44

1.2K 62 0
                                    

44.shekaru 27 dasuka wuce---------- alhaji muhammed  da alhaji ibrahim. Ya da kanine agun galadiman  billiri. Saidai alhaji muhammed shine babba wanda yayi auren wuri ya aurosu fatyma wato hajiya babba. Da anty amarya. Kaninsa alhaji ibrahim matarsa daya hauwau. Wacce tahaifi danta daya. Ahmed.tarasu agun haihuwa. Hakan yasa aka kawo wa hajiya babba.wacce alokacin tahaifi bankwanninta yarasu. Hakan yasa inbanda hajiya da galadima da anty amarya dakuma su adda salma da babban yaya da shi ibrahim bawanda yasan maganan. Sai daidaikun tsoffi  . Don mutane dayawa sun zata da hauwau tarasu harda danta. Hajiya babba tacigaba da rainon ahmed kasancewar tamkar jego itama takeyi. Ahaka yagirma cikin kulawa. Kuma alhaji muhammed yace karta bari asani. Gudun kar ahmed din yasani yanajinshi kamar badan gydaba. ya Bayan watanni Allah yadauki ran ibrahim. Ahaka shima mahaifinsu yarasu inda shi muhammed yagaji sarautar galadiman yaci gaba da mulki. Alokacin da aka gano afrah yar Adda salma ce. Kuma aka nuna kanwarsa ce. Taso ta musanta don abar yartata ta zabi ahmed. Saidai mijinta ya kwabeta kartada zaune tsaye. Hakan yasa tayi shiru ta zubama sarautan Allah ido. Kunji bayani. Wato dai ahmed dan kanin galadima ne. Kuma afrah tana jika da gydan galadima uhmmm muje xuwa dai<br />
Alokacin ahmed yayi sallama dakowa inda yakarya xuciyan duk mai imani. Acewarsa idan yamutu sutaimaka su isar da sakonshi ga afrah. Kan cewa duk da tana kanwansa yanasonta. Kuma itace gudaliyansa. Kullum tana ransa. Aikuwa kuka akeyi  donkuwa lokacin husiena tatashi ta sabe sosai. Don koda taga aliyu namata hidima taji dadi. Harda murna akan an aura mata shi. Bakaramin kuka tayiba akan ahmed da afrah ba. Itakam ta tausaya musu. Karfe uku akashiga da ahmed. Don afara aiki. Kowa sai addua yakeyi. Aikuwa karfe biyar saiga fake aminu yana xuwa yafara meke faruwa. Akagayamasa nan yatada bori. Waisaidai abarshi yashiga operating rum. Kar ahmed yabada kidney .shibai yaddaba bayaso. Duk suka tsaya kallonshi. Kasancewar babban yayane agun namiji shida aliyu. Yace mekakeyi haka aminu?. Yazaayi kishi yarufe maka ido kanema ka kashe matar dakake aura. Yayanta nefa ba aure a tsakaninsu. Aikuwa aminu ya katseshi da Allah rufamin baki munafikin banza munafikin wofi. Inace boyewa kukeyi?. To nasani. Ai ba yanta uwa daya uba daya bane. Sannan nasan ahmed badam galadima bane. Hussiena ne tadauki hannu ta kwasheshi da mari  bakada hankali ne?. Kokayi looosing manners dinka?. Yazaayi kace yaya ba yaya na bane. Hannu yasa zai rama. Yaji ancafko shi aliyune  idonshi jaaa. Yace karka kuskura katamin mata. Matsiyacin banza matsiyacin wofi  aikuwa babban yaya yakira yan sanda yace sutafi dashi

KECE GUDALLIYA (2013)Where stories live. Discover now