*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 20*Washe gari Ibrahim bai bi ta kan Fiddausi ba fita yayi tun safe kai tsaye gidan su ya nufa duk da suna da nisa amma a k'asa yaje sabida zuciyar sa gabadaya babu dad'i a haka ya kwana ya tashi komai ya tsaya masa baya Jin dad'in komai. Har baya so ayi masa magana sabida abinda yake ji a zuciyar sa baya son bud'e bakin sa. Da sallama ya shiga gidan su ya tarar da Hajiya a zaune a kan kujera a tsakar gida Jin maganar sa ya saka ta dago kai ta amsa tace, "A'a ibrahim kaine yau da safe?." Murmushi yayi ya k'araso ya zauna a kan tabarmar da take kusa da Hajiyan yace, "Barka da safiya Hajiya."
"Barka dai, ka tashi lafiya? ya wajan su Fiddausin?."
"Lafiya lau."
"Baka tafi wajan aikin ba?."
"Bana Jin dad'i sai zuwa anjima." Hajiya ta kalle shi tace, "naga ka fad'a kuwa fuskar ka ta nuna alamun rashin Jin dadi. Amma ka sanar da mai gidan naku baza ka samu damar zuwa ba?."Ibrahim yace, "zan fad'a masa." Hajiya tace, "Ya kamata dai ka fad'a masa." Ya kalli tsakar gidan ganin baiga giftawar kannen sa ba yace, "Ina Fadima da Sadik naji gidan shiru?." Hajiya tace, "Fadima na aike ta gidan ka ta mayar da Amir ya koma gaban Babar sa tayi kara da yawa ai kar ya zama an cutar da ita, shi kuma Sadik ya tafi siyo min gawayi."
Ibrahim yace, "Meyasa aka mayar da Amir din yanzu?." Hajiya tace, "Haba kai kuwa kwanan sa nawa a nan din? Ai gwara a kai mata shi itama ko babu komai in baka nan zata dinga jin mostin sa a kusa da ita." K'arar bude kofar band'aki ya saka ya kalli wajan yaga Mariya ta fito yace, "Ke kuwa zuwa da safe?."
Ta ajjiye butar hannun ta tace, "Kaima kazo balle ni?." Murmushi yayi kawai Hajiya tana ta bin sa da kallo ganin yayi shiru sai tace, "Ko zaka sha kunu? Dazu na dama." Ya daga kai Hajiya ta kalli Mariya tace, "Taimaka ki kawo masa yana madafa a kwanon sha, sai dai yayi sanyi." Mariya ta tashi ta d'auko ta kawo masa had'e d a kofi ya bud'e yana zuba yana sha.
"Salama alaikum" Fadima ta fad'a tana shigowa ita da Amir. A guje Amir yayo wajan Ibrahim yana fad'in, "Abba oyoyo" ya fad'a jikin sa shima ya rik'e shi yana murmushi yace, "Dan gidan Hajiya." Mariya tace, "Ya kuka dawo da Amir din?." Fadima ta zauna tace, "Mun je gidan muna ta bugawa ba'a bud'e ba sai Maman Zainab din nan makociyar ta tace ai ta fita yanzun nan aka d'auka ta a mota."
Daidai lokacin Ibrahim ya kai kofin kunun bakin sa bai san lokacin da kofin ya kusa sub'ucewa ba kunun ya dan zuba a gaban rigar sa ya kalli Fadima kafin yayi magana Mariya tace, "Daman bata gıda da ka fito? Ta fad'a Tana kallon sa.
Dakyar ya daidaita nutsuwar sa yace, "jiya tace min zata je unguwa daman yau, na manta shaf sai yanzu." Zuba masa ido Hajiya tayi Tana kallon sa kafin ta d'auke kai tace, "Anjima da daddare a kawo shi to." Da sauri yace, "A'a Hajiya a kyale shi kawai, yana jin dad'in zama a nan d'in ya koma nan gaba." Hajiya bata tanka ba dan ta hango matsala a zamantakewar auren d'an nata ko a yanayin sa ya gwada haka.
Fadima ya kalla yace, "Bani ruwa da tsumma a goge kunun nan da ya zube min." Ta tashi ta kawo ya goge Amir na kusa dashi ya tashi tsaye ya saka hannu aljihu ya dauko dubu biyu ya ajjiye gaban Hajiya yace, "Hajiya a k'ara a siyi wani abun, na wuce wajan aiki." Hajiya tace, "Kace baka jin dadi kuma."
"Zan lallab'a naje kawai."
"To Allah ya kiyaye, Allah yayi maka albarka ya k'ara arzuki" ya amsa da amin ya fita jiki a sanyaye.Yana fita Mariya tace, "kin tabbatar da abinda nake fada miki ko Hajiya? Yarinyar nan ta jima tana fita bata fad'a masa ba, sau da dama zamu yi magana dashi nace zanje yace tana gıda babu inda zata je in naje naga bata nan, yau gashi a gaban ki kin tabbatar." Hajiya ta kalli Amir da yake gefe sai ta fasa magana ta tashi ta shiga d'aki sai kuwa Amir ya mik'e yabi bayan ta.
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...