Page 12

87 8 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
               FitattuBiyar

          ©️ *Nana Haleema.*

*Page 12*

           Jan hannunta tayi ta zauna akan kajure ta kalle ta tace, "Ta dole ai zamu saka ya sake ki ba wani abun ba, yanzu dai kafin wannan yasan da cikin jikin ki?." Fiddausi ta girgiza kai tace, "Bai sani ba kuma bazan fad'a masa ba."
"Yauwa kar kiyi gaggawar fad'a masa, ki buɗe shafin rashin mutunci daga yau kinga yana sakin ki sai mu zubar da cikin shikenan kin gama iddah."

A tare suka tafa cikin zallar nishad'i Fiddausi tace, "haka za'ayi. Amma bana tunanin akwai abinda zan yiwa Ibrahim da zaiyi saurin sakina domin kin san shi yana da haƙuri kamar bashi da zuciya, kome nayi masa wallahi zai iya jurewa. Ki duba wulaƙancin da nayi masa akan had'a shinfid'a dani amma wallahi baiyi fushi ba shine ya sake nemana, kuma atamfar da nake d'aga murya a kai yau ya siyo min."

Tsaki Zakiyya tayi tace, "Indai zaki tuna wannan to wallahi bazaki tab'a samun abinda kike so ba. Ki ajjiye batun haƙuri ko wani abu malama kiyi abinda yake gabaki in kika yi sake wallahi garin neman gira zaki zo ki rasa idanu."
Ajiyar zuciya tayi tace, "Zanyi fa Kiyya ke kin san zanyi, kawai ina jin zuciyata wani iri ne wallahi."
"Yauwa, in kika yi mana asarar Alhaji Bello ai kin cuce mu wallahi. Ayi auren nan a wuce wajan ku wuce Saudia."

Farrr tayi da idanu ta buɗe kudin ta fito dasu tace, "wanda ya bani jiya mafa suna nan Kiyya badan kin bani jaka ba haka zan tafi dasu a hannu, ga wasu wanda suka fi wad'annan yawa ina zan kaisu?." Kiyya tace, "ki kashe."
"Bazan iya ba ai, kinga zan d'auki wani abun dan ina so nayi siyayya a hanya" ta mik'a mata wasu tace, "Ajjiye min wannan sabida tsaro."

Karb'a Zakiyya tayi tace, "Ki saka a account mana."
"Tuni ya jima da zama domant ai account d'in, ina naga kud'in da nake sakawa ba dole su kulle ba?." Zakiyya tayi dariya tace, "Kawo wayar ki na buɗe miki Opay yanzu sai na saka miki na karb'i cash d'in daman Sweet yana nema." Ba musu ta bata wayar ta kalli wayar ta kalle ta taja tsaki tace, "Wallahi yanzu za'a canja wayar nan, kin gama amfani da ita daga Yanzun nan" ta fad'a tana tashi ta fita.

Jim kad'an ta dawo tace, "yauwa yanzu za'a kawo waya ki zab'a ki darje wannan karakani toilet d'in mai aikina zan bawa." Ita dai bata ce komai ba sai akayi sallama aka shigo Zakiyya tace, "Yauwa kawo muga." Ya k'araso yana fadin, "Hajjjaju kamar nasan zan amsa kiran ki yau ban fita kasuwa ba." Karbar wayoyin leda ya bata tana dubawa tace, "Wannan za'a d'auka. Nawa?." Mai wayar yace, "Hajajju IPhone 11 ce. Naira dubu dari biyu da hamsin ce kacal babu tsada."

Zakiyya ta d'auki kud'in ta bashi tace, "Gashi nan, na siya." Karb'ar kud'in yayi ya bata shaidar biya yana fad'in, "Ai wallahi nasan harka dake babu Wa'alaiki a fad'a a cika kenan." Karb'ar shaidar tayi ya tafi Fiddausi tace, "haba Kiyya, waya harta wannan kud'in?." Hararar ta tayi tace, "ta hannuna miliyan d'aya ce da wani abun, yanzu kike cewa baki san me zakiyi da kud'in ba dan an siyi wayar dubu dari biyu wani abun ne?. Mtswww kina bada ni wallahi, kamar ba Fidyn dana sani ba" ta fad'a tana 'bare kwalin wayar.

Tashi tayi ta saka chajin wayar ta dawo suka cigaba da hirar yadda abin zai tafi cikin tsari yadda babu wanda zai kawo suna sa hannu a abun kafin su tashi suyi sallar azhar a d'auki sabuwar waya ana saita ta.

                                    *☆☆☆*

         Tun bayan tafiyar Rukky Ameena take zaune daman zaman su tare da Rukky ne yake d'auke mata wata damuwar amma tunda ta tafi sai take jinta kamar marainiya komai baya yi mata dad'i gidan gabad'aya yana sake fita daga ranta. Tana zaune shiru daga ita sai Zaitun da take wasa a jikinta gabad'aya hankalin ta baya jikinta.

Har ya shigo bata sani ba sai girgiza kafad'arta taji anyi ta kalli wajan da take jin motsin suka had'a ido dashi yace, "Tunanin me kike?." Yanayin fuskar sa sai ya hanata magana domin kuwa a d'aure take kamar yadda ya saba yi mata a kwanakin baya ba kamar yadda ya sake a kwanakin nan ba.

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now