🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 3**____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
~Bismillahi rahmani rahim~Saida ruwan yayi zafi kafin tadau bokiti a hankali takeyin komai, ruwan zafin tasa aciki Bata sirka ba, ta d'auka ta tafi Band'aki, bath ta d'auko ta zuba ruwan aciki, Zama tayi zafin ruwan ya ratsata, ihu take Shirin yi Amma tasa hannunta abaki ta tsoshe sabida kada ajiyota, hannu abaki tarinka kuka, daga zuciya har fuskarta kuka take, Saida ruwan yafara sanyi kafin taji d'an sauki, Saida ta gasa kanta kamar yadda take gani a littafin hausa (Novel) daganan tad'ibi ruwan tayi wanka, Saida tayi wankan tsarki kafin tayi wankan sabulu, zani ta d'aura a kirji sannan tasa hijabi, tad'au sabulunta da sosonta tafito, a hankali take tafiya tana bud'e kafa, gaba d'aya Bata hayyacinta daurewa kawai take, dakinta tawuce tadau paracetamol acikin wata 'yar Jakarta sannan Tasha, nanfa ta kwanta akan tabarmar d'akinta tafara bacci.
_Asuba Tagari_
"Ammi gaskiya abinda yaya yayi beyi daidai ba, akan me ze mari Inna? Innafa macece baya ganin mutuncinta? Koba komai ai ta haifeshi, kawai Dan Bata gama abinci da wuri ba, haba Dan Allah arink'a tunawa da Ubangiji mana" wata kyakkyawar yarinya ce black Beuty, idan ka ganta bazakayi tsammanin zata iya magana da harshen hausa ba, Dan gaba d'aya batayi kama da Nigerians ba, kamar daga Ethiopia tafito,
To saikizo ki dakeni kinji ko uwata? Nace kizo ki dakeni, naga kamar idonki yafara bud'ewa Noor, nice kikewa tsawa haka? Shi Yayan naki bazaki iya zuwa kiyi mishi magana ba?"
Cewar wata Mata datake zaune akan wani gado na Alfarma, da gani kasan itace mahaifiyar yarinya me maganar, domin kamanninsu yafito, saide matar farace katt sab'anin yarinyar Kuma bak'a, Amma hakan be Hana kamansu fitowa ba,
Wacce aka Kira da Noor ce ta turo Baki da gani kasan ranta a b'ace yake, cikin b'acin Rai takuma cewa "Ammi gaskiya fa nake fad'a kinsan da Abba Yana Nan wallahi..."
Filo Ammi ta d'auka sannan ta wurga mata, tace "to ai saiki kirashi tunda mutuwa yayi ba Yana raye, ki Kira number d'inshi na London kice yadawo yayiwa Yayan naki hukunci"
Shiru Noor tayi tana kallon Ammi datake ta masifa, tasan itace da gaskiya Amma mahaifiyar ta ce take magana dole tayi shiru sabida mutuntawa irinta 'ya da uwa"
Kafin Ammi ta karasa sukaga yashigo musu d'aki, Ammi tace "yawwa gashinan saiki fad'a mishi beyi daidai ba"
A tsorace Noor tad'ago kai tana kallon yayan nata, Wanda yake kallonta fuska ba yabo ba fallasa, a dakile yabud'e d'an karamin bakinshi kamar bazeyi magana ba yace "me kike cewa?"
