*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 3*Yusuf kai tsaye katafaran store d'in sa mai hawa uku da yake kan titin zoo road ya nufa, store ne babba wanda babu abinda ba'a siyarwa, tun daga kan kayan abinci, kayan wuta, kayan sakawa da sauran su. tunda aka hango motar sa aka buɗe gate ya shiga mutane suka zo suka zagaye shi ana kawo gaisuwa ya sallame su ya wuce can k'arshe saman ya shiga office d'insa.
Kulle k'ofar yayi ya k'arasa wajan taga ya d'aga labule yana hango mutanen da suke shige da fice a cikin store d'in duk wanda ka gani ka ganshi da k'atuwar Leda a hannun sa yayi siyayya wasu kuma da karama. ya saki labulen ya zauna a akan kujara maganar Ammah tana sake dawo masa cikin zuciyar sa. "Meena" ya furta a bayyane yana jin jikin sa yana sake yin sanyi sosai tausayin ta yana sake shiga jikin sa musamman in ya tuna alqawarin da ya yiwa mahaifin ta.
Waya ya d'auko a aljihu da niyar kiran ta sai kira ya shigo wayar, sunan My love shine yake yawo akan screen d'in wayar ya furzar da iska kamar bazai d'auka ba sai kuma ya d'auka ya saka a kunne kafin yace, "Zan kira ki." Datse kiran yayi ya kirata ta d'auka kawai sai ta fashe masa da kukan da baya son ji.
Lumshe ido yayi ya buɗe yana jin sautin kukanta har cikin zuciyar sa yace, "Kukan na meye?." Bata daina ba sannan bata bashi amsa ba sai sake k'ara d'aga murya take yi hakan ya saka shi yin shiru yana sauraren ta kusan mintina biyu a haka sannan ta sassauta kukan tace, "My love kana sona kuwa?."
Yadda muryar ta take rawa ya tabbatar masa da kukan gaske take yi kuma daga zuciyar ta yake sai ya sauke numfashi yace, "Ina sonki mana My love, kinfi kowa sanin ina sonki."
"Amma me ya hanaka turowa gidan mu har yanzu? Kasan da cewa su Baba suna niyar yi min auren dole?."
"Wanne irin auren dole kuma My love?" Ya fad'a da mamaki da kuma tsoro."Nidai kawai kazo gida kafin zuciyata ta buga, kai nake so kuma kai nake qauna in suka rabani dakai ban san inda zan saka raina ba. Dan Allah kazo."
"Shinenan my love kwantar da hankalin ki, in akayi sallar la'asar zanzo amma ki daina wannan kukan dan Allah kin san bana so ko?."
"Taya zan daina kuka bayan ana so a raba mu?."
"Babu wanda zai raba mu My love, ni mallakin kine in sha Allah. Ki daina wannan kukan yana tab'a min zuciyata."Asiya tace, "Shikenan my love, na daina sabida kace baka so amma kazo gida anjima." Yusuf yace, "in sha Allah zanzo, kar ki damu."
"Me zan dafa maka?."
"Abinda nafi so" ya fad'a yana murmushi itama tayi murmushin tace, "Tohm sai kazo. Ina sonka."
"Nima ina sonki My love." Murmushi sukayi a tare ya yanke wayar yana sauke numfashi har lokacin murmushin yake yi dan yana matukar jin dadin hira da Asiya.Knocking d'in k'ofar akayi ya bada umarnin shigowa aka shigo kai tsaye inda yake zaune wanda ya shigo yayi ya zauna kusa dashi yace, "Yusuf yane? Na d'auka ma bazaka shigo ba." Yusuf ya kalle shi yace, "Kasan na dawo ne?." Usman yayi murmushi yace, "Nasan ka dawo mana tunda gashi har nazo nan kai tsaye. Gwara da ka dawo ai akwai abubuwa da yawa wanda ake jira kayi approving, akwai wanda suka kawo kaya suna so a karb'a a fara siyarwa cikin shopping store."
Yayi k'aramin tsaki yace, "Dole sai ni? Wai meye amfanin kane Usman?." Shima ya kalle shi yace, "Akwai abinda bani da amfani dole kai ake nema bani ba. Akwai wata mata da tazo min da buk'atar tana son kawo irin kayan zak'i kamar su alawar madara haka da sauran su, amma ban karba ba dan nasan baza'a saka kaya a cikin store babu nafdac ba kuma a yanayin ta kamar bazata iya aikin nafdac ba."
"To yanzu meye amfanin fad'a min?" Ya fad'a yana kallon sa cikin jin haushi."Usman yayi dariya yace, "Sabida gabad'aya Store d'in mallakin kane ba nawa ba, aikina sai Baka nan yanzu kuma kana nana." K'aramin tsaki ya kuma yi ya zubawa waje d'aya idanu alamun tunani Usman da yake kallon sa yace, "Me yake damun ka ne?." Ya kalli Usman d'in yace, "Ammaa fa ta matsa min akan bazan auri Asiya ba Usman, ban san meyasa Ammah bata son na auri Asiya ba."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...