🌸🌸🌸🌸🌸
*MUTUNCINA*
🌸🌸🌸🌸🌸
_Book one free_
Na
Jiddah S Mapi*Chapter 20*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Paid Book*~Da kafa take tafiya yanzu ta ɗanji dama-dama tunda taci abinci, zafin rana da akeyi sosai acikin garin yasa kafafunta suka fara yimata zafi, babu kuɗi a hannunta da zata siya Takalmi tasa, tausayin kanta takeji sosai, tasha wuya kafin ta iso gida, da sallama a bakinta tashiga, ganin Baba akan tabarma da yayunshi da abokanshi sunkai shida da alama tattaunawa suke, dukar da kanta tayi kasa har tashiga ɗalinta, gefen katifa tasamu ta rakuɓe zuciyarta babu daɗi, abubuw a sun taru sunyi mata yawa, "Amal" tajiyo sautin muryan Unty Laila, Saida gabanta yakuma faɗuwa kafin ta amsa, jikinta yana ɓari tafito waje, durkusawa tayi wurinsu sannan tace "Gani"
Unty Suwaiba ce tace "Gobe zamu koma sabida haka mun yanke shawarar za'a zubda cikin dayake jikinki"
Shiru Amal tayi kanta ya kulle, meyasa zasuce ta zubar da cikin?
"Ki shirya gobe da safe doctor zaizo ya zubar, tashi kibamu wuri"
Tashi tayi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, saida ta shiga ɗaki tafara tunani, "to yanzu idan suka zubar da cikin yaya zanyi?" Shine tambayar datake yiwa kanta, da sauri tace "kai wallahi bazan yadda a zubar ba ko ana halin yaya saina raini cikina nima inason ɗana kamar yacce kowace uwa takeson ɗanta, yanke shawara tayi itada zuciyarta daganan taje tayi Alwala tazo tayi sallah, kwanciya tayi domin taɗan samu bacci, saide baccin yaki ɗaukanta saboda tunani daya cika zuciyarta, tunanin halinda Hafeez yake ciki take, wayarta ta ɗauko tafara, yimishi Text kamar haka,
"Nasani nasaka a halin damuwa, tirr da haihuwar yarinya mara Sa'a kamata, wallahi bakai ba harni Amal na tsani kaina, Ka yadda Dani Hafeez Fyaɗe akayimin Amma kowa yaki yadda da maganata, Ni ba mazinaciya bace, kaima kasani, zanyi kokari na cireka a Zuciyata kaima ina rokon haka dukda nasan abin bamai sauki bane amma ya zanyi? Haka Allah ya kaddaramin acikin Rayuwata, Hafeez inaso ka manta cewar ka taɓa sanin wata me suna Amal, nagode da taimakon da kukayimin kaida iyayenka, zan tafi inda bazaku kara ganina ba, cikin jikina zan haifeshi watakila shi ya yadda dani tunda ku kunki yadda da abinda yafaru dani, inayi maka Fatan Alkhairi taka Amal wacce tayi maka tabo acikin zuciyarka ta lalata maka farin cikinka tirr da haihuwan yarinya irina, ka baiwa Mami Hakuri, na Barka lafiya"
Kashe wayar tayi bayan ta tura, gaba ɗaya ta jika gaban wayar da hawaye, cire Sim ɗin tayi tasa a baƙar leda, jakan data tattara kayanta aciki ta ɗauko tasa Sim ɗin a kasan kayanta, saida ta tabbata kowa yayi bacci kafin ta sulale tabar gidan, gudu take a layin burinta tabar unguwar kada ta haɗu da kowa, saida ta tabbata tabar unguwar kafin tasamu waje a kofar wani gida ta zauna tana Haƙi, ruwan datasa a gora ta ɗauko ta kafa a bakinta saida tayi rabi kafin ta saukar tana maida ajiyar zuciya, bayan ta dawo daidai tafara tunanin ina zataje yanzu, jakan ta ɗauko wanda yafi karfinta domin kamar zai kadata kasa takeji, ja tafarayi tana tafiya tana kalle kalle, can ta hango wani Runfar me shayi wanda ya kasance ba kowa a wurin, murmushi tayi domin tasan tasamu wurin kwana, isowa wajen tayi tasamu ɗankwalinta ta shinfiɗa akasa, kanta ta ɗaura akan kayan sannan ta lulluɓa da Hijabinta, bacci ɓarawo shine ya sace Amal a wannan daren, duk yawan sauro dasuke shawagi a wurin bata damuba ita fatanta kawai gari ya wayeBaiwar Allah lafiya?
Wani magidancine yake tambayarta hannunshi rikeda kwalin Lipton da alama shine mai shayin wurin,
Murza ido tayi tana kallonshi da bacci sosai acikin idanuwan nata, yace "lafiya?"
A hankali tamike tana kallon jakarta, tabbas taji daɗi da babu wanda yayi mata sata, "malam dama Ni bakuwace jiya zan koma garinmu Amma sai dare yayi shine na kwana anan"

STAI LEGGENDO
MUTUNCINA!!!
Storie d'amoreA tunaninka Zaka zubarmin da Mutuncina sannan ka zauna lafiya? To kasani idan kabata yarinya Kuma kana tunanin auren Me tarbiya Allah baze tab'a barinka ba idan ka lalata Dole kaima ka auri wacce wani ya lalata.