Page 8

51 5 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
                Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 8*

        Kallon ta Fiddausi take da mamakin abinda tace kafin ta girgiza kai cikin sanyin jiki  tace, "Na zubar fa kika ce Kiyya?." Ta wara hannayen ta tace, "To meye amfanin sa?, na gida ma ya aka cika dashi da za'a fara k'ok'arin samun wani?. Ni wallahi na raina wayon ki ma ban d'auka zaki sake bari kiyi ciki a wannan gidan da kike ciki mai kama da kejin kaji. Kinga Kefa nake yiwa gata ba kaina ba."

Fiddausi tace, "Koma dai meye bana tunanin zan fitar da cikin nan."
"Akan me? In fa kin zubar bai sani ba."
"Yayi zaman chemist a da yasan maganin masu ciki yana gani zai gane, ni bazan iya ba."
"Ai sai ki ta zama dashi har Alhaji Bello ya gano matar aure ce ke ya rabu dake y'an kudaden da nake miki hangen zaki samu ki rasa."

"Nifa daman bance zan saurare shi ba, ina fa da aure Zakiyya."
"To wannan auren naki ai dashi gwara babu, aure babu jin dad'in rayuwa kullum kina zaune cikin duhu kina fama da gawayi wani lokacin nama ma gararar ki yake yi meye amfanin sa?. Ki duba gidan nan ki kuma duba gidan Ameena, ko Ruky da bata yi aure ba gwara ita a kanki sabida ita tun da iyayen ta kin san ya suke. Dukkan mu k'awaye nehar mukayi candy ko wacce tana cikin daula kece kawai kike zaune da matsiyaci duk da nasan rabon Amir ne ya saka aka kai yanzu."

Fiddausi tace, "Kin manta Rukayya gwara ni da auren ita kuma ai babu." Zakiyya tayi dariya tace, "To banda abin ki Fid ba gwara ma Rukky tasan bata da auren ba a kanki? Bata da aure kuma babu abinda ta rasa. Kefa gabad'aya kece kika k'askanta a cikin mu ni kuma bana son ganin hakan Allah ya sani. Dakyaun ki, da saurar ki ace kina zaune a gidan da dubu goma zata gagare ki."

"Bari kawai, kudin ma fa da naje nayi burga dasu Meena ce taje gidan ta bani tace na Amir ne in badan su ba da yanzu ina murtala ina kan layin ganin likita."

Zakiyya tace, "A haka kuma kike cewa zaki kuma haihuwa dashi." Fiddausi ta kalle ta tace, "Bazan yi saurin yanke hukunci ba sai naga abinda hali yayi. Yunwa nake ji fa." Zakiyya tace, "Kedai kika sani kece a gidan bani ba" ta fad'a tana kwalawa mai aikinta kira ta bada umarnin a kawowa Fiddausi abinci nan da nan aka cika mata kan table da abinci ta fara ci.

       Ta jima a gidan Zakiyya sai bayan azahar ta tafi kai tsaye gidan su ta nufa da niyar gaida mahaifiyarta.
Y'an gidan su mata duk suna nan k'annen ta da kuma yayen ta ta shiga cikin falon Maman su tana fad'in, "Yau babban taro ake shine ko a sanar dani?."

D'aya daga cikin su ta kalle ta tace, "Kaga matar Ibrahim irin wannan kyau haka kamar ba ke ba, lallai Ibrahim ya tsaya miki kina abinda kike so. Fiddausi ta karaso ta zauna jin ta take wani iri kamar magana suke fad'a mata.

Maman su da take zaune tana shan rake irin wanda aka yanka k'anana tace, "Ai sai dai ku fi Fiddausi manyan gida da motoci amma zaman lafiya da biyan buk'ata baza ku fita ba. Mijin ta yana k'ok'ari da ita sosai duk da bashi da k'arfi amma burin sa ya samu abinda zai kyautata mata shiyasa kullum kya ganta fess kamar Hajiya."

Duk sukayi dariya wata a cikin su ta kuma cewa, "Ai haka shine fata daman ba ka auri mai kudin ba kaje can kasha wahala, ita kam ai ta dace sosai, Allah ya cigaba da baku zaman lafiya." A tare suka amsa babbar su ta kuma cewa, "Kwanciyar hankali yafi zama a cikin daula wallahi. Allah ya k'ara muku zaman lafiya k'anwata ya kawo mana kani ko k'anwar Amir."

Yak'e tayi ta zauna tana fad'in, "Ni ko gaisawa bamuyi ba ana ta magana." Gaisawa sukayi gabad'ayan su kafin Maman su tace, "Daga ina haka da rana?."
"Naje asibiti ne sai na biya gidan Zakiyya."

"Too ko dai an samu k'anin Amir?" Yayar ta ta fad'a tana kallon ta. Fiddausi tayi dariya tace, "Wanne ciki ana zaune lafiya? Ciwon kaine sai suka ce jini na ne yayi k'asa na dinga shan ruwa sosai." A tare suka had'a baki sukayi mata sannu kafin Mama tace, "Har yanzu Amir d'in yana gidan kakar sa kenan?." Ta d'aga kai tace, "yana can, amma nasan dak'yar in bai dawo dashi yau ba" ta kalli y'an uwan nata tace,

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now