*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 5*Sassanyan dad'i yaji yana shiga ilahirin jikin sa, farin ciki yana mamaye ko wanne gurbi na zuciyar sa kamar ana soka masa allurar farin ciki haka yake ji dan tunda yaji ta amsa yasan shikenan kuma amma bai nuna mata ba ya rausayar da kai ya kalli idanun ta yace, "My choice kar fa na takura ki kiyi abinda ba shi kike so ba, na fad'a miki zan iya hak'ura."
Hawayen da suka sakko mata ta goge tace, "babu takura my Choice ayi hakan kawai, in ta mutu ta dalilin ka kamar ta dalilina ta rasa ranta, ga alk'awarin da ka d'auka gwara kawai ayi a wuce wajan." Tsam tsam ya rungume ta yana jera mata kisses a fuska da bayan ta son da take masa bai tab'a yi masa rana ba sai lokacin yace, "Na gode My Choice, na gode Allah ya biya ki da gidan Aljanna. Ke din mai qaunar cigaban rayuwata ce Allah a barmu tare dani dake har abada."
Ya d'ago ta daga jikin sa yana kallon ta yaga tana murmushi tace, "yaushe zamu samu Ammah da maganar?." Fuskar sa baza ka fassara yanayin sa ba yace, "Sai muje da safe kafin na wuce office. Amma dan Allah my choice ban cutar dake ba?."
"Duk abinda kake so shi nake so koda zai cutar dani" ta fad'a a sanyaye tana kallon sa ya sauke numfashi yana binta da kallo yace, "Duk yadda akayi Allah ya k'addara ita d'in matata ce, kin san k'addara tun tana ciki Allah ya rubuta sunana a matsayin mijinta tun bamu zo duniya ba. In badan haka ba banga dalilin da zai saka na auro wata bayan ke ba, ke kawqi nake so dake kawai naso rayuwa amma k'addarar aure ta kan iya d'aukar rai."
Numfashin itama ta sauke bata ce komai ba yace, "Allah zai baki ladan taimakona da kika yi itama kuma kin taimake ta. Har abada bazan manta da wannan taimakon naki ba My choice, Allah yayi miki albarka ya baki duk abinda kike so." Ta amsa da amin a ciki ya bita da kallo yasan akwai abinda take ji a zuciyar ta amam shi dai tunda ta amsa shine burin sa duk abinda zata ji wannan daga baya ne.
Yace, "Me kike so ki fad'a min ko meye." Sai ta fashe da kuka tace, "Kar ka sake nisa dani, ka cigaba da zama a my choice din dana sani tun a baya. Kar ka koma min Yusuf dan Allah,sam bana jin dad'in hakan ina cutawa sosai. Kar kuma ka aure ta ka wulaƙanta....." Bata k'arasa ba ya toshe mata baki da hannun sa yana girgiza kai yace, "Har abada hakan bazata faru ba My choice, kece farko kece k'arshe babu wata bayan ki. Ina sonki" ya fad'a yana kallon idanin ta itama haka.
Kwanciya sukayi zuciyar sa tamkar audiga sabida haske farin ciki yake ji sosai yana kuma gode Allah da ya bashi mata mai k'aramin wayo kamar Ameena wacce soyayyar sa tayi mata yawa zata ita komai sabida shi, Burin sa kawai gari ya waye dan yasan da anje an samu Amma zancen ya k'are sai dai tayi fad'an ta gama amma zata amince tunda Ameena din ce zata fad'a da kanta.
Bata iya komawa bacci ba shima haka ta b'angaren ta zallar damuwa ce da dana sanin amincewa shi kuma farin ciki yayi masa yawa har taso ta fahimci hakan duk da yana b'oyewa amma taso ganewa dan labarin zuciya a tambayi fuska, yanayin fuskar ta saki sosai sai sun had'a ido sai ta d'an yi murmushi.
Yana fita sallar asuba itama ta d'auki Zaitun ta bar d'akin nasa gabad'aya bata jin dad'in zuciyar ta haka ta koma nata d'akin ta kwanta bayan ta idar da sallah ba tare da tasan abinda yake damun ta, jin zuciyar ta take kamar an d'ora mata dutse sabida nauyin da tayi mata ga zafi da take ji a duk jikin ta. Da ya dawo yaga bata nan d'akin nata ya nufo ya same ta a kwance.
"My choice" ya fad'a yana shigowa ta d'ago ta kalle shi ya k'araso yace, "ya naga kin sakko?." Tace, "Babu komai."
"Akwai my choice, kalli fuskar ki fa duk ta canja alamun Kinyi kuka. Ko maganar jiya ce dai?."Ta girgiza kai tace, "A'a, kawai bana jin dad'i ne shiyasa." Ya sake kallon ta yace, "To me ya same ki haka?."
"Nima ban sani ba."
"My Choice na fad'a miki in akwai damuwa a bar maganar nan farin cikin ki yafi min komai a duniyar nan."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...