Page 4

111 6 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
                Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 4*

A guje Asiya ta shiga gida tana shiga falon ta fad'a jikin Umma Sakina tana ihun murna da farin ciki, Umma Sakina ta rik'e ta tana dariya tace, "Buk'ata ta fara biya ko?." Asiya ta d'ago daga jikinta tana dariya farin ciki ya cika fuskar ta tace, "Wallahi Umma Sakina bai tab'a nuna min soyayya kamar yau ba, bai tab'a min magana ta hankali wacce zata tabbatar min da gaske zai aure ni ba sai yau. Kinga yadda jikin sa yake rawa da ina kuka? Sai fa da ya sakko daga kan kujera ya tsuguna yana rarrashina. Umma Sakina Allah ya bar mana ke" ta fad'a tana sake rungume ta cikin farin ciki.

Umma Sakina tayi dariya mai sauti ta d'ago ta d'aga jikinta tace, "Ai na fad'a miki abinda yaci da abinda ya shak'a ba abubuwa bane masu sauk'i, zasu ta tasiri a jikin sa har sai yaga ya aure ki hankalin sa zai kwnata. Yau yana nan yana fama da muguwar qaunar ki da kuma sha'awar ki bashi da burin da ya wuce a yanzu yaga ya mallake ki. Shin baiyi yunƙurin tab'a ki ba?."

Asiya tace, "Abinda bai tab'a min ba yau yayi domin har hugging d'ina yayi" ta fad'a tana kulle fuska da hannun ta. Dariya ta sake yi ta dake ta a bayan ta tace, "Kin rikita shi ne, ina tabbatar miki da ko babar tasa ce da gaske bata so ko matar tasa a wannan karon bazai tsallake tarkon mu ba, zai iya barin kowa saboda ya mallake ki. Ai ba iya wannan aikin zamu tsaya ba akwai na karkashin k'asa."

Umma da take ta kallon su tana murmushin farin ciki Asiya ta mik'awa Umma Sakina kudin tace, "kinga abinda ya bani." Ta karb'a ta juya kud'in tace, "Dubu d'ari ce gata nan ko tab'a ta ba'ayi ba. To muna ganin irin wannan arzuk'i taya zamu bari ya kubce mana? Ai wallahi sai mun sark'afo shi ya kasa guduwa ko ina."

Umma tace, "ai wallahi ko k'afar sa bai isa ya d'aga daga gidan nan ba tunda har ya furta ya shiga uku, ko meye zamuyi dan ya auri Asiya bai isa ya gudu muna kallo ba."
"Barshi kawai k'awata. Yanzu kinga wannan kud'in zan d'auki dubu d'aya ta sama data k'asa dan nasan tabbas akwai wacce yatsun sa suka tab'a, to daman haka muke so da ita zamu kuma amfani wajan kamo shi hannu biyu. Dan so muke fa ko ta shiga gidan kar uwar gidan ta rufe ta, ta zama itace gaba uwar gidan na baya, dan yadda muka kasance na gaba a gidan mu haka muke so ta zama itama."

Umma tace, "Gaskiya ne wannan." Umma Sakina ta kalle ta tace, "Ya rage abincin da kika bashi?." Asiya tace, "ya rage yana plate ma."
"To maza jeki ki d'auka ki zaga baya wajan shukar baban ku ki hak'a rami ki binne, ki binne sosai fa kar a tono ta nan kusa. Yadda kika binne ta daidai yake da kin binne zuciyar ki a cikin tasa." Ta amsa da to ta mik'e ta fita cikin zumud'i.

Umma Sakina ta kalli Umma tace, "Ki kwantar da hankalin ki cikin shekarar nan in sha Allah sai mun rage y'an matan nan da suke gaban mu, Asiya sai ta shiga gidan aure ko ta tsiya kota dad'i." Umma tace, "Allah yasa. Burina kenan Sakina ko bacci nayi mafarkin hakan nake."
"Kar ki damu zai tabbata, komai ai yazo k'arshe." Kiran sallar magriba ya saka suka tashi daga hirar da suke yi.

*☆☆☆*

"Assalamu alaikum." Kallon sa tayi ta amsa a ciki ta d'auke kanta ya k'araso ya ajjiye ledar hannun sa yana kallon ta yace, "Fiddausi lafiya kike naga duk kin canja?, akwai abinda ya faru da bana nan ne?" Ya fad'a yana zama yana kallon ta cikin tsantsar kulawa.

Banza tayi masa bata amsa ba ya sake cewa, "Fiddausi magana nake miki fa, meya same ki?." A kufule tace, "Nifa babu abinda ya same ni kawai na gaji da zaman gidan nan ne." Kai ya girgiza kawai baice komai ba daman yayi tunanin hakan zata ce.

Ledar hannun da ya ajjiye ya mik'a mata yace, "Yau nayi ciniki a wajan aiki ga wata atamfa na gani na siyo miki na sanki kina son kala ja" ya fad'a da murmushi yana mik'a mata. Karb'a tayi ta buɗe ledar tana kallon atampar  tare da tab'a cikin ta takalle shi tace, "Kuma nawa kud'in ta?."

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now