Page 13

77 4 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

              ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 13*
      

Yadda ta firgice tana zare idanu shine ya kai hankalin sa ga hannunta da kud'in da suka zube a k'asa sun watse ya bisu da kallo yana kallon ta cikin mamaki mai yawa kafin yaga ta daidaita nutsuwar ta ta sunkuya ta tattara kud'in ta nufi inda kayan ta suke ta buɗe ta saka ta juyo suka had'a ido ta sake d'aure fuska ta wuce ta zauna a gefen gado tace, "Haka kawai a dinga shigowa mutane babu sallama."

Shigowa d'akin yayi jikin sa yayi sanyi zuciyar sa na bugawa a guje tsoro ya gama mamaye jikin sa k'araso yana kallon ta yace, "Fiddausi wannan kud'in masu yawa a na waye?." K'aramin tsaki tayi ta murguda baki tace, "Bafa kud'ina bane kud'in Mama ne ta bani na ajjiye mata, kasan dai ba wannan kudin ne dakai ba balle kace sata na fara yi maka dan bana tunanin ka tab'a rike kud'i kamar su."

Share abinda tace yayi dan so yake yaji yace, "Amma yadda kika firgita hakan ya nuna min kamar baki da gaskiya" idon sa ya kai kan iPhone 11 d'in da take hannun ta a d'azu ya k'arasa wajan wayar zai d'auka tayi zaraf ta d'auka tace, "Wai yaushe ka koma mai bincike ban sani ba?, kawai dan kaga waya baka san ta wacece ba sai ka dauka?. Na fad'a ai tawa ce ko? Zakiyya ce ta aramin nayi amfani da ita."

"Me zakiyi da ita da kika ara? Ke meyasa bakya gudun abun magana ne Fiddausi?."
"Meye abin magana a nan?, naga dai kawata ce kai ka san da hakan ko?."
"Kawar ki ai ba y'ar uwar ki bace ba."
"Kaga Abban Amir dan Allah ka kyale ni kaje ka kwanta ni na gaji bana son magana" ta kalli d'akin taja tsaki tace, "Ni wallahi na gaji da zama a duhu, tun ban shiga kabari ba na saba da zaman duhu wallahi bazai yu ba."

Numfashi ya sauke yana girgiza kai zuciyar sa tana so ta jefa masa alamar tambaya akan Fiddausi domin abubuwan da take yi ya fara k'in amincewa da lamarin taya cize bakin sa ya fita domin kuwa dole yasan abinda zaiyi. Yana fita tayi tsaki tace, "Aikin banza, ko ta tsiya kota arzuk'i sai na bar gidan nan wallahi. Ni a dawo min da d'ana ma hutun ya isa haka na gaji da zaman gidan nan babu shi."

*Washe gari.*

          Tunda Yayar Bauchi ta sanar da Amina ta taso ta daure take dan yi mata abinda zata ci dan zuciyar ta cike take da zumudin ganin yayar tata dan sun jima basu had'u ba tun wani taro da akayi suka had'u basu sake ganin juna ba. Sai a lokacin Yusuf ya sakko ya same ta a tsaye a falon tana magana da masu aikin ta ganin sa suka gaishe shi suka bar falon.

Juyowa tayi ta kalle shi suka had'a ido sai tace, "Barka da safiya." Gira ya d'age duka biyun yana kallon ta kafin ya furzar da iska daga bakin sa yace, "Barka" yana fad'a ya fita daga falon bai sake ko kallon ta ba ta bishi da kallo tayi saurin kawar da abinda yazo ranta ta koma ta cigaba da aikin ta.

Sai azahar Yayar ta ta shigo cikin gidan a lokacin ta gama yi mata komai ta shirya tana zaman jiran zuwan ta. Shigowar ta ya saka Amina tashi a guje ta fad'a jikin ta sai kawai ta fashe da kuka.

Rungume ta tayi itama tana shafa bayanta tana fadin, "Haba Amina yanzu irin tarbar da zan samu daga wajan ki kenan?." D'agowa tayi ta goge idanun ta tace, "Kiyi haƙuri Yayata, Sannu da zuwa, muje sama kiyi wanka ki huta." Hannunta ta riƙe zasu hau saman sai a sannan ta lura da babar yar Yayar tata mai sunan Maman su wacce suke kira da Amira tace, "Amira ai ban ganki ba."

Tayi dariya tace, "Taya zaki ganni Anty Amina kina murnar ganin Mama?." Dariya tayi tace, "Bari kedai kawai, Yaya nake gani kuma Mama nake gani a fuska guda d'aya." Dariya Amira tayi kawai suka hau saman gabad'aya tana jin kewar mahaifiyarta na sake zagawa jikin ta.

Dak'i suka shiga wanda yake kusa dana Amina ta kalli Yayar tace, "Yaya kiyi wanka bara na kawo muku abinci" ta fad'a tana niyar fita. Hannun ta Yaya ta rik'o tace, "Ba wanka ko hutawa ne ya kawo ni ba Amina, nazo ne akan abinda yake damun ki har kikayi wannan ramar." Kallon Yayan tayi jin yadda take magana da rauni tana kallon ta alamun abin na damun ta sai tayi murmushi tace, "Ku fara hutawa tukkuna Yaya, Amira shiga kiyi wanka zaki ji dadi. Ina zuwa" ta fad'a tana fita duk suka bita da kallo ganin yanayin tafiyar tama kana kallo kasan bata da cikakkiyar lafiya.

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now