16

79 4 0
                                    

*MAI ƊAKI...!*
            Fitattubiyar

   ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 16*


          Hankalin Rukayya duk ya tashi bata tab'a ganin mata da miji suna fad'a gaban ta ba jikin ta har rawa yake yi hankalin ta ya kai k'arshe wajan tashi sai bin su take da kallo tana dana sanin ma zuwa gidan , a zabure tabi bayan Fiddausi zuwa d'aki ta same ta a tsaye tana mita cikin masifa kamar a gaban sa take.
"Haba Fiddausi!, Haba Fiddausi, mijin ki kike yiwa wannan rashin kunyar har haka? Kuma ko kunya bakya ji a gaban idanuna?."

Fiddausi ta kalle ta tace, "Ke din bak'uwa ta ce? Ko kuma akwai abinda zan b'oye miki ne?. Kinga na gaji da zama da mutumin nan wallahi saki na nake so yayi ko yana so ko baya so, zaman shekara biyar d'in da nayi dashi Allah ya amfana nayi k'okari iyakar iyawata, tura takai bango a wannan lokacin bazan iya ba wallahi." Rukayya mamakin ta kawai take dan bata san rashin hankalin Fiddausi har ya kai haka ba tace, "Wai kina cikin hankalin ki kuwa? Kin samu miji mai sonki da qaunar ki da burin kyautata miki shine kike neman yiwa kanki salalan tsiya?, ne ya shiga kanki ne? Ina ilimin addinin da na sanki dashi?. Kowa a unguwa kwatance yake da mijin ki yana fatan y'arsa ta samu kamar sa amma shine kike fad'ar haka?."

Fiddausi tace, "kee har ilimi in talauci yayi yawa fecewa yake, ki adana wa'azin ki wallahi bazan raga masa ba daman kiris nake jira, bai isa yayi min na kyale ba, solar kuma dole na saka tunda kudina ne."
"A Ina kika samu kudin ke?."
"Wannan kuma sırrı ne bai dame ku ba, Kun San dai ba sata zanyi ba." Girgiza kai Rukayya tayi tace, "Wallahi kin bani mamaki, kin bani kunya, ban tab'a zaton hakan daga gare ki ba. Mijin ki na aure, mijin ki na sunna kike yiwa wannan tijarar a gaban idon b'akuwar ki kuma hakan bai dame ki ba. Mijin ki uban d'anki wanda kika haifa Keda shi kike yiwa wannan wulaqancin kawai sabida wani abun ya rufe miki ido. Kiyi gaggawar neman yafiyar sa in ba haka ba zaki kuskuren da baki tab'a yi ba a rayuwar ki."

Dariya Fiddausi tayi ta tafa tace, "Ai kuskuren nake so nayi Rukayya, indai wannan fak'irin zan bawa hakuri kice za'a tashi kiyama kenan, kuma wallahi bai isa ya hanani abinda nayi niya ba Tunda shi bashi da kud'in da zaiyi min. D'ana kuma dole a dawo min dashi gabana na gaji da zaman gidan nan baya kusa dani." Rukayya da take kallon ta  mamaki sai ya hana ta sake cewa komai sai kallo kawai kafin ta bud'e baki tace, "in ma wani yake zuga ki, in ma aljanu ne a akanki Ina baki shawarar kiyi gaggawar neman mafita dan zasu kai ki su baro kine, suna so ki aikata kuskuren da har abada baza ki goge shi ba. Mijin ki ba talaka bane domin ya tsare miki dukkan haqiin ki da yake wuyan sa, ke kinfi matar wani mai kudin Kyan gani sabida kulawar da yake baki. Talaka shine wanda bashi da cin yau bare na gobe ke kuwa kin fin k'arfin abinci" ta sassauta murya kana ta cigaba da cewa,

"Kin samu miji Allah ya rufa miki asiri meyasa kike son tonawa kanki asiri kina d'aga murya maqota suna jinki? Mu da bamu da mijin nema muke meyasa kike wulaqanta naki Fiddausi?. Ina ilimin da ake baki kyauta a kansa lokacin da Muna islamiyya? Ina duk suka tafi?, ya akayi kika bari shaid......" saurin dakatar da Rukayya tayi tace, "Ke bani da wani aljan ko shad'ai ko zuwan bil adama kamar ni da zaiyi tasiri a kaina, duk wannan soki burutsun da kike ba tasiri zaiyi a kaina ba. Zancen miji da nake dashi baki dashi me zai hana bazaki auri ibrahim d'in ba? Daman ai naga ke talaka kike nema ko? To Gashi kin samu ki aura ki shigo ki zauna ni kuma na fita domin banga abin kishi a wajan sa ba. Ke ko ina gidan nan ma ki shigo, banga abinda zanyi kishi a wajan sa balle ni ficewa zanyi wallahi bazan zauna ba."

Mamaki ya saka Rukayya ta kasa magana sai kawai ta fara hawaye ta toshe bakin ta tana girgiza kai dan bata d'auka son duniyar Fiddausi ya kai haka ba tace, "kiji tsoron Allah Fiddausi, kiyi ta'awizi ki kori shaid'an in ba haka ba wallahi yana gab da komawa gefe yayi miki dariya. Shawara nake baki matsayina na k'awar ki mai son cigaban ki, wallahi Fiddausi ki tuba kije ki bawa mijin ki hak'uri."
"Wallahi baza ni ba, ina kuma tabbatar miki da baza ki sake dawowa ki tarar dani a gidan nan ba sai dai wani amma ba nan ba, ke ki aure shi kinga kin samu abinda kike so."
"Allah yana kallon ki duk abinda kike yi Fiddausi" abinda ta iya fad'a kenan ta juya ta fita daga d'akin da sauri.   A zaune taga Ibrahim yayi tagumi fuskar sa ta nuna alamun b'acin rai da alama duk yaji abinda suka tattauna bata iya yi masa magana ba ta fita a guje tana kuka zuciyar ta na sake tabbatar mata tabbas akwai abinda yake damun Fiddausi.

MAI ƊAKI...!Where stories live. Discover now