*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 22*Gaban Ibrahim yayi mugun fad'uwa ya runtse idanun sa zuciyar sa nayi masa zafi da rawa sosai jin abinda Hajiya tace ya bud'e ya sauke numfashin da yake ji ya tsaya masa a k'irji a hankali ya kalli Hajiyar da take kallon sa kafin yayi magana Alhaji yace, "ya zaki yi saurin yanke hukunci haka? Ai sai ki jira muji abinda yake faruwa har aka zo wannan gab'ar."
Hajiya tace, "Baka ji me tazo ta fad'a bane? A gaban idona a gaban ka da y'an uwan sa, tazo har cikin gidan su tace wai ya sake ta bata qaunar sa in ba haka ba zata kashe shi, kuma sai ayi shiru a barshi ya cigaba da zama da ita akan me?. Ai ko a akan wanne dalili ne babu wannan maganar Alhaji."
"B'acin rai ne yaja ta fad'a haka amma in komai ya daidaita sai kiga komai ya wuce, baki San me yayi mata har tazo tace hakan ba, kamata yayi a tsaya a bincika tukunna."
"Zancen komai ya wuce ai bai tashi ba, yarinyar da tazo har gaban mu ta furta wannan kalmar meye zai wuce kuma?. Ai babu abinda zaiyi saura, in ma laifin nasa ne haka zai sake ta tunda abinda take nema din kenan."Alhaji ya kalli ibrahim yace, "Kai me ya kai ka dukan matar ka? Matar taka ma mai ciki?, ga shaida nan kuma Mun gani dan ga fuskar ta nan a kunbure haka ma bakin ta. Haba Ibrahim kamar ba kai ba." Shiru yayi baice komai ba dan bai san me zaice ba dan Fiddausi ta shayar dashi ruwan mamaki gabad'aya bakin sa ya d'aure ya kasa furta komai.
Babban Yayan su wanda suke kira da Yaya Sulaiman yace, "Alhaji ba na shiga maganar ku baku sako ni ba, amma tunda yarinyar nan ta kai ga furta wannan kalaman a gaban ku zama da ita bafa alkhairi bane, macen da zata furta kisa akan sab'ani na miji da mata ai ba wacce za'a saki jiki da ita bace." Wanda yake biye masa wanda suke kira Yaya Yaqub yace, "nima dai hakan zance gaskiya, babu amfanin zama da ita gaskiya abu mai sauki ya sake ta."
Alhaji yayi murmushi yace, "Duk da haka zamu zauna da ita ai ba'a san dalilin da ya saka ta furta hakan ba, zan kira mahaifinta ya kira ta aji a inda matsalar take. Waye yake son rabuwar aure banda dole? Ga d'an su Amir so kuke ya tashi babu mahaifiya a kusa dashi?. Kuma in kuka tuna shida ita babu wanda ya tab'a zuwa yace mana kallon banza wani a cikin su ya yiwa wani, Tunda har aka zo nan sai a tsaya a nutsu kuma a gano inda damuwar take ba a yanke hukunci nan take ba." Hajiya tace, "ni banga amfanin wani magana ba wallahi Alhaji, Tunda sakin take so ba sai ayi ba."
Alhaji bai bata amsa ba ya kalli Ibrahim yace, "Meye ya had'a ku?, baka tab'a kawo k'arar ta ba muna alfahari da hakan nida mahaifiyar ka, mahaifin ta ma yana alfahari da kai dan yana fad'a min in muka had'u. Yau ka kawo k'arar ta na tabbata ba Abu bane mai sauki sai wanda yafi k'arfin tunanin ka, kafin kayi magana itama tazo kaga kenan matsalar ba k'arama bace, Meya had'a ku?." Numfashi ya fesar ya sunkuyar da kansa k'asa yace, "Alhaji in rabuwar ce alkhairi gwara kawai mu rabun." Hajiya tayi karaf tace, "Tunda kaji ya furta hakan gwara kawai a san abinda za'a yi gaskiya, bana goyan bayan ace wai za'a daidaita su Allah ya sani."
Alhaji ya mik'e tsaye yace, "zan kira iyayen ta yanzu in yaso sai a had'a su da Ibrahim din aji abinda yake faruwa, ai ba'a shari'ar aure b'angare d'aya, ku kwantar da hankalin ku in sha Allah babu wata damuwa. Kai Ibrahim muje" ya fad'a yana fita duk mazan suka bi bayan mahaifin nasu.
Bayan fitar su Yaya ta kalli Hajiya tace, "Wallahi Hajiya ba k'aramar wahalar Fiddausi yake sha ba, kawai yana sonta ne kuma Allah ya d'ora masa hak'uri da zurfin ciki shiyasa baya fad'a, kin san Mariya ce k'awar shawarar sa yaje har gida da matsalar Fiddausi shekaran jiya, kowa a unguwar yasan ta canja daga wacce aka sani a baya."
Hajiya tace, "ki ture duk abubuwan da take masa a bayan idanun mu ne ya faru, amma wannan har gabana tazo tace bana son sa bana qaunar sa, yanzu ko daidaita auren nasu akayi har abada zan ga farin tane?." Hajiya ta girgiza kai tace, "Har abada bazan ga farin ta ba wallahi, ta fita daga raina gabad'aya in sha Allah kuma k'arshen auren nasu ne yazo dan ni kalamam ta sun bani tsoro."
"In sha Allah auren ya kare, babu amfanin zama da mace irin ta."
"To koma meye har gıda Kizo gaban iyayen mutum kice bakya son sa?." Yaya Hadiza tayi shiru kawai dan taga alama kalaman t sun yiwa Hajiya zafi sosai.
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...