Tace "bance komai ba"
Hanya ya nuna Mata yace "fita"
Fita tayi zuciyanta Yana tsinkewa, Saida takai Bakin kofa yace "kizo"
Juyawa tayi Takoma wurinshi ta tsaya, ya nuna Mata kasa yace "yi knilldown anan"
Cikin muryan kuka tace "Dan Allah Yaya kayi Hakuri wallahi na tuba"
Be Kara magana ba, yafara kokarin zaro Belt, da sauri ta durkusa ta daga hannunta sama, shikuma karasawa yayi ya kwanta a cinyar Ammi cikin muryan shagwab'a yace "Ammi Yunwa wallahi"
Shafa lallausan gashin daya Tara a kanshi tayi sannan tace "yanzu zata gama girkin kayi hakuri kad'an"
Bece komai ba, Ammi ce tad'an tab'a wuyarshi tace "NABIL lfynka kalau kuwa? Naji jikinka da zafi"
A hankali yace "Eh Yunwa ne kawai"
Tace "sannu NABIL yanzu zata gama"_Asalinsu_
Yan garin Maiduguri ne aikine ya kawo mahaifinsu Alh Muhammad Mai lafiya garin Kano, Mahaifiyarsu itama 'yar Borno ce daga karamin hukuma wato Biu acan Mahaifinsu ya aurota, Mahaifiyarsu wato Ammi Asalin Sunanta shine Fatima, sun haifi 'ya'ya uku tare sune Akeela, Nabil, da Noor, Akeela tanada auren anan Kano itama Asalin mijinta d'an Maiduguri ne Amma suna kano da zama, sakamakon aikin Bank da mijin yakeyi, Alh Muhammad Mailafiya babban Dan kasuwa ne Wanda har kwangilar kayeki Yana karba daga kasar waje, sannan yana saro kaya daga waje, yanason yaranshi sosai musamman Nabil dashike shine namiji, Nabil shine namiji Amma har yafi matan kyau domin matan sun biyo Babansu a yanayin fata wato bakake shikuma yabiyo Ammi yazo Fari tass kamar balarabe,
Nabil yagama secondary school d'inshi a Dubai, sannan yanzu yana cigaba da makaranta a Egypt inda yake karantar Doctor, wato (Likitanci)
Noor Kuma yanzu tashiga babban aji a secondary wato Ss1 a wata makarantar kud'i,
Nabil ya kasance Yarone me gata Wanda gatan nashi yasa yafara Raina mutane baya ganin darajan talaka ko kad'an, a ganinshi kud'i sune rayuwa, sannan yasamu d'aurin gindi daga wurin Ammi, saide Abba dukda Yana sonshi hakan besa yadaina fad'a mishi gaskiya ba, Ammi tanada wata kanwarta wacce takeda auren Kanin Gomna na Maiduguri, dunanta Sadiya, Sadiya tanada Yara uku, yammata biyu da namiji d'aya, namijin shine sa'an Nabil sunanshi Ameed, Amma Nabil Yana cemishi Bro, sai kannen Ameed Wanda suka girmi Noor sunansu Nadiya, da Asiya, yaran basaji ko kad'an musamman Nadiya da karatu a Turai ya bud'ewa ido sosai, wayewarsu tayi yawa, suna yawan zuwa hutu gidansu Nabil,
Ameed be kadai za'ace da d'an sauki sauki, Shima ba sosai ba, kyau da kudi da hutu sune suke magana a wurin yammatan dakuma samarin, domin kakarsu ma'ana maman mamansu Shuwa Arab ce, tanada kyau ta wurinta suka biyo, bugu da Kari ga Abba dayake cikakken Bafulatani Wanda Shima yake da hanci sosai saide kawai shi bakine,_wannan kenan_
"Noor ganin tagaji yasa tafara rokanshi tana cewa "Yaya Nabil dan darajan manzon Allah (S A W) ka kyaleni wlh hannuna ya gaji"
Ko kallonta beyi ba, Dan bacci yafara d'aukanshi, Ammi ce tace "Tashi kije gobe kya Kuma"
Tashi tayi tabar d'akin da gudu Dan kada yakara kiranta, a daidai Bakin kitchen taga Inna tana tace Zobo, wurinta ta karaso tace "Inna kiyi hakuri da halin Yaya"
Inna wata tsohuwace Amma Bata tsufa sosai ba, itace take girki agidan Mailafiya, ta iya girki sosai na zamani Dana gargajiya, d'ago kanta tayi tace "'yata Noor ba komai kada kidamu, Ni Raina be b'aci ba, Allah de ya shirya mana yaran zamani"
Noor tace "Ameen"
Sama tahau Nan tashiga dakinta dayake cike da kayan Alatu na rayuwa kamar ba d'akin budurwa ba, Dan wata me aurenma bazata samu kayan dayake d'akin Noor ba, kwanciya tayi akan gadonta ta d'au wani English Book tafara karantawa, gaba d'aya gidan haushi yake bata idan Yaya Nabil Yana gida, bayan ta gaji da karatun tada'au wayarta ta kunna data Nan tafara chatting da classmates d'inta, daganan tafara jin farin ciki a ranta.*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

YOU ARE READING
MUTUNCINA!!!
RomanceA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.