sha da madara kullum da safe akwai madara acikin ledan, ta ɗau wani tace "wannan kuma haka zaki rinƙa sha kullum da daddare kaɗan kaɗan kinji"
Tace "Eh Mami"
"Good Girl"
Da alama Amal Bata fahimci menene abun ba,
Mami tace "Amal!!!"
Amal tace "Na'am"
"Hafeez bai taɓa son mace Kamar yadda ya soki ba, bamuyi tunanin Hafeez zai so mace haka ba a rayuwarshi, dan Allah Amal ki rike Amana ki soshi ki kula dashi, ki taimaka mishi Hafeez yana sonki, sannan Hafeez yanada wani abu guda ɗaya, yana saurin sa abu a ranshi idan yasa abu arai har sai anyi mishi faɗa domin baya cirewa idan ma yacire yana zuwa yazame mishi cuta, cutan da har Aman jini zai iyayi, inayi miki wannan Maganar ne a matsayin Mahaifiyarki, ki ɗauka cewar nice na haifeki, Amal bansan meyasa ba soyayyar da Hafeez yake miki sainaji nima inayi miki irinta, wallahi nida Hafeez da Babanshi da kannenshi muna sonki, ki rike mana Amana kishigo gidanmu a matsayin ƴa kizo mu zauna kamar mu muka haifeki"
Amal hawaye tafara tace "Insha Allah Mami, nagode.. Nagode.. Nagode sosai"
Mami tace "Nima nagode"
Jakanta ta buɗe taciro kuɗi sanin cewar Amal bazata karɓa ba yasa tasa mata a jaka tareda abinda tabata,
Saida suka zauna dasu Teema suka kara Hira kafin Hafeez yazo yace "To Muje ko"
Abeeda tace "dan Allah yaya Hafeez kabarta ta kwana"
Harara ya watsa mata kafin yariko hannun Amal yace "Muje"
So take ta kwace hannun amma yahana, Mami dake tsaye a bakin kofarta tana kallonsu tana murmushi har suka shiga mota suka fita, hawayen farin ciki ta share kafin ta juya tashiga Ɗaki,
A hanya ya kalleta yace "Me Mami tafad'a Miki?"
Tace "Sirri ne"
Da mamaki ya juya ya kalleta, tace "ka kalli hanya da kyau"
Yace "wato zancene tsakanin Uwa da ƴarta?"
Tace "yawwa ashe ka gane"
Murmushi yayi yace "To nikam bana ciki kenan?"
Tace "Eh kai baka ciki"
Shiru yayi ya kunna kira'a yanabin bakin malamin, itama bi take a zuciyarta, bayan sun iso yace "ki gaida su Baba"
Kallonshi tayi tace "Bashiga gida zanyi ba"
Yace "me zakiyi to dare yayi yanzu fa 9"
Tace "kiss zanyi maka"
Waro ido yayi yana kallonta, tace "Yes bakai kace kanaso ba?"
Shiru yayi, tace "to matso" fara matsowa tayi da sauri ya matsa, takara matsowa, zuwa tayi daidai fuskarshi tayi kamar da gaske zatayi mishi da sauri yace "Dan Allah kada kiyi"
Kallonshi tayi tace "um um kaifa kace kanaso"
Yace "nifa wasa nake miki"
Tace "A,a sainayi"
Gaba ɗaya yawani td
tsorata yana ja da baya, dama tasani ba halinshi bane da gayya take mishi hakan, tasan baze taɓa yadda ba, ganin da gaske take yasa yafita a motar da sauri yaje ya buɗe mata kofa yace "kishiga gida 9 yayi"
Fita tayi tana dariya, tasan Hafeez da kunya yake yau kaɗai ace ya canja hali? Shiyasa ta gwada domin tabbatar da hakan, Gashi kuma tagani,
Ya ganeta shima kawai yashiga motarshi yana dariya.
YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.