17

68 3 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
            Fitattubiyar

  ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 17*

Ameenatu kuwa tana zaune a falon ta k'asa Zaytun na cinyar ta tana wasa ita kuma rik'e take da waya tana dubawa sun gama waya da Yaya kenan tana sanar da ita sun jima da isa gida ita kuma tana saka mata godiya. Falon shiru sai sautin cartoon ake kallo akan tv da yake tashi kad'an-kad'an.

"Ina abincina?." A sama taji maganar hakan ya saka ta zabura ta juya tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta yana tsaye a bayan ta tace, "ban dafa ba sai dai in na dafa maka yanzu." Ido ya wara yace, "Baki dafa ba?." Tace, "Eh, In na dafa baka ci shiyasa ban dafa ba asarar sa ake."
"Ke kika kawo abincin?."
"Bani bace amma nice mai dafawar, in na dafa ya lalace na zubar nice nayi almazazzaranci."

          "Hmmm kin kyauta" ya furta kawai ya bar wajan zai koma sama. Bata tashi ba balle tayi niyar dafawa ta d'auki Zaytu suka hau sama ta shiga d'akin ta dan bazata dafa ba sai dai duk abinda zaiyi yayi ta gaji itama da wulak'ancin da yake mata dan yaga tana yin hak'uri.

Yusuf yana shiga d'aki wayar sa ta fara k'ara ganin sunan My love ya saka shi katse kiran ya samu waje ya zauna sannan ya kira ta tana d'auka tace, "Shine Ina kiran ka baka d'auka ba ko?." Murmushi yayi yace, "na sauka k'asa yanzu na shigo."
"Kodai kana wajan Antyna ne?."
"Mtsww! Ki daina min maganar ta kar ki sake b'ata min rai."

Dad'i ya mamaye zuciyar Asiya ta sake kashe murya tace, "Kayi hakuri my love. Naji muryar ka wani iri baka da Lafiya ne?." Yusuf ya shafa kansa yace, "Yunwa nake ji kuma abincin ki kawai nake so naci" ya kalli agogon hannun da yace, "Gashi dare yayi har takwas ta kusa da nazo naci." Kamar yana gaban ta Asiya tayi farii da ido tace, "Dare baiyi ba my love zan girka maka, me kake so kaci?." Ya girgiza kai yace, "no bana so na wahalar dake."

          "Babu wata wahala my love, zan girka maka yanzu me kake so?." Yayi murmushi yace, "Duk abinda kike so shi nake so, gani nan zan zo but take away zanyi."
"Ba matsala."
"Kinga sai mu tattauna yadda bikin mu zai kasance, ki fad'a min abubuwan da kike so ko?." Tayi dariya tace, "Sai kazo kawai." Shima murmushin yayi ya kashe wayar ya tashi ya d'auki key din mota ya sakko daga saman.

Yana sakkowa falon Ameena na saman ya ganta a tsaye a jikin fridge din falon tana shan ruwa ta saka rigar bacci gajeriya mai kyau sai khamshi take gabad'aya khamshin turaren ta ya cika falon, ga khamshin mai sanyi kana ji kasan night perfume ne. Rigar tabi jikin ta sosai halittar jikin ta ta bayyana komai ya fito rasss tana shan ruwa dan bata San ma ya sakko ba. Ido ya zuba mata kawai yana kallon ta yana jin wani abu na shiga jikin sa hakan ya saka shi kasa d'auke ido daga kanta.

A sannan ta juyo suka had'a ido sai ta d'auke kai kamar bata ganshi ba ta sake bud'e fridge d'in ta d'auki madara a jarka ta wuce shi zuwa d'akin ta. Numfashi ya sauke lokacin da ya daina ganin ta kamar yabi bayan ta sai kuma ya fasa ya sauka ya hau mota ya fita.

          A bangaren Asiya tana sanar da Umma batun girkin nan da nan aka fara had'a masa farar taliya da miyar kwai, nan da nan aka gama tana kwashe miyar tana zubawa a pack na roba irin wanda in anci za'a yar ta shigo tace, "Mayar da miyar nan cikin tukunyar ki zuba wannan rubutun ki ya sake tafasa sai ki kwashe." Karb'a tayi ta kuma yi abinda tace sannan ta kwashe ta shiga dak'i tana shafe jikinta da turaren da Umma Sakina ta bata.

Tana gamawa yayi mata waya gashi ya k'araso ta d'auka ta fita ta hangi motar sa ta k'arasa ta bud'e bayan motar ta saka masa abincin sannan ta shiga gaban motar ta zauna tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta. Turaren ya shak'a ya lumshe ido Allah ya sani turaren ta yana bala'in kashe masa jiki kawai dauriya yake yi duk sanda suke tare.

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now