*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 21*A mota suna tafiya Fiddausi a gaba kusa da Zakiyya tana tuk'awa Rukayya tana baya tana danna wayar ta abinda yake damun ta daban da abinda yake damun su, Zakiyya tace, "Wato ke Rukky wai d'auka kike mijin da bashi da ko sisi yana da wata daraja ne?." Rukayya ta d'ago ta kalle ta tace, "da Allah ya tashi bayani akan miji ai bai ware mai kudi yace yafi daraja ba ko?."
Fiddausi tayi dariya tace, "Kiyya wannan fa bazata fahimci komai ba sai Allah ya had'a ta aure da irin su İbrahim sannan zata gane me nake nufi." Rukayya bata ce komai ba tayi shiru suka cigaba da tattaunawa ita da Zakiyya kafin Zakiyya ta kuma cewa, "Rukky an ina zan sauke ki ba gida Fiddausi tayi ba." Rukayya tace, "Sauke ni a nan ma kawai na k'arasa."
"A'a mu k'arasa gaba sai ki sauka."
"A'a sauke ni kawai daman Ina so na biya gidan Sajida."
"Okay to, ki gaishe ta" ta fad'a tana samun wajan parking sukayi sallama Ruky ta sauka su kuma suka yi gaba.Fiddausi tace, "Ni wallahi tausayin Rukayya nake ji, Gashi ta jima babu aure sannan ga zuciyar son talaka." Zakiyya tace, "Nima haka wallahi, Ina mata addu'ar samun mijin da zai rik'e ta haka ni kaina bana jin dadi wallahi musamman in Muna tare haka."
"Dukkan mu da aure da yara ita kadai ce babu, ko saurayin ma bata dashi abin sam babu dadi."
"Allah ya kawo mata da gaggawa. Ke muyi abinda yake gaban mu, mu k'arasa gıdana ku had'u a can?.""Mijin ki baya nan?."
"Yana lagos sai gobe zai dawo."
"Muje to." Hanyar gidan Zakiyya suka nufa kai tsaye dan Alhaji yayi mata waya zai shigo bayan magriba.Suna zuwa ba jimawa akayi sallah Fiddausi ta sake wanka tayi sallah Zakiyya ta bata kaya ta saka tayi kyau sai khamshi take a wannan lokacin Alhaji yazo yana jiran ta. A hankali take fitowa yana zaune a kujerar da take kallon inda take fitowa ganin ta fito tana tafiya da rausaya ga khamshin da take yi bai San ya mik'e tsaye ba sai da ta 'karaso yayi murmushi tace, "Barka da zuwa Alhajina, ka zauna mana" ta fad'a tana zama kamar wacce ta bashi Umarni ya zauna yana sake bin t da kallo.
Fiddausi ta had'a dukkan abinda yake so a jikin mace, gata fara, gata mai murjajjen jiki, gata da sura mai kyau. Hakan yana daga cikin abinda ya saka hankalin sa yake tashi, in yana tare da ita dakyar yake iya daidaita kansa a gaban ta dan in badan hakan ba komai zai iya faruwa. Ya kasa daina kallon ta har sai da ta sake yin murmushi tace, "Barka da dare." Lumshe idanun sa yayi ya sauke Ajiyar zuciya Maimakon ya amsa mata sai yace, "Fiddausi ki tausayawa bawan Allah ki san yadda zakayi dani, wallahil azim bana so na rasa ki" ya fad'a kamar zai mata kuka yana kallon ta.
Fiddausi tayi dariya tace, "Waye yace zaka rasa ni?."
"Gashi kina neman saka min hawan jini, kin kasa kashe auren ki nace miki zan biya mijin naki ya sake ki kince A'a, kaina ya kulle ban san ya zan miki ba Fiddausiiiiiii!" Ya 'karasa fada da wani irin salon da ya saka ta jingina da kujera tana kallon sa.Tace, "Bawai nak'i bane kawai dai...." Ya katse ta ta hanyar fad'in, "Kawai me? Dan girman Allah kar ki min haka in ba so kike na rasa raina tun lokacina baiyi ba." Fiddausi tayi shiru bata ce komai ba tana kallon sa hakan ya saka ya sake cewa, "Soyayyar ki tayi min mugun kamu Fiddausi, wallahi waya ake min tafiya zuwa America ta kama ni amma na kasa tafiya sabida bana son tafiya ba tare da magana mai k'arfi tsakanin mu ba."
Fiddausi tace, "Ina bin komai a sannu ne bana son nayi abinda za'a gano nice na kashe auren da kaina, kodan sabida iyayena bana son yin abinda zai jawo musu magana." Ya girgiza kai yace, "Kina da gaskiya, amma ni kuma takura min hakan yake yi wallahi bana iya yin komai gashi ko waya ban cika samun ki ba, inda ina jin muryar ki da sauk'i to sai lokaci zuwa lokaci. hankalina yana neman bari jikina ko aiki bana yi yi gabadaya."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...