*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 11*Da sanyin jiki ta tashi a haka tayi wanka ta gyara gidan kamar kullum ta d'ora ruwan tea kafin almajirin ta mai mata aike yazo ta d'auko kudi ta bashi ya siyo indomie da kwai ta dafa indomie ta soya kwan zuciyar ta na bugawa sosai bata san dalilin hakan ba, gabadaya in ta tuna inda take niyar zuwa sai taji gaban ta ya fad'i.
Tana gamawa tayi wanka dan da wuri take son fita ta shirya tana fitowa falon ta ya shigo ya bita da kallo kamar ba ita ba yace, "Khamshin me nake ji haka?." A sanyaye tace, "Kwai ne, ka zauna" ta fad'a tana nuna masa wajan zama. Bai musa ba ya zauna yana kallon ta yace, "A ina aka samu kwai a gidan nawa?."
Zama itama tayi tace, "Jiya daga asibiti ai na biya gida, shine Yaya ta bani kudi tace na hau mota shine da ragowar na siya." Yayi murmushi yace, "Allah Sarki! An gode sosai." Murmushi itama Fiddausin tayi kafin tace, "Kaci abincin." Kallon abincin yayi indomie d'in tayi kyau sai tiriri take sabida zafi ga kwai a kai sai ya girgiza kai yace, "Bana jin zan iya cin wani abu a yanzu gaskiya, kici kawai."
"Meyasa?." Yadda tayi maganar ya saka shi ya kalle ta yace, "Bana jin yunwa ne."Ledar hannun sa ya mik'a mata ta karb'a tana kallon sa yace, "Atamfar da kike so ce ita na siya miki jiya. Nayi ciniki jiya Alhamdulillah, mai gidan mu yazo yayi mata kyautar dubu ashirin ashirin duk wanda ya tarar a wajan sai na cire kud'in atamfar na siyo miki naga kina so" ya fad'a yana kallon ta da murmushi a kan fuskar sa.
Buɗe ledar tayi ta tab'a atamfar taji jikin ta yayi laushi sosai alamun babbar atamfa ce ba k'arama ba, kallon sa tayi da murmushi tace, "Na gode, tayi kyau ka iya zab'ar kala." Murmushi shima yayi ya matso kusa da ita yace, "Koda zan rasa farin cikina a duniya zan iya jurewa indai zan samar miki da naki farin cikin, burina naga kina farin ciki a koda yaushe bana so naga kina b'ata rai akan komai, zan iya rasa komai sabida ke. Ki cigaba da daurewa akwai ranar da zakiji dad'i dukkan burin ki zai cika, babban gida, babar mota, kayan more rayuwa da komai in sha Allah zan samar miki dashi matuk'ar Ina da rai. Wannan gidan da muke da kanki zaki kyautar sa ga wanda kike zuwa lokacin kin fi k'arfin sa. Sai anyi haƙuri ake cin riba, arzuk'i lokaci ne Fiddausi" ya fad'a yana rik'o hannunta yana kallon idanun ta cikin taushin murya yayi maganar.
Kallon sa take yi zuciyar ta na mugun harbawa domin indai iya kalamai masu kwantar da hankali Ibrahim ya iya su yanzu zai karya maka zuciya ka fasa abinda kayi niya. Shiru tayi tana kallon sa kafin tace, "Ina so zanje gidan Zakiyya d'anta Fahad bashi da lafiya." Numfashi ya sauke ya kalle ta yace, "Sai kin dawo, amma kar ki kai dare" ya fad'a yana tashi tace, "In sha Allah." Kallon ta yayi dan shi mamaki yake yi ganin daga jiya da daddare zuwa safiyar nan ta canja gabad'aya kamar wacce aka yiwa wani abun.
Fita yayi tana jin fitar sa ta sauke numfashi ta kalli abincin itama sai taji yana neman fita daga ranta haka kawai a bayyane tace, "Bazan yi asarar kud'i ba sai naci." Ta fad'a tana jawo abincin ta fara ci sai ta kalli atamfar ta tab'e baki ta cigaba da cin abincin.
Bayan ta kammala ta kwashe kayan ta kai kitchen ta sake gyara wajan, sai sha d'aya da rabi na safe ta kulle gidan kai tsaye gidan Zakiyya ta wuce.
Lokacin da ta shiga mijin Zakiyya yana fita a mota tana tsaye a kusa dashi suna sallama suka gaisa ta shiga ciki, bata jima da zama ba ta shigo tana fad'in, "Hajiya Fidyn Alhaji Bello, wallahi yarinyar nan farin jini gare ki kinga yadda ya tayar min da hankali jiya? Ga Sweet yana nan hankalina ya tashi kar yaji ina waya dashi" ta fad'a tana zama kusa da ita.Fiddausi ta d'aga kai ta kalle ta tace, "Daman ya sanki ne?."
"Ina ya sanni, ai a cikin wannan awannin ya saka anyi bincike a kanki da nima har number ta aka samo masa ya kira ni shifa wallahi da gaske yake ya za'ayi, nace masa to yau mu had'u a nan dan Abban Fahad jirgin sa a America zai sauka yau."
"Zakiyya ni wallahi tsoro nake ji fa."
"Tsoron me? Dalla kar ki bada ni. Tun muna makaranta burin ki auren wanda zai d'auke ki ku tafi America ne, yanzu kuma kin samu shine zaki dinga jin tsoro?."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...