9. Gab da laasar suka shiga garin abuja har anguwansu maitama. A lokacin afrah ta tashi. Bayan horn dayayi maigadi yabude tsararren gidan. Tsabar kallo afrah bude baki tayi. Ashe titi da wuta datagani har motoci nafila ne akan kaftareren gydan dasuka xo. Parking dayayi daidai dafitowan wata mata fara ce tas kyakywa zakace irin shuwan nanne. Dogon rigane ajikinta dagudu ta rungume shi oyoyo darlin. Nan suka shiga wata duniyan afrah kqm kunya yarufeta ga jaka tarike hannu. Kiciniyar bude booth ne yasaasu dawowa hankalinsu haryace dear ga mai taimakq miki nakawo. Tadan yamutsa fuska oh to badamuwa. Nan afrah ta rusuna tagaysheta. Ta amsa ba yabo ba fallasa. Sunshiga inda aka nuna mata fannin dazata zauna. Nsnma kallo tayitayi harda ac. Da gadonta babba . Ga bandaki dakuma wardrobe. Tazube tashiga bayangida tayo alwala sannan tayi sallah a kankanta shekarunta tasan illan barin sallah.idarwanta keda wuya yaya babba yashigo tare dacewa fito kici abinci tabishi sukafita. Kitchen yanufa da ita taga yabude leda takeaway yafitar yabata shima yadau daya tare dazuba a plate yadau cokali yanufo falo. Itama hakan tayi saidai tanufi daki. Tanacin abincin tana mamaki itadai a saninta abincin siyarwane akesawa acikin abun takeaway. Toh meyasa matansa bata masa girkiba?. Kaman yadda hajiya takewa galadima idan yayi tafiya kafin yadawo ayi abinci kala kala azuba masa. Sai inda yakoshi. Anma shikam gakudin saidai wayam. Wani zuciyan tace meruwanki. Kikasan ko matar batada lafiyane?. Nanta basar tagama cin abincinta anan bacci ya kwasheta. Sai magriba tafarka tafita kitchen anan taga yaya babba yana fera dankali tace yaya kawo intayaka. Nan yace tazauna su fere tare. Duk da Allah yayisa da kyankyami bayacin abincin maaikata hakan yasashi tunda amina matarshi bata girki shiyake shiga yayi abunsa. Suna ferawa yana tambayanta abubuwan daya shafi addini. Yaga ashe yarinyan tanada dan sani. Ga wayo da basira dayayi mata yawa. Sukagama. Yakoya mata yadda ake kunna gas tare dacewa kinga inbani gida saikixo kigirka. A banki nake aiki. Sai dare nake dawowa. Amina bata girki. Nan takalleshi kaman zatayi magana saita basar. Suka soya dankalin da kwai yahada tea kakkaura yadibi nasa yatafi falo itama tadiba tayi daki. Anan taci tayi kyam kafin ta tashi taxo tawanke kwanukan.tayi sallahn ishai. Sannan tayi wanka tabi lafiyan gado!<br />
Aminu kuwa tun tafiyanta yabi yasusuce yawani dawo marar lafiyan doke. Har yasa mutane sukagane kowa lafiya yau haka?. Baitaba sanin yashaku da afrah ba sai ranan. Wani irin kaunarta yakeji. Lalle SO GUDALIYA ce. Sannan so haukane. Inbahakaba yarinyan dabata dare shekara 12 ba meye abunso?. Wani zuciyan yace gamo najini ne.