Page 7

56 4 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
              Fitattubiyar

        ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 7*

Ammah suna gama waya ta fita zuwa b'angaren mijinta ta same shi a zaune yana breakfast ta zauna batayi magana ba har ya kammala cin abincin sannan tace, "Matar Yusuf ce tazo min tana neman alfarmar wai na barshi yayi auren tunda yana so, wato dana hana shi sai yaje yasan yadda ya lallab'ota ita da yake bata da wayo sai ta amince tazo ta same ni" ta fad'a tana kallon sa.

Yayi murmushi yana kallon ta yace, "To ai daman tun farko kece kika matsa akan maganar nan banga dalilin da zaki hana shi aure ba tunda Allah ya hore masa babu abinda ya nema ya rasa akan me zaki hana shi tunda yana so?." Ammah ta kalle shi tace, "Haba Abbah, kwata-kwata kwanan sa nawa da auren da yake tunanin wani? In akayi haka ba'a yiwa matar sa adalci ba sam, inda Humaira ce a wannan yanayin ai banza so hakan ba, kafi kowa sanin Ina d'aukar yarinyar nan kamar ni na haife ta."

"To akwai wanda zai ja da ikon Allah ne? In Allah ya rubuta ita wacce yake burin auren matar sace ke da kika matsa sai ya d'auki ranki bayan bakya duniya kuma ayi. Tsananin rabo yana kisa musamman rabo irin na aure nasan kin San da hakan sake tuna miki nake yi, Tabbas bai kyauta mata ba amma ya za'ayi da abinda Allah ya k'addara akwai wanda zai canja ne?."

Ammah tayi shiru bata ce komai ba  tana kallon wani wajan daban yace, "Kuma tunda ya fara maganar nan kika hana shi yake ganin kamar itace ta hana sanin kanki ne baza taji dad'in auren ba gabad'aya domin shi namiji in yana son abu musamman ma k'arin aure idanun sa rufewa yake yi indai baiyi auren nan ba hankalin kowa bazai kwanta ba ciki kuma harda ke. Ki barshi yayi auren hankalin matar ya kwanta namu hankalin ma ya kwanta dan Allah."

Ammah tace, "A jikina nake jin auren nasa ba alkhairi bane." Ya katse ta da fad'in, "Allah yana canja k'addara komai girman ta sai dai in baka addu'a."
"Yarinyar nan da yake so bata da tarbiyya ko kad'an, y'ay'an mata ne basa girmama mahaifin su, kowa ya shaida basu d'auki mahaifin su a bakin komai ba taya zamu bari ta shigo ahlin mu?."

Abbah ace, "Ke ya akayi kika sani?." Ammah tace, "Na saka anyi min bincike a kanta tun farko, mahaifiyar su itace kamar mijin a gidan mahaifin su shine matar. Dan Allah taya zamu d'auko irin wannan yarinyar mu kawota ahlin mu sai ta gurb'ata mana suna?."

Abbah yace, "Duk abinda Allah ya tsara babu wanda zai canja shi, tunda kika ga ana zuwa a dawo akan maganar nan kawai ki kawar da kai daga kai baki san me Allah ya b'oye ba, duk abinda kika ga yana tafiya yana dawowa dakyar in bai faru ba gwara ki saka hak'uri a zuciyar ki. Zan saka ayi binciken da kaina domin tabbatarwa zan kuma saka aje a nema masa auren ta hankalin kowa ya kwanta" ya fad'a yana kallon ta itama tana kallon sa.

Ammah tace, "baka ganin yayi wuri?."
"Baiyi wuri ba, dan Allah ki bar maganar nan haka. Indai da gaske kina son matar sa kamar y'arki to kiso kwanciyar hankalin ta, kina nan tana can baki san me yake mata akan hakan ba tunda ba fad'a miki zata yi ba."
Ammah ta sauke numfashi kawai tayi shiru badan taso ba sai dan babu yarda zatayi ne amma zuciyar ta gabad'aya tak'i karb'ar auren Yusuf koda wasa.

*☆☆*

"Abban Amir ina so zanje asibiti a duba ni yau na tashi bana jin dad'i gabad'aya" ta fad'a tana zaune ba tare da ta kalle shi ba.
Kallon ta yayi ya cigaba da cin abincin sa yace, "A dawo lafiya, Allah ya kara lafiya."

Kallon sa tayi tace, "kud'in mota dana magani." Bai ce komai ba ya gama cin abincin ya tashi ya d'auki dari biyar a aljihun sa ya ajjiye yace, "Gashi nan Kiyi na mota na maganin in kin dawo wanda aka rubuto sai na siyo." Ta kalle shi ta kalli kud'in tace, "Wannan kud'in ai bazai kaini asibiti ba balle kuma ya siya min magani. Kuma ni bafa murtala zan tafi ba ko wani k'aramin asibiti ba, asibitin kud'i zanje can sunfi kula da mutane na daina zuwa k'aramin asibiti. Kawai ka bani dubu biyar na gwada na gani."

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now