*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar.©️ *Nana Haleema.*
Wattpad @Nana_haleema
ArewaBooks @nanahaleema11_Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah subahanahu wata'ala da ya bani dama da ikon sake d'aukar alqalami a wannan lokaci, ya Allah yadda ka bani damar fara labarin nan lafiya Allah ka bani ikon gamawa Lafiya. Ya Allah ka bani ikon aikata alkhairi a ciki sa kasa na kaucewa akasin hakan, Allah ka iya min ka dafa min muje karshen sa cikin aminci da kwanciyar hankali, Ameen._
_Wannan labarin na k'irk'ire shi ne banyi da wata ko wani ba, in kin karanta yayi kama da naki ayi hak'uri rashin sani ne._
_Ban yarda wani ko wata su canja min labari zuwa wata siga daban ba tare da izinina ba._
*Book 1*
*Page 1*Babban gida ne mai hawa uku sama da tsakiya da kuma can k'arshe, yana da tsayi sosai dan sai ka mik'a wuya sosai zaka iya hango k'arshen sa, tun daga gate d'in gidan zaka san ba k'aramin gida bane zaka tabbatar da mamallakin gidan ba k'aramin dukiya yake da ita ba, duba da yanayin tsaruwar gidan da kyale-kyalen da aka yi masa kana gani kasan na matashin mai kud'i ne. In ka shiga compound d'in gidan girman sa sai ya baka mamaki dan motoci sama da hamsin zasu yi parking a gidan sabida girman sa ga shuke-shuke na fulayoyi karaye ko ina da haske a tare dasu.
Daga cikin gidan a can sama na biyu a tsaye take a bakin k'ofa tana tunanin ta shiga ko kar ta shiga, gaban ta fad'uwa yake sabida bata san tashin hankalin da zata tarar da cikin ba in ta shiga hakan ya saka firgici ya bayyana a tare da ita sai zare idanu take sabida tsoro da tashin hankali. Iya fad'an da zai mata ma tayar mata da hankali yake yi balle kuma in yayi mata tsawar da take haukata mata tunani.
Dak'yar ta daure a hankali ta tura k'ofar falon ta shiga da sallama ta hange shi a zaune ya d'ora k'afa kan d'aya da sauri tace, "Amma ce tazo, gata can ak'asa tana jiran ka." Banzan kallon da yayi mata sai da hantar cikin ta ta juya ya taso yazo kusa da ita yace, "Munafurcina kika kai mata kice sai yau na dawo ko?." Kai ta girgiza tace, "A'a, kawai tazo ne amma ba muyi waya ba." Kwafa yayi ya sauka zuwa falon ta biyo bayan sa.
Babban falo ne iya ganin ka girman sa na ban mamaki an saka masa kujeru a tsakiya da carpet mai laushi sanyin a.c yana tashi ga kuma t.v na aiki a kunne. Babbar mace ce a zaune akan kujera ta d'ora k'afa kan d'aya tana bin su da kallo shi da ita musamman ma da yake zaune a kusa da ita da kallo fuskar ta babu alamun annuri ko kad'an kana kallon ta kaga b'acin rai a tare da ita.
"Yusuf yaushe ka dawo?." Jin yadda tayi maganar babu wasa ya saka shi yin shiru ya kasa magana hakan ya saka ta sake cewa,
"Yusuf baka ji me nake ce maka bane?." Wanda ta kira da Yusuf ya gyara zaman sa baice komai ba kansa yana k'asa kana kallon sa kasan bashi da gaskiya. Kallon wacce take gefen ta tayi suka had'a ido ta sake kallon wacce take zaune kusa da Yusuf d'in tace, "Ameenatou kika ce min tun kwana uku da ya wuce ya dawo gida, kenan daman k'arya kika yi min da ki kare shi?."
Wacce aka kira da Ameenatou ta shafa kanta ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba kafin tace, "Kiyi hak'uri Amma." Ammata kalli wacce take gefen ta tace, "Yaushe Ameena zatayi hankali ne akan Yusuf? Har ta kai ta kawo tana b'oye min laifin sa dan kawai kar nayi masa fad'a?." Wacce ta kalla batayi magana ba sai sauke ajiyar zuciya da tayi ta sake kallon sa tace, "Yusuf baza ka fad'a min matsalar ka akan rashin dawowar ka k'asar nan ba bayan kasan kana da mata?."
Sai a sannan ya d'ago ya kalli mahaifiyar tasa kafin yace, "Kiyi hak'uri Amma."
"Tambayar ka nayi ba hak'uri nace ka bani ba."
"Babu komai." Amma ta gyara zama tace, "Kenan kawai iskanci ne da rashin mutunci? Ko kuma dan na hana ka auren waccen y'ar macen wacce bata da tarbiyya balle ilimi shiyasa kake wucewa akan Ameena dan kaga tana da hak'uri ko?."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...