*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 18*
A tare dukkan su suka kalli juna gaban Yusuf yayi mugun fad'uwa ya fara zare idanu ya sunkuyar da kai yana shafa kansa hankalin sa ya tashi sosai, yasan Ameena baza ta ya dake ta ba maganar Ammah ce baya so. Amma ta sake kallo Ameena da ita kanta fuskar ta ta nuna alamun rashin gaskiya tace, "Amina me nake gani a wuyan ki haka? Da gaske duka ne?." Bata iya amsa mata ba dan bata san me zata ce ba Ammah ta sake cewa, "Kalli yadda wuyan ki yayi Ja fa, Yusuf ne ya dake ki?."Yadda gaban Yusuf yake fad'uwa haka ita kanta Ameena din dan bata san abinda zata ce ta kare kanta ba, a tare gaban su yake faduwa shi tsoron kar ta tona masa asiri shine rashin hankalin sa ita kuma rasa abinda zata cewa Ammah shine yake d'aga mata hankali ita kanta Ammah burin ta kar taji ance Yusuf ne yayi dukan. "Kai Meya same ta haka?". Ta fad'a Tana kallon Yusuf ya dago kai ya kalli Ameena kafin yayi murmushi yana tattaro abinda zai fad'a yace, "Mayafi ne, ta nad'a jiya a wuyan ta da tazo cirewa sai taja shi da karfi shine yayi haka."
"Da yake mafayin qusoshi ne a jikin sa?" Ta tambaya tana kallon sa.Kafin yayi magana Ameena tace, "Haka ne Amma, kin San wani lokacin baka yi tsammanin abu ba sai ya faru. Ni kaina ban San wajan yayi ja haka ba zai d'azu dana gani."
Da mamaki Ammah take kallon su duka biyun kafin tace, "amma wannan baiyi kama da abinda kika ce ba da zanen abin duka yayi kama." Murmushi tayi tace, "Amma waye zai dake ni?." Ta kalli Yusuf da yake kallon Amina Ammah tace, "ka fada mata zancen tsayar da ranar bikin naka?." A firgice ya kalli Amma ya kalli Amina da take kallon sa ya sake kallon Amma yace, "Ban sanar da ita ba Amma."
"Meyasa?."
Tashi tsaye yayi yace, "rashin Lafiyar da take fama da ita ya saka ban fad'a mata ba, ban San ta inda zan fara fad'a mata ba shiyasa na bari sai ta samu Lafiya. Ammah ana kira a store Sai na dawo" yana gama fad'a ya fita daga d'akin da sauri.Amma ta kalle ta tace, "An tsayar da lokacin bikin sa sati takwas mai zuwa." Amina ta girgiza kai tace, "Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin Amina. Kar ki saka komai a ranki kar komai y dame ki kinji ko?." Murmushi tayi tace, "To Amma in sha Allah." Humairah da take gefe har lokacin bata ce komai ba tausayin Amina take ji sosai a zuciyar ta tana kuma tabbatar da ba wani mayafi dukan ta kawai aka yi.Kalamai masu dadi Amma ta dinga amfani dasu tana kwantar mata da hankali har sai da taga ta saki jiki suna hıra da Humaira sannan ta basu waje Amina zuciyar ta cike take da tsoro wani b'angren kuma cike take da Jin dadin uwa da ta samu bayan rasa wacce ta haife ta da tayi, badan Amma da take kwantar mata da hankali ba tabbas da zuciyar ta zata iya bugawa ko wanne lokaci.
Tunda ya zauna ya dafe kai baiyi magana ba itama kuma bata ce masa komai ba dan Tunda taga yanayin da ya shigo tasan akwai babban abinda yake damun sa sosai. Musamman da yayi tattaki yazo gidan ta duk da mutum ne mai zumunci amma bai cika zuwa ba sai da dalili. Shirun taji yayi yawa ya saka tace, "İbrahim Lafiya wai?."
Sai sannan ya d'ago ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Ina zan kai damuwar Fiddausi ne?." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "Ikon Allah yau kuma da kanka kake tambayata inda zaka kai damuwar Fiddausi masoyiyar ka?." Kai ya girgiza ya lumshe ido zuciyar sa na bugawa sosai dan Allah ya sani yana son Fiddausi so mai tsanani abubuwan da take masa bai saka son ya ragu da yawa ba, damuwar daren jiya ce ya kasa jurewa sai da ya garzayo gidan Yayar tasa abokiyar shawarar sa ya furta mata abinda yake zuciyar sa ko zai ji dadi.
Ganin ya sake yin shiru ya saka tace, "Me Fiddausi tayi maka?."
"Meye ma bata yi ba?, sam Fiddausi ta canja akwai Wanda yake zuga ta ko kuma aljanu sun shafe ta."
"Ba wata zuga ko aljanu wallahi, ita kad'anta itace aljanar kanta. Tun yaushe nake fad'a maka yarınyar kanta yana rawa nan gaba bazata zauna da kai ba kace min kai ba haka ba?. Tana da hange ne İbrahim Tana kai kanta inda Allah bai kaita ba, gasa take da k'awayen ta wanda suka fita auren masu kudi. Ita kuma gasa duk wanda yace zaiyi wallahi yana tare da wahala."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...