*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 15*Tunda ta fito daga d'aki yaga tana cika tana batsewa yasan akwai tashin hankalin da take nema dashi hakan ya saka ya cigaba da kallon tv yayi kamar bai ganta ba dan baya son tashin hankali. Zama tayi a gefen sa tana shan khamshi kamar gimbiya kana tace, "wai yaushe Amir zai dawo ne? Nifa na gaji da zaman gidan nan baya nan." Ko kallo ta baiyi ba yayi mata banza sai daga baya ya juyo ya kalle ta yace, "Bazai dawo ba."
Baki ta tab'e tace, "Kaima kasan wasa kake."
"In nace na barwa Hajiya shi akwai abinda zaki iya ne?."
"Akwai mana domin nice na haife shi dole a bani shi ko kotu ta karb'ar min." Kallon ta yake yi dan ya lura raga mata da yake yi shine ya saka take sake raina masa hankali dan kawai yana hakuri."Ga hanya nan jeki" ya fad'a yana nuna mata k'ofa. Kai ta girgiza tayi k'wafa tana girgiza kanta ta k'arfi so take ta jawo masifar da zai sake ta. Tsaki yaja ya tashi ya fita bai sake kallon inda take ba itama ta mayar masa da martanin tsakin sa. Sarai ya jita baice komai ba ya fita daga gidan gabad'aya.
Da harara tabi hanyar da yabi tace, "Aikin banza, wallahi ko ta wanne hali sai na bar gidan nan ko baya so." Wayar tace tayi k'ara ganin sunan Zakiyya ya saka ta d'auka kafin tayi magana daga can b'angaren tace, "Kee Wai ya ake ciki ne? Har yanzu bai yi sakin ba?." Fiddausi tace, "Gashi nan sai kace dan mayya."
"Kuma kina masa rashin mutunci kuwa? Nasan halin ki fa wani lokacin kina da tsoro."
"Na rasa tsoron wa zanji sai na Ibrahim? Mtswww kema dai wasa kike wallahi. Jiya baki ga yadda yazo a matuk'ar buqace dani ba amma nak'i bashi had'in kai na gaggaya masa magana mai d'aci amma yau ko gezau baiyi ba sai ma wani sabon salon da ya fito dashi."Zakiyya tace, "Ya kamata mu san abin yi domin kuwa wallahi Alhaji ya kagu, bana son mu rasa wannan damar ne Fiddau". Fiddausi tace, "Babu batun rasa dama Kiyya, wallahi sai ya sake ni koda baya so. Kafin nan cikin k'udin nan Ina son a had'a min solar yau a gidan nan."
"Mtsww, Keda kike shirin barin gidan solar uban me za'ayi miki?."
"Ai hakan zai sake tunzura shine, koda na bar gidan ya dandali arzuki shima." Zakiyya tayi dariya tace, "Zan aiko da masu had'a miki da komai da komai nan da anjima kad'an. Amma Ina da shawara." Fiddausi tace, "Ina jin ki."
"Ke kin san yadda yake girmama hajiyan sa, me zai hana baza kije kiyi rashin mutunci a gidan su ba kinga in ta fad'a masa ai dole ya sake ki ko?."Fiddausi tayi shiru tana juya maganar kafin tace, "Hajiyan sa tana da kirki sosai fa Kiyya, bana son sako ta cikin wannan maganar Allah ya sani."
"Ai shikenan sai ki tayi ai, ki bari kirki ya rufe miki ido Alhaji ya sub'uce miki ki shiga uku."
"Bazai sub'uce min ba Kiyya, nasan abinda zanyi kawai ki kyale ni."
"Haka kike cewa amma kin kasa aikata komai sai shegen cika bakin tsiya". Kafin Fiddausi ta kuma magana zakiyya tace, "Alhaji ya takura min yana so ya ganki fa, ya za'ayi ne?."Fiddausi tace, "Hak'uri zaiyi komai ya lafa tukunna."
"Kawai ki kunna datar ki zai kira ki video call ta WhatsApp Tunda yanzu shegen ya fita ko?."
"eh ya fita, amma kar wani ya shigo ya tarar dani fa."
"Dallah malama a gidan ki kike fa, ki tashi kije ki kulle waccan langa-langar k'ofar gidan naki kizo kiyi kwalliya ki saka rigar da ta d'an miki yawa yadda wuyan zai dinga yin k'asa a haka zamu sake kamo wuyan Alhaji."Fiddausi ta tashi waya na Kunen ta ta kulle kofar kamar yadda Zakiyya tace ta dawo har lokacin wayar na kunnen ta kafin tace, "Ke ni bazan saka wata Riga ba zanyi a haka bana son iskanci."
"Banza doluwa kawai, ai ganin wani abu daga cikin surar ki shine zai saka koda ya yi niyar fasawa ya haqura ya jira ki sai kin fito dan shima ya mora. Wallahi Fiddausi kika tsaya wasa wannan girmama yayar taki da ake a gidan ku ke baza'a yi miki ba har abada, in fa kika aure shi wallahi ko meena da muke ganin ta kere mu albarka. Amma kar kiyi nifa Ina cikin daula ke nake ji amma naga kamar bakya so" ta fad'a Tana niyar kashe wayar.
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...