Chapter 23

193 10 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸

      Na
Jiddah S Mapi

*Chapter 23*

     *____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

      

             ~Zuciyar Fadila cike yake fal da tambayoyi saide tarasa wa zata tambaya, gashi Hamma Sadauki yaja kunnenta akan Tambayar Amrish, ga Amrish da Wauta yanzu tana tambayarta zata faɗa mishi, haka kawai taja bakinta tayi shiru, yanzu Burinta kawai ta haihu lafiya domin neman Abinda yafiyar da ita duniya.
Cikinta yana daɗa Girma kuma yafito sosai, babu abinda yakeyi mata daɗi kamar idan taji cikin ya motsa sai taji zuciyarta tayi sanyi ta tabbata zata samu wanda zai tayata yaƙin neman ƴancinta

Kwance take akan gadon Inna tana karatun littafi Kamar kullum, Innace tashigo hannunta rikeda wani magani, mikawa Amal tayi "Inna wannan Kuma na menene?"
"Jiƙawa zakiyi ki rinƙa sha safe da yamma wannan zaisa idan kinzo naƙuda yayi miki sauƙi"
"Haba Inna wannan magunguna ai sunmin yawa Ni tsoro ma nake kada ya illatamin yaro" tafaɗa tana turo baki haɗe da ajiyewa Inna Maganin a gefe, Salati Inna tafara tana tafa hannu, gyara daurin zaninta tayi tace "Amalu Ni kike faɗawa haka? Ni zakiyiwa Gorin haihuwa dan ban taɓa haihuwa ba? Shine zakice kada na illata miki yaro?" Kuka matan take tsakaninta da Allah, ganin haka yasa jikin Amal yayi sanyi, wallahi batayi tsammanin Inna Bata taɓa haihuwa ba har cikin Ranta da wasa tafaɗa, riketa tayi tana cewa "kiyi hakuri Inna wallahi ban san baki taɓa haihuwa ba"
"Hakane nasan baki sani ba ƴata kuma kin faɗa ne cikin wasa amma dole abin yamin ciwo, Ni Allah bai taɓa bani haihuwa ba"
Shiru Amal tayi, Inna tace "ki shirya ranar Litinin zakuje Asibiti a birni in Allah ya yadda domin me ciki dolene ta rinƙa ziyartar Asibiti"
"Toh" kawai tace, buɗe labulen yayi Yashigo fuskarshi ba yabo ba fallasa, wani irin kallo yake yiwa Amal, bakinta na rawa tace "ina wuni?"
"Idan kinsan kuka zaki rinƙa sa ƴan gidannan ki tattara kayanki kibar gidan, koda shike babu ma kaya kikazo sai wanda aka taimaka miki dashi, ki tashi kibar gidannan yanzu"
Jikin Amal ne yafara ɓari ganin yanda yake maganan tasan da gaske yake, hakuri tafara bashi cikin tsawa yace "kitashi nace"
Tashi tayi idonta har ya cika da Hawaye Inna tace "dawo ki zauna"
Cikin tsoro ta dawo ta zauna tana kallon kasa, Inna Tace "Jeka zata gyara"
Fita yayi a zuciye domin ranshi ya mugun ɓaci yarinyar tanada shishigi da yawan tambayoyi shikuma a halin yanzu babu abinda ya tsana kamar tambaya, tafiya yayi yabar gidan, daji yaje bakin wani babban Kogi ya zauna, nannaɗe kafar wandonshi yayi yasa kafafuwanshi cikin ruwan, duwatsu ƴan kanana ya ɗauko yana wurgawa cikin ruwan, yanayin yana bashi nishaɗi sosai, saida ya gama jefawa kafin yasa hannayenshi ya dafe kasa idanunshi akan ruwan yana tunani, abinda suka wuce abaya yafara zuwan mishi cikin kwakwalwar shi, a hankali hawaye suka fara sauka daga idanun namijin duniya gwarzon namiji Sadauki, hannu yasa ya share bayason tuna baya amma abinda yawuce yana yawan zuwa mishi akai, ruwan kogin ya ɗibo a tafin hannunshi yafara wanke fuskarshi, kallon kanshi yake acikin ruwan "ga kyau ga kwarjini ga farantaka amma babu amfaninshi Omer" abinda yake faɗa kenan acikin zuciyarshi, a fili kuma yace "kuka ba naka bane, kaifa gwarzon namiji ne, kaine kake kula da duk cikin Kauyennan kaine kake taimaka musu, idan kayi kuka su kuma me zasuyi? Yakamata na manta da baya dukda ba abune me sauƙi ba"
Saida gari yafara duhu kafin yabar Bakin Kogin, shi kaɗai yake tafiya acikin dajin babu alamun tsoro ko kaɗan atare dashi, saida ya isa gida yayi alwala yashige ɗakinshi, sallah yayi sannan ya zauna akan sallayan yayi shiruu, sallama akayi jin muryan Amrish yasa yace "shigo" shigowa tayi hannunta rikeda kwano, akasa ta ajiye sannan ta gaisheki yace amsa ta juya zata tafi, "Amrish?"
"Na'am" tafaɗa tana dawowa, zama tayi akasa yace "matso" matsowa tayi dab dashi, kallonta yayi yadda ta dukar dakai tana kallon kasa, ɗauke kanshi yakuma yi atake, da sauri yasa hannu ya goge hawayen dayake sauka a idonshi dan baison ta gani "Bakida wani damuwa?"
"A,a babu Hamma"
Wasu hawayen yaji suna kara sauko mishi, da sauri yace "okay you can go"
Bataji me yace ba "na'am?"
Yace "kije"
Tashi tayi ta tafi, tana fita ya kifa kanshi a sallayan yafara Raira wani ɗan Marayan kuka, ganin babu me rarrashinshi yasa ya baiwa kanshi haƙuri yayi shiru, kwanciya yayi awurin duk da cewar ɗakin babu haske amma ya kunna fitila irin ta ƴan gargajiya, taƙure kanshi yayi waje ɗaya "haƙiƙa wannan hukuncin shiya dace dani" abinda yafaɗa kenan ƙasa ƙasa.

MUTUNCINA!!!Where stories live. Discover now