*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 10Da ciwon kai ta farka mai zafi hakan ya saka tunda tayi wanka take zaune Zaitun tana ta wasan ta ta d'auko wannan ta d'aiko wancan yana ta magana ita kad'ai, ko gyaran d'akin ta kasa sabida yadda take jin kanta na ciwo sosai kamar zai rabe biyu. Buɗe k'ofar d'akin taji anyi hakan ya saka ta juyo ta kalle shi ya k'araso yana kallon ta tare da fad'in, "My choice lafiya kike?" Ya fad'a yana tab'a wuyan ta yaji zafi ya kalle ta ya kuma cewa, "Jikin ki akwai zafi my choice, me yake damun ki haka?."
"Kaina ne yake min ciwo" ta furta a sanyaye hannunta dafe da kanta.
"Tun yaushe kan yake ciwo?."
"Safe" ta bashi amsa a tak'aice tana sake dafe kanta.
"Kin sha magani kuma?."Zatayi magana wayar sa ta fara k'ara ya juya screen d'in my love ya bayyana a jiki ya kalle ta yaga ta gani sai ya danna power d'in wayar screen d'in ya d'auke ya basar kamar bashi ba yace, "Bara na kawo miki magani kisha bakya zauna da ciwo ba" ya fad'a yana tashi ya k'arasa inda drawer take ya d'auko magani ya buɗe k'aramin fridge d'in d'akin ya d'auko ruwa ya kawo mata.
Karb'ar tablet din tayi ta damke a hannunta amma bata sha ba ya kalle ta yace, "Kisha mana." Shiru tayi bata ce komai ba sannan bata sha ba ya sauke numfashi ya tsuguna a gabanta yace, "Tun farko na fad'a miki in maganar nan zata haifar miki da damuwa a barshi amma kika k'i gashi yanzu hakan yana jawo miki matsala."
Ruwan da ya bata tasha amma bata ce komai ba ta kalle shi sai tayi murmushin takaici ta cize bakin ta ganin hakan sai yasha jinin jikin sa dan ya kasa fahimtar me murmushi yake nufi ya kuma tabbatar da wata manufa tayi ya kalli agogon hannun sa yace, "Kisha maganin mana my choice."
"Basai nasha ba." Mik'ewa tsaye yayi yana kallon agogo yace, "Ana jirana an office ina da bak'i na gaggawa, Kisha magani pls" ya fad'a yana dafa kanta kafin ya d'auke hannun sa ya fit.Da kallo ta bishi har ya b'ace ta sauke numfashi ta koma da baya ta kwanta tana jan numfashi kanta na harbawa sosai kirjin ta na duka kamar ana buga ganga. Hawaye taji suna sakko mata daga idanunta tuna sunan da ta gani akan wayar sa yana yawo ta lumshe ido zuciyarta na cigaba da bugawa kamar zata fito, zuciyar ta n sake tabbatar mata da wautar da ta aikata na goyan bayan auren sa.
Damuwa tayi mata yawa dalilin da ya haifar da ciwon kan kenan zuciyar ta zafi take sosai ji take kamar zata fashe, ta tabbata aka auna bp din ta ya hau a lokacin sabida damuwar ba k'arama bace. Tashi tayi zaune ta saka maganin a baki ta d'auki ruwan tasha ta koma ta kwanta tana jan numfashin ta zuciyar na nayi mata d'aci.
Rufe ido tayi abubuwan da suka faru suna dawowa mata cikin kanta, tarin soyayyar da yake nuna mata tana cigaba da bayyana a idanunta kamar a lokacin da hakan yake faruwa. A hankali ciwon kan yake sauka tana jin dad'in kan har lokacin idanunta yana kulle amma yadda jijiyoyin kan suke harbawa yana raguwa sosai.
"Meena lafiya kike dai?." Jin muryar wacce batayi zato ba ya saka ta buɗe ido ta kalli bakin k'ofar ganin Rukky ya saka ta tashi zaune ita kuma tayi saurin k'arasowa ta rik'e ta tana fad'in, "Meena yadai?." A kafad'arta ta kwantar da kanta kawai sai ta fashe da kuka mai ciwo dan bata da wanda zata kwanta a kafadar sa tayi kika a kusa da ita.
Hankalin Rukky ya tashi jin yadda jikinta yayi zafi sosai tace, "Subahanallah! Meena jikin ki yayi zafi sosai, kodai muje asibiti?." Kai take girgiza mata alamun a'a tayi shiru tana sauraron kukan nata tana ta bata hakuri kafin ta sassauta kukan ta mik'e tana goge idanunta.
Rukky tace, "Meena me yake damun ki haka?." Kai ta girgiza kafin ta kalli Rukky taga itama fuskar ta tayi ja ga alamun damuwa ya bayyana a tare da ita tace, "Rukky lafiya kike?."
"Ke zaki fara fad'a min abinda yake damun ki Meena, kin rame sosai fa sai haske da kika sake yi. Ko dai ciki ne dake?."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...