*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 9*Tunda Fiddausi ta koma gida ta shiga d'aki bata fito ba tana jin motsin dawowar Ibrahim tayi burus kamar bata ji ba tana zaune tana tunanin maganar Zakiyya da kuma maganar y'an uwan ta akan abinda yake cikin ta, tabbas ya zama dole ta d'auki mataki kafin wankin hula ya kaita dare, bazata bar cikin ba gwara kawai ta zubar tun lokaci bai k'ure mata ba.
Tasan sai yaje yayi sallah ya dawo sannan zai shigo tana zaune aka kawo wutar nepa haske ya gauraye d'akin gabad'aya, tayi ajiyar zuciya ta tashi tayi itama tayi sallar tana nan zaune tana sak'awa da kwacewa har ya shigo d'akin da sallama.
Da kallo ya bita ya zauna kafin yace, "Ya jikin naki? Na kira ki naji yanayin ki baki d'auka ba kuma baki kira ni ba. Me suka ce a asibitin?." Ta kalle shi tace, "ka bani kud'in katin ne?." Kawar da maganar yayi bai tanka ba kafin yace, "Yanzu dai me yake damun ki?."
"Jinina ne yayi k'asa sunce na dinga shan ruwa sannan inda hali a dinga siyo min hanta kullum ina ci."
"Subahanallah, abun har ya kai haka kenan?."
"Uhum!" Ta bashi amsa a tak'aice ba tare da ta kalle shi ba dan wani irin k'unci take ji a zuciyar ta in ta Tuna tana da ciki."Bara na fita na samo miki hantar kici sai ki kwanta" ya fad'a yana tashi ya fita ta bishi da kallo ta tab'e baki tare da jan k'aramin tsaki. Tana ji ya buɗe kofa ya fita tace, "Dole ne na rabu da wannan cikin tun kafin ya farga, maganar Zakiyya gaskiya ce ya akaji dana gidan ma balle a samu wani? Ai komai sai ya sake lalacewa."
Wayar ta taji tana k'ara ta jawo tana kalla taga bak'uwar lamba bata kawo komai a ranta ba ta d'auka ta saka a kunne, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki kyakykyawar sura fara mai farar aniya, ina fatan gimbiya Fidy ta koma gida lfiya?."
Gaban ta yayi mugun fad'uwa ta wara idanu waje jin muryar mutumin da batayi tunani ba ta had'd'iye yawu ta kasa magana tayi shiru kirjin ta na bugawa cikin tsoron da ya bayyana a kan fuskar ta. "Gimbiyata kinyi shiru, baki gane mai magana bane?."Muryar ta rawa take yi ta kasa furta komai yayi murmushi yace, "Kar ki damu na samu komai a labarin ki, kina da aure kina kuma da yaron mu Amir. Gidan wacce muka je d'azu gidan k'awar kine Zakiyya wacce kuka taso har kuka yi makaranta tare da ita, haka ne abinda nace?."
Wara ido waje tayi kamar yana gabanta murya na rawa tace, "kasan ina da aure meyasa ka kira ni?."
"Sabida ina sonki tsakani da Allah badan wani abun ba, ina so na aure ki ne in kin amince. Ban kira ki da niyar b'ata miki aure ba, ga gaske auren ki zanyi."
"Kamar ya ka aure ni bayan yanzu kake shaida min kasan ina da aure?."Ya sake yin murmushi yace, "Gidan da kike Fiddausi bai dace dake ba, matar manyan mutane ce ke sam baki cancanci zama da wannan mijin naki da kuke tare ba. Ke matar manya ce kowa ya kalle ki a kallon farko zai gane hakan, matar irin mu ce ke kawai ki bani dama." Fiddausi tace, "me kake nufi?."
"Kinga maganar waya bazata yu ba, yaushe zamu had'u?. Bani nufin cutar dake ko d'aya, ni auren ki nake so nayi."Shiru tayi bata amsa ba ya sake cewa, "Taya kike tunanin zaki zauna a irin gidan da kike zaune Fidy? Ke kalar hawa manyan motoci ce da hawa jirgi ki bar k'asar meyasa kike zaune da wanda ba ajin ki ba?. Kalli k'awar ki Zakiyya mana bakya sha'awar irin tata rayuwar?. Ina tabbatar miki da matukar na aure ki rayuwar ki zata ninka ta ta rayuwar sau babu adadi." Shiru tayi bata amsa ba tana shawarwarin ta kashe ko kuma ta cigaba da jin abinda yake cewa kafin ya kuma cewa, "A shirye nake da na aure ki in kika kashe auren ki, baki da wata fargaba domin Allah yasa min sonki lokaci d'aya ba tare dana shiryawa hakan ba. Yaushe zamu had'u mu tattauna?."
Fiddausi duk tsoro ya cika mata zuciya ga tsoron kar Ibrahim ya dawo tace, "ni bazan iya had'uwa dakai ba, kayi haƙuri." Jin zata kashe wayar yayi saurin dakatar da ita yace, "Kar ki kashe dan Allah, ki taimake ni ki kuma taimaki kanki ki amince mu had'u, wallahi ni ba irin wanda kike tunani bane da zuciya d'aya nazo wajan ki. Ki amince gobe mu had'u a gidan k'awar ki domin mu samarwa da kanmu mafita. Da gaske nake ina sonki kuma wallahi auren ki zanyi."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...