*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 14*Ta jima tana bacci, sallar asuba ma dakyar ta iya tashi tayi Tunda ta koma ta kwanta take bacci sosai, sai da rana ta fito ta farka tunawa dasu Yaya suna nan ta tashi da sauri ta shiga band'aki ta wanke bakin ta ko wanka batayi ba ta fito zuwa d'akin dasu yayan suke.
Da sallama ta shiga Yaya ta amsa tana zuba kaya a jaka ta juyo tana kallon ta itama ita take kallo kafin ta dauke Kai tace, "Yaya barka da Safiya." Kallon ta tayi tare da yin murmushi tace, "Barka dai! Maza d'auki Zaytun sai kuka take tun d'azu." Ba musu ta d'auke ta ta d'ora a cinyar ta ta fara shayar da ita.
"Ina kwana Anty Amina?" Amira ta fad'a tana kallon ta ta amsa tana fad'in, "Amira amma dai kin had'a muku breakfast ko?". Tayi dariya tace, "Tun yaushe ma, Taya Mama zata kai yanzu bata karya ba kin San ai bazai yu ba."Amina tayi dariya tace, "Wallahi bacci nayi ne sosai shiyasa." Yaya tace, "To Ameena mufa Mun shirya tsaf daga nan zamu dan zaga dangi zamu wuce Bauchi." Da mamaki Ameena tace, "Kai Yaya wai tafiya zakuyi?".
"Ga zahiri Amina" ta fada tana zuge zip d'in k'aramar jakar. Amina ta marairaice fuska tace, "Amma Yaya baki fada min ba, na d'auka sai gobe wallahi zaku tafi. Dan Allah ku bari sai gobe sai ku tafi bana so ku tafi yau wallahi" ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon su."A'a wallahi bazamu Kai gobe ba, ke kin san da yadda na iya kwana a gidan nan naki kuwa? Matsayin uwa nake a wajan ki kuma nazo gidan y'ata na kwana, baki ji yadda nake jin nauyi ba kamar an daure ni wallahi. Yau zan tafi minti talatin bazan k'ara a gidan nan ba." Hawaye suka sakko daga idanun Ameena ta janye Zaitun daga jikin ta ta kalli Yayan tace, "Matsayin uwa kike a wajena Yaya shiyasa nayi tunanin zaki zauna dani na kwana biyu kodan zuciyata tayi sanyi, in kika barni a nan ciwo zai iya kamani. Zaman ki daga jiya zuwa yau kina ganin bacci nayi mai nauyi Yaya, Yaya zaman ki a gidan nan kamar magani ne a wajena wallahi, bana so Kiyi nisa dani."
Jikin Yaya yayi sanyi amma bata nuna mata ba sabida kar hankalin Ameena din ya tashi ta zauna a gefen ta tace, "Hakuri zakiyi Ameena, zamana a nan bazai canja abinda Allah ya riga ya rubuta ba. Kiyi hak'uri ki daure komai zai wuce kamar bai faru ba, in kika rik'e abubuwan dana fad'a miki tabbas baza kiyi dana sani ba." Ido Ameena ta goge ta kalli Amira tace, "Daughter ki taya ni bawa Yaya hak'uri dan Allah ta bari sai gobe."
Amira ta kalli Yaya bata ce komai ba ita tace, "Bazan zauna bafa Ameena, tafiya zamuyi ko meye zai faru ma yi magana a waya."
"To ki bar min Amira dan Allah."
"Bana yanke hukunci mahaifinta bai sani ba, ki bari mu koma sai na tambayar miki shi in ya barta sai ta dawo tayi miki wata guda ta koma tunda bata fara makaranta ba yanzu."Ameena ta girgiza kai jikin ta duk ya mutu ta sake goge idanun ta, zuwan Yayar tata ya saka tana ji tamkar mahaifiyar su ce tare da ita, hakan ya k'ara mata nutsuwa a zuciyarta shiyasa bata son rabuwa da ita gabad'aya. Yaya ta kalle ta tayi dariya tace, "Kiyi hakuri Ameeantun Yaya Adam ki saki jikin ki komai lokaci ne dashi, auren da an d'aura shikenan komai zai wuce kiyi fatan Allah ya baki ta gari kawai. Nasan kina da kyakykyawar zuciya baza kiyi wani abun da zaki cutar da ita ba, nasan baza ki biyewa rud'in zuciya ba kice zaki bi malam ko boka dan hana auren ba, kiyi addu'ar Allah yasa haka itama take kamar ki kuyi zaman ku Lafiya. Shifa namiji da kike gani in ya d'auko aure sai kin jure dan zaki ta ganin abubuwan da baki kawo su ranki ba, haka nayi fama da Abban su Amira lokacin da ya auro matar sa ta biyu, wallahil azim kud'in abinci baya bamu gabad'aya kudin sa na aure ne. Ki gode Allah ke akwai ci da sha ni da akayi min tawa babu abincin kirki a gidan amma haka zai kwashe kudin sa ya Kai mata."
Ta dafa kafad'arta tace, "Ga Amira nan ki tambaye ta wahalar da muka sha ban fad'a miki bane sabida bana son yawan rok'on ke kin sani balle ma kina iya bakin kokarin ki a kaina. To Kiyi hak'uri nima da nayi hak'uri yanzu gashi komai ya wuce ta shigo taga bazata iya zaman gidan ba ta fita ta barni dashi d'in. Daman in kika ji ana kayi hak'uri an maka wani abun ne Ameena; amma zaki ga ribar sa wallahi. Sai kin daure dan a wannan zamanin da muke ciki babu macen da zata samu miji kamar Yusuf ta bari ya kubce mata, duk hanyar da zata bi zata bi domin ganin ta sake rik'e shi bai je ko Ina ba. Kishiya akwai ciwo na sani sai Kinyi hak'uri kin kawar da kanki komai mai wucewa ne."
YOU ARE READING
MAI ƊAKI...!
General FictionRayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da